An kama malamin jami’a saboda wallafa Bidiyon rawa na dan Gwamnan Bauchi
Kotu a jihar Bauchi na shirin yanke hukunci kan wani malamin jami'a da ya wallafa tsohon Bidiyon dan gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad yana rawa.
A yau Alhamis ne ake sa ran kotun zata yanke hukuncin neman belin malamin me suna Dr. Abubakar Ahmad wanda dan gwamnan me suna Shamsudeen Bala Mohammed ne ake zargin ya shigar dashi kara.
Malamin na koyarwa ne a kwalejin Federal College of Horticulture dake jihar.
An kamashi ne saboda wani tsohon Bidiyon da ya wallafa na dan Gwamnan da matarsa suna rawa.
Me ikirarin kare hakkin bil'adama kuma mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore ne ya wallafa hakan.
Yace An tsare malamin makarantar na tsawon makonni 2 bisa cin zarafi da rashin adalci.
Matar malamin me suna Fatima ta nemi a saki mijinta.
Fatima ta yi kira ga Gw...








