Saturday, December 13
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Cristiano Ronaldo ya sabunta Kwantirakinsa da Kungiyar Al Nasr, Ji damar da suka bashi ta ban mamaki

Cristiano Ronaldo ya sabunta Kwantirakinsa da Kungiyar Al Nasr, Ji damar da suka bashi ta ban mamaki

Duk Labarai
Tauraron dan kwallon Portugal, Cristiano Ronaldo ya sabunta kwantirakinsa da kungiyar Al Nasr ta kasar Saudiyya. Daga cikin damarmakin da aka bashi shine yana da bakin magana akan duk dan wasan da kungiyar zata siya. Ronaldo dan shekaru 40 ya amince da ci gaba da zama a kungiyar ta Al Nasr har zuwa shekarar 2027. Tun a shekarar 2023 ne dai Ronaldo ya je kungiyar ta Al Nasr.
‘Yan Kwaya sun karu a Najeriya>>Gwamnatin Tinubu ta koka

‘Yan Kwaya sun karu a Najeriya>>Gwamnatin Tinubu ta koka

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, 'Yan kwaya sun karu a Najeriya. Hakan na zuwane yayin da ake tunawa da zagayowar ranar yaki da shan kwaya da safararta a Duniya. Gwamnatin ta yi kiran hada kai dan yakar wannan matsala. Babbar sakatariya a ma'aikatar lafiya ta tarayya, Daju Kachollom, cee ta bayyana hakan a ganawa da manema labarai. Tace matsalar ta'ammuli da miyagun kwayoyi ba matsalar mutum daya bace ko kuma masu sha kawai, matsala ce ta kowa da kowa dan haka hadin kai...
Karanta Jadawalin Gwamnonin Babban Bankin Najeriya CBN da aka taba yi da shekarun da suka yi suna rike da mukaman

Karanta Jadawalin Gwamnonin Babban Bankin Najeriya CBN da aka taba yi da shekarun da suka yi suna rike da mukaman

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} 1 Abdulkadir Ahmed — 11 years, 97 days 2 Godwin Emefiele — 9 years, 8 days 3 Clement Nyong Isong — 8 years, 40 days 4 Paul Agbai Ogwuma — 5 years, 241 days 5 Joseph Oladele Sanusi — 5 years, 2 days 6 Ola Vincent — 5 years, 1 day 7 Charles Soludo — 5 years, 1 day 8 Lamido Sanusi — 4 years, 263 days 9 Aliyu Mai-Bornu — 3 years, 333 days 10 Olayemi Cardoso — 1 year, 284 days 11 Adamu Ciroma — 1 year, 278 days
Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji

Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar Canji. Rahotannin yanda kasuwar ta kasance a ranar Laraba na cewa, an sayi dala akan Naira N1,549.26 wanda hakan ya nuna darajar Nairar ta fadi idan aka kwatanta da yanda aka sayi dalar akan Naira N1,549.04 a ranar Talata. Nairar ta rasa darajar Kwabo N0.22. Wannan farashin kasuwar Gwamnati ne. A kasuwar 'yan bayan fage kuwa Dalar an saye ta ne akan Naira N1,590 a ranar Laraba inda hakan ke nuna darajar Nairar ta dan tashi da Naira 5 idan aka kwatanta farashin da aka saye ta na Naira N1,595 a ranar Talata.
Kalli Bidiyo: Mijina bai iya soyayya ba, ko Kis bai taba min ba tunda muka yi aure, kullun kawai saidai ya zo yace in bude mai>>Matar aure ta kaiwa Fasto karar Mijinta

Kalli Bidiyo: Mijina bai iya soyayya ba, ko Kis bai taba min ba tunda muka yi aure, kullun kawai saidai ya zo yace in bude mai>>Matar aure ta kaiwa Fasto karar Mijinta

Duk Labarai
Wata matar aure ta dauki hankula bayan kai karar Mijinta wajan Fasto bisa zargin bai iya soyayya ba. Matar tace tunda suka yi aure ko kiss Mijin nata bai taba mata ba, da yayi Niyyar kwanciyar aure da ita saidai kawai yace mata ta bude masa. https://twitter.com/NigeriaStories/status/1938153791884562726?t=WKQilKs5FLBd9-R5ELA4jg&s=19 Menene ra'ayinku aka wannan?
Duk me Tambayar me aka yi da kudin Tallafin man fetur, ya zo jihar Nasarawa ya gani>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule

Duk me Tambayar me aka yi da kudin Tallafin man fetur, ya zo jihar Nasarawa ya gani>>Inji Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule

Duk Labarai
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa masu tambayar ya aka yi da kudin tallafin man fetur su zo jihar Nasarawa su ga yanda aka yi dasu. Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihar Nasarawa ta kwanaki daya inda ya samu rakiyar manyan ma'aikatan Gwamnati ciki hadda Gwamnonin APC da dama. Gwamnan yace manya-manyan canje-canjen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kawo wa Najeriya sune cire tallafin Man fetur sai kuma cire tallafin dala. Ya bayyana cewa kuma duka an shaida irin ci gaban da hakan ya kawo musamman su a jiharsu ta Nasarawan.
A yau zan kafa sabon Tarihin saka hannu a kudirin dokar canja Haraji da zai amfani har wadanda bama a haifa ba>>Shugaba Tinubu

A yau zan kafa sabon Tarihin saka hannu a kudirin dokar canja Haraji da zai amfani har wadanda bama a haifa ba>>Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, a yau, Alhamis zai kafa sabon Tarihi da Tubalin ci gaban Najeriya wanda zai amfani har ma wadanda ba'a haifa ba. Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ta kafar sada zumuntarsa inda yace yana godiya ga 'yan Najeriya bisa hadin kan da suka bashi na canja fasalin Karbar Haraji a Najeriya. Shugaban yace wannan sabon kudirin na Haraji zai habaka kasuwanci a Najeriya sosai domin akwai adalci a cikinsa. Shugaban ya bayyana cewa, yana kira ga 'yan kasuwa na Duniya cewa ga dama ta samu ta zuba hannun jari a Najeriya. Ya kuma godewa, Kwamitin da ya kafa na canja fasalin karbar Harajin da majalisar dattijai da Gwamnatocin jihohi bisa gudummawar da suka bayar wajan tabbatar da canja fasalin karbar Harajin.
Shugaba Tinubu yaki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu, Ji Dalili

Shugaba Tinubu yaki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu, Ji Dalili

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu wadda 'yan majalisa suka amince da ita. Shugaban ya aikewa da majalisar tarayya da wasika dake kunshe da dalilansa na kin sakawa sabuwar dokar hannu. Shugaba Tinubu yace dalilinsa shine sabuwar dokar na kunshe da cewa, idan hukumar ta NDLEA ta kwace kwaya ko kayan laifi, zata iya ajiye ko rike wani sashi na kayan da ta kwace. Shugaban yace dokar da ake da ita a yanzu ta tanadi cewa ne a saka ko ma wane irin abune aka kwace zuwa asusu na musamman da aka ware dan kula da kayan da aka kwace, kuma bai ga dalilin da zai sa a canja wannan tsari ba. Yace shugaban kasa ne kawai ke da ikon baiwa duk wata hukuma kudi daga cikin asusun da ake tara kudaden da aka kwace. Yace tsarin da ake kansa yafi tabbatar da tsar...
Gwamnatin Tarayya ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan rage farashin man

Gwamnatin Tarayya ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan rage farashin man

Duk Labarai
Shugaba kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bukaci a rage farashin man fetur a Najeriya. Kuma hukumar kula da sayar da man fetur din Najeriya, NEPZA a takaice ta bayyana aniyarta ta hada kai da matatar man fetur din Dangote dan tabbatar da wannan bukata ta shugaban kasa. Shugaban hukumar, Dr. Olufemi Ogunyemi ne ya bayyana haka a Abuja yayin wata ziyara da aka kai masa. Itama matatar man Dangote ta ce a shirye take dan tabbatar da wannan kudirin na shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu. Wannan shiri zai samu nasara ne ta hanyar tabbatar da ci gaba da sayar da man fetur din Najeriya da kudin Naira maimakon dala musamman ga matatar Dangote.
Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas

Duk Labarai
Obi ya koka kan rushe ginin ƙanin sa a Legas Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi Allah-wadai da rushe wani gini da ya ce na ƙaninsa ne da ke jihar Legas. Ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da ya saɓa wa doka kuma yana nuna yadda Najeriya ke ƙara nutsewa cikin rashin bin doka a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Obi ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya kai ziyarar gaggawa zuwa wurin da aka rushe ginin, inda ya nuna ɓacin ransa kan "take hakkokin ‘yan ƙasa da rashin bin ka’ida da aka yi ba tare da wata hujja ba." Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya ce jami’an tsaro sun hana ɗan’uwansa samun damar ceto duk wani kayan da ke cikin ginin kafin a fara rushewar. Ya ƙara da cewa wannan abin da ya faru hujja ce ta yadda tsarin ...