Friday, January 3
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Ji yanda Magidanci ya zubawa matarsa man fetur ya bankawa mata wuta

Ji yanda Magidanci ya zubawa matarsa man fetur ya bankawa mata wuta

Duk Labarai
'Yansanda a Ota dake jihar Ogun sun kama wani mutum me suna Olubunmi Johnson dan kimanin shekaru 55 saboda kunnawa matarsa wuta. Lamarin ya farune da misalin karfe 8:30 pm na ranar Juma'ar data gabata a gidansu dake kan titin Fagbuyi na yankin Ilogbo. Wanda ake zargin ya jike matarsa da man fetur sannan ya kunna mata wuta. Kakakin 'yansandan jihar, Omolola Odutola ta bayyana cewa, dangin matar ne suka sanar dasu abinda ke faruwa. Tace an garzaya da matar zuwa Asibiti inda shi kuma mijin aka kamashi inda ake bincikensa kan yunkurin yin kisa.
Peter Obi ya baiwa daliban Najeriya shawarar su tafi kasar waje dan neman saukin rayuwa

Peter Obi ya baiwa daliban Najeriya shawarar su tafi kasar waje dan neman saukin rayuwa

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023 da ta gabata, Peter Obi ya baiwa daliban makarantar koyon jinya dake jami'ar College of Nursing Sciences dake Adazi-Nnukwu, jihar Anambra shawarar idan sun kammala karatunsu in suna son fita zuwa kasar waje yana goyon bayansu. Peter Obi yace ya sha baiwa hukumar kula da malaman jinya ta Najeriya cewa su daina hana malaman jinya dake son fita kasar waje zuwa neman kudi da ingancin aiki. Yace idan daliban suka ga cewa ba zasu samu abinda suke so ba a nan Najeriya ba laifi bane su tafi wani wajan dan samun abinda suke nema. Yace ba zasu baiwa daliban shawarar su zauna a inda abubuwa basa tafiya yanda ya kamata ba. Yace duk wanda ke son ya fita zuwa kasar waje ba laifi bane yana iya fita ia tabbata idan suka ...
Magidanci ya kàshe duka iyalansa sannan ya kàshè kansa saboda haushin Donald Trump ya ci zabe

Magidanci ya kàshe duka iyalansa sannan ya kàshè kansa saboda haushin Donald Trump ya ci zabe

Duk Labarai
Wani magidanci me suna Anthony Nephew dan kimanin shekaru 46 dake zaune a Duluth, Minnesota ta kasar Amurka ya kashe kansa. Lamarin ya farune da yammacin ranar Alhamis. Hakanan an ruwaito cewa mutumin ya kashe matarsa me suna Kathryn Ramsland 'yar kimanin shekaru 45 sannan ya kashe dansa me shekaru 7 me suna Oliver. Mutumin wanda bashi da addini kamin kashe kansa ya bayyana cewa yana gudun irin yanda masu addini zasu rika kallonsa a matsayin shedan shi da iyalansa da kuma kakaba masa dokokin addininsu. Mutane da yawa ne ke fama da matsalar tabin hankali a kasar Amurka.
Kalli Bidiyon yanda matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata 400 ke rufe fuskarta dan Kunya

Kalli Bidiyon yanda matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da mata 400 ke rufe fuskarta dan Kunya

Duk Labarai
Matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da matan aure sannan aka ga Bidiyon sama da 400 ta bayyana a bainar jama'a. Matar dai itama an ga wasu Bidiyo da aka zargi tana lalata da wani wanda ba mijinta ba. Lamarin ya jawo cece-kuce inda da yawa suka bayyana cewa dama duk me yi sai an masa. https://twitter.com/GistLovers/status/1855230310595637410?t=lFDV-yG-BcpC5BoNgf_ufg&s=19 A wani sabon faifan Bidiyon da ya bayyana an ga matar tana rufe kanta saboda kunya yayin da take kokarin shiga kotu. Ba dai a bayyana yaushe lamarin ya faru ba.
Kungiyar Kwadago zata tafi yajin aikin sai mama ta gani saboda gazawar Gwamnati na aiwatar da mafi karancin Albashin dubu 70

Kungiyar Kwadago zata tafi yajin aikin sai mama ta gani saboda gazawar Gwamnati na aiwatar da mafi karancin Albashin dubu 70

Duk Labarai
Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ta baiwa membobinta umarni a jihohin da basu fara aiwatar da mafi karancin kasafin kudin dubu 70 ba su shiga yajin aikin sai abinda hali yayi daga ranar 1 ga watan Disamba. Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ne ya bayyana haka bayan wata ganawa da suka yi a birnin Fatakwal na jihar Rivers. Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta sake duba wasu tsare-tsaren ta wanda yace suke cutar da mutane inda yace hakan ya jefa mutane a matsin rayuwa da kunci. Shugaban kungiyar Kwadagon yace sun kafa kwamiti na musamman da zai duba da kulawa da yanayin aiwatar da mafi karancin albashin da wayar da kan ma'aikata su tashi tsaye su nemi hakkinsu.
Kalli hotunan motar Tesla Cybertruck ta Naira Miliyan 224 da mawaki Davido ya siya

Kalli hotunan motar Tesla Cybertruck ta Naira Miliyan 224 da mawaki Davido ya siya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Mawakin Najeriya, Davido ya bayyana sabuwar motar da ya siya ta Tesla CyberTruck. Motar dai kirar 2024 Matte Black Tesla Cybertruck kudinta sun kai kwatankwacin Naira Miliyan 224. Davidi ya wallafa maganar sayen motar ne s shafinsa na sada zumunta. Kuma Tuni masoyansa suka fara nuna son kotar da tayashi murna.
Maza ku daina neman kara girman mazakutarku, Ka zama Gwani wajan gamsarda mace shi ake bukata ba girman mazakuta ba>>Inji Fasto Sam Adeyemi

Maza ku daina neman kara girman mazakutarku, Ka zama Gwani wajan gamsarda mace shi ake bukata ba girman mazakuta ba>>Inji Fasto Sam Adeyemi

Duk Labarai
Babban Fasto na cocin Daystar Christian Centre Sam Adeyemi ya bayyana cewa, maza su daina damun kansu da son kara girman mazakutarsu. Ya bayyana hakane a wajan zaman cocin na ranar Lahadi. Yace mafi yawan ci matsi ne musamman daga kafafen sadarwa zamani ke sanya mutane neman maganin karin girman mazakuta wanda daga baya da yawa ke yin danasanin yin hakan. Yace iya amfani da mazakutar wajan gamasar da macene shine abu mafi muhimmanci ba girmanta ko tsawonta ba. https://www.youtube.com/watch?v=y8podTJjpnM Yace maza su mayar da hankali wajan fahimtar abinda matansu ke bukata a gado yafi neman maganin kara girman mazakuta amfani.
Ji yanda wahalar rayuwa ta jefa kananan ‘yan mata masu shekaru 14 zuwa 16 Kàrùwàncì a Najeriya

Ji yanda wahalar rayuwa ta jefa kananan ‘yan mata masu shekaru 14 zuwa 16 Kàrùwàncì a Najeriya

Duk Labarai
Kananan 'yan mata wadanda basu kammala karatun sakandare ba sun samu kansu a halin karuwanci saboda tsadar rayuwa da talauci. A wani rahoto da jaridar Punch ta hada a Legas, wakilin jaridar ya je wani otal a Mushin inda ya nuna kamar shima ya je yin lalata da kananan yaranne. Manajan Otal din ya hadashi da wata me suna Mayowa 'yar kimanin shekaru 16. Da suka ware, ya fara mata tambayoyi inda tace ta je Legas ne daga garin Ilaro na jihar Ogun. Tace a lokacin da ta baro gida shekarunta 15 kuma dolene yasa ta bar gidan saboda iyayenta talakawa ne basa iya kula da ita, basa iya turata makaranta. Tace da ta je Legas ta fara yiwa wata mata aiki ne inda matar ta rika hada ta da Masu harkar kwaya. Tace wata rana jami'an tsaro sun je wajan inda suka tarwatsa su dalili kenan da ta ...