Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya gana da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara a fadarsa a daren ranar Alhamis.
Shugaban ya kuma gana da wakilan majalisar dokokin jihar ta Rivers.
Saidai babu cikakken bayanin kan abinda suka tattauna.
Shugaban 'yansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin yin bincike dan gano gaskiyar ikirarin wani tsohon dansanda da yace an biyashi Naira Miliyan 2 a matsayin kudin sallama.
Hutudole ya ruwaito muku cewa, Bidiyon dansansan ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda ya jawo cece-kuce.
Dansandan wanda yayi ritaya da mukamin Superintendent of Police yace ba zai karbi Naira Miliyan 2 ba saboda ta masa kadan bayan shafe shekaru 35 yana aiki a matsayin dansanda.
Dansandan wanda yayi ritaya a watan October 1, 2023 yace hukumar kula da fansho na 'yansanda ta sanar dashi cewa kudin sallamarsa Naira Miliyan 2 ne sannan akwai Naira Miliyan daya ta bashin kudin fansho da yake bi.
Kakakin 'yansandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana cewa, shugaban 'yansandan ya baya...
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shirin tabbatar da amfani da gas wurin girki ya shiga yankunan arewacin Najeriya.
Karamin ministan man fetur na Najeriya, Ekperikpe Ekpo ne ya ƙaddamar da shirin yau Alhamis a garin Sokoto.
Lokacin da yake jawabi a wurin ƙaddamar da shirin, gwamnan jihar Ahmed Aliyu ya ce matakin zai taimaka wajen rage dogaro kan amfani da itace a wajen girki, lamarin da ke cutar da muhalli musamman a jihohin Najeriya da ke iyaka da hamada.
Sai dai ya buƙaci masu ruwa da tsaki su yi ƙoƙarin ganin farashin gas ɗin ya yi daidai da ƙarfin talaka.
“Matuƙar ana so wannan shiri ya yi tasiri dole ne sai an samar da gas din LPG a wadace kuma cikin rahusa ga mutanen Najeriya masu matsakaicin karfi,” in ji gwamnan.
Hukumar 'yansandan jihar Kano sun kama barayin a daidaita su 4.
Kuma an kwato Keke Napep din sata guda 6 a hannunsu.
Kakakin 'yansandan jihar, DSP Hussaini Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar yau Alhamis.
Yace a ranar 17 ga watan Yuni sun samu bayanan sirri kan wasu barayin adaidaita Namiji da mace, Auwal Mohammed, 'm', 30 wanda ke zaune a Hotoro, sai kuma Maryam Ibrahim, 'f', 25 wadda 'yar jihar Bauchi ce.
Yace sun baiwa wani me adaidaita, Shu'aibu Aliyu kwaya suna kokarin kwace masa Keke Napep dinsa amma zuwan 'yansanda yasa basu yi nasara ba.
Yace da bincike yayi tsanani an gano wani me suna Suleiman Lawal, wanda aka fi sani da Aljan da kuma Muhammad Tajuddeen, 'm', 32 wanda suke aiki tare dasu.
Yace an kwato a daidaita 6 daga hannunsu kuma...
A sabon rahoton sa na shekarar 2025, bankin Duniya ya bayyana cewa, 'yan Najeriya Miliyan 86.8 ne ke cikin duhu basa samun wutar Lantarki a Najeriya.
Bankin yace wannan shine mutane mafiya yawa da ya zarta na kowace kasar Duniya.
Rahoton yace a cikin kasashen 20 da basa samun ingantacciyar wutar lantarki, guda 18 na Afrika ne.
Rahoton yace kaso 60 cikin 100 na 'yan Najeriya ne ke samun wutar lantarki sannan kaso 26 cikin 100 na 'yan kasar ne ke amfani da makamashi me tsafta na girki.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya sakawa sabuwar gadar sama da ya gina sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sule ya bayyana hakane yayin bude gadar a ranar Laraba.
Yace tsarin Gwamnatin Tinubu ne ya karfafa masa gwiwar aikata wannan aiki inda yace kuma an yi wadannan ayyukane ba tare da cin bashi ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa zai cika duka alkawuran da yawa 'yan Najeriya.
Ya bayyana hakane a ziyarar aiki da ya kai jihar Nasarawa.
Shugaban kuma ya bayar da tabbacin baiwa jihar Nasara gudummawar da take bukata wajan ci gaba musamman ta fannin ma'adanai da noma.
Ya bayyana hakane yayin ziyarar da ya kaiwa Sarkin Lafiya,Sidi Bage Muhammad sannan ya jinjinawa Gwamna Abdullahi Sule game da ayyukan ci gaba da yayi a jihar.
Da Ɗumi-Ɗumi
Matar tsohon gwamnan jihar Kebbi Dr. Zainab Shinkafi Bagudu ta sanar da ɗaukar nauyin duk wata waƙa da za a samu wanda zai yi a matsayin martani ga wadda mawaƙi Ali Jita ya yi ta “Uwargida”.
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false}
Dr. Zainab wadda ita ce amarya ga tsaron gwamnan wanda a yanzu shi ne Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙin Najeriya, a wani saƙo cikin raha da ta wallafa a shafinta na Instagram ta ambaci sunayen Naziru Sarkin Waƙa, Hamisu Breaker, Auta Waziri, Dauda Kahutu Rarara, Na...
'Yan Nijeriya Mu Kàra Baiwa Shugaba Tinubu Dama Ya Yi Tazarce A Zaben 2027 Saboda Ya Cigaba Da Wanzar Da Kyawawan Manufofinsa, Ra'ayin Khadija Santuraki
Wannan wani dan sahu ne da ya mayar da Naira Miliyan 4 da wani dan kasuwa ya manta a cikin kekensa.
https://twitter.com/NigeriaStories/status/1938315073887367651?t=Tsc0rNwMigpWIfkExKB2jw&s=19
Lamarin dai ya sa an ta yaba masa.