Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Daya daga cikin masu laifin da suka tsere daga gidan yari yace a aikawa mahaifiyarsa Ladar Naira Miliyan 5 da aka saka ga duk wanda ya taimaka aka kamasu shi kuma zai koma gidan yarin da kanshi

Daya daga cikin masu laifin da suka tsere daga gidan yari yace a aikawa mahaifiyarsa Ladar Naira Miliyan 5 da aka saka ga duk wanda ya taimaka aka kamasu shi kuma zai koma gidan yarin da kanshi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnati ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama wadanda suka tsere daga gidan yarin Ilesa na jihar Osun. Saidai wani shafi a Twitter wanda yake ikirarin shi daya daga cikin wadanda ake nema ne yace damfarar dala $20 kawai yayi aka kamashi. Yace amma a aikawa Mahaifiyarsa Miliyan 5 din da aka ce an saka akan duk wanda ya taimaka aka kamasu shi kuma zai koma gidan yarin da kansa. https://twitter.com/illxgally/status/1925263845938852073?t=W7WZEzT9q4WDx1QjtJ9pLg&s=19 Saidai wasu na shakkun cewa ba shi bane.
Dangote ya shiga cikin mutane 100 da suka fi bayar da taimako a Duniya inda yake bayar da kyautar Naira Biliyan 50 duk shekara

Dangote ya shiga cikin mutane 100 da suka fi bayar da taimako a Duniya inda yake bayar da kyautar Naira Biliyan 50 duk shekara

Duk Labarai
Jaridar Time ta saka Dangote cikin mutane 100 da suka fi bayar da kyauta a Duniya. Rahoton yace Dangote yana bayar da kyautar Naira Biliyan 50 duk shekara. Dangote dai shine wanda yafi kowane bakar fata Kudi a Duniya sannan shine na daya a Afrika. A baya, Dangote ya rabawa 'yansandan Najeriya kyautar Motocin aiki.
Gwamnati ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama masu laifin da suka tsere daga gidan gyara hali su 7, kalli Hotunansu ko kasan wani

Gwamnati ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama masu laifin da suka tsere daga gidan gyara hali su 7, kalli Hotunansu ko kasan wani

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta wallafa hotunan masu laifi da suka tsere daga gidan gyara hali na Ilesa dake jihar Osun. Gwamnatin tace ta saka ladar Naira Miliyan 5 ga duk wanda ya taimaka aka kama su. Da safiyar ranar Talata ne dai masu laifin suka tsere a yayin da ake tsaka da ruwan sama.
Kalli Bidiyon yanda masunta suka kama Katoton maciji a Kaduna me ban tsoro

Kalli Bidiyon yanda masunta suka kama Katoton maciji a Kaduna me ban tsoro

Duk Labarai
Bidiyon yanda wasu masunta da suka je kamun kifi amma suka kama Katon maciji a jihar Kaduna ya dauki hankula. An ce aun ajiye macijinne har kusan tsawon wata daya inda wani ya sayeshi amma ya rika yunkurin tserewa. Abin dai ya bada mamaki: https://twitter.com/Nasir1on1/status/1925204970732745095?t=hVC6JcLoXlxX71V2rZlvdQ&s=19 Da yawa aun yo mamaki da ganin girman Macijin.
Bankin Duniya yace rabin mutanen Najeriya watau mutane sama da Miliyan 100 sun fada Talauci tsamo-tsamo

Bankin Duniya yace rabin mutanen Najeriya watau mutane sama da Miliyan 100 sun fada Talauci tsamo-tsamo

Duk Labarai
Bankin Duniya yace kusan rabin 'yan Najeriya sun fada cikin talauci tsamo-tsamo saboda tsadar rayuwa dake karuwa akasar. Sanarwar da bankin ya fitar yace kaso 46 na 'yan Najeriya watau mutane Miliyan 107 sun fada cikin talauci inda suke rayuwa a kasa da Dala $2.15 a kullun. Bankin yace ma'aikata basa samun rayuwa me kyau saboda Albashinsu baya kai musu yanda ya kamata. A baya dai bankin yace akwai Talauci sosai a tsakanin kauyawan Najeriya.
Kalli Bidiyo: ‘Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta ‘yan majalisa Bidiyonta tsirara wanda tace tsohon saurayinta ne ya dauke ta ba tare da izinin ta ba kuma tana son a hukuntashi

'Yar majalisar Amurka, Nancy Mace ta nunawa abokan aikinta a zaman majalisar Bidiyon ta tsirara dan ta kafa shaida akan zargin da takewa tsohon Saurayinta cewa ya yada Bidiyon tsiraicinta ba tare da izinin ta ba. Ta ce ya yada Bidiyon ta har guda dubu 10 ba tare da izininta ba. https://twitter.com/nypost/status/1925193881437548789?t=LGLEHnJo4XBJNQ4g_OZW_g&s=19 Saidai mutane na shakkar cewa ta yaya zai samu Bidiyon ta har guda dubu 10 kuma tace ba tare da saninta ba? Ana zargin dai ya kafa kyamarori ne a gurare daban-daban inda ta hakane ya samu Bidiyon nata.
An buɗe cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto

An buɗe cibiyar koya wa almajirai kwamfuta a Sokoto

Duk Labarai
Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ƙaddamar da wata cibiyar bai wa almajirai da yara mata marasa zuwa makaranta ilimin kwamfuta da na sana'o'i "domin inganta rayuwarsu". Cibiyar wadda gwamnatin ta gina tare da tallafin asusun tallafa wa yara na duniya UNICEF, zai mayar da hankali wajen koya wa ɗaliban ilimin yadda za su yi sana'a ta amfani da fasahar zamani, ta hanyar amfani da wayoyin hannu da kuma kwamfuta. Manufar shirin ita ce tallafa wa tsarin bayar da ilimi ga kowa, a matakin jiha da ƙananan hukumomi. Baya ga ilimin kwamfuta, ɗaliban za su kwashe shekara ɗaya suna samun horo a sana'o'i daban-daban da kuma ilimin rubutu da karatu. Sokoto na cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar yawaitar yara marasa zuwa makaranta da kuma almajirai masu gararamba a kan titu...
‘Ƴan majalisar Najeriya na cusa kwangilolin son rai a kasafin kuɗi’

‘Ƴan majalisar Najeriya na cusa kwangilolin son rai a kasafin kuɗi’

Duk Labarai
Rahoton wata ƙungiya mai sanya ido kan kasafin kuɗi a Najeriya da wasu ƙasashen Afirka (BudgIT) ya gano cewa wasu ƴan majalisar dokokin Najeriya na cusa kwangiloli marasa amfani, waɗanda ba su da alfanu ga ƙasa a cikin kasafin kuɗin Najeriya. BudgIT ta ce ta gano kwagiloli har 11,122 wadanda za su lashe kuɗin da ya haura naira tiriliyan 6.93 da aka saka a cikin kasafin kuɗin 2025 da Majalisar ƙasa ta cusa ba tare da la’akari da cancanta ba. Haka nan rahoton ya bayyana cewa an cusa irin wadannan ayyuka a kasafin hukumomi da ma’aikatun gwamnati waɗanda ba su da wata alaƙa da ayyukan. Wasu daga cikin kwangilolin da aka lissafa sun haɗa da kwangilar bayar da tallafin karatu da rabon takin zamani da gina cibiyar koyar da kwamfuta ICT/CBT, da kuma samar da motoci don tsaro da sauransu d...