Monday, December 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Karanta Jadawalin mutane 9 da zasu yi takara da Sheikh Isa Ali Pantami wajan neman takarar Gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027

Karanta Jadawalin mutane 9 da zasu yi takara da Sheikh Isa Ali Pantami wajan neman takarar Gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027

Duk Labarai
Tuni dai magana ta yi karfi wajan bayyanar babban malamin Addinin Islama kuma dan siyasa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami wajan neman takarar gwamnan jihar Gombe a shekarar 2027. Sunayen sauran mutane 9 da zasu yi taka dashi sun bayyana kamar haka: Prof. Isa Ali Pantami Arc. Yunusa Yakubu Dr. Aminu Yuguda Muhammad Jibrin Barde Hon. Usman Bello Kumo Hon. Ali Isa JC Engr. Aliyu Mohammed (Kombat) Hon. Khamisu Ahmed Mailantarki Hon. Mohammed Gambo Magaji Barr. Sani Ahmed Haruna
Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami’ar Da Ta Koma Sana’ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi

Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami’ar Da Ta Koma Sana’ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Gwamna Abba Kabir Ya Bukaci A Kawo Masa Takardun Makarantar Tsohuwar Dalibar Jami'ar Da Ta Koma Sana'ar Wainar Fulawa Da Awara Saboda Rashin Aikin Yi
Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu, shi kuma Trump baya son raini dan haka yace zai amince da kasar Falasdinawa ya ga tsiya

Dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu, shi kuma Trump baya son raini dan haka yace zai amince da kasar Falasdinawa ya ga tsiya

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, dangantaka ta yi tsami sosai tsakanin shugaban kasar Amurka Donald Trump da na Israela, Benjamin Netanyahu. Tun da farko dai hakan ya bayyana ne bayan da kasar Amurka ta amince ta taimakawa kasar Saudiyya mallakar tashar makamin Kare dagi, Nokiliya, ba tare da saka kasar Israela a cikin maganar ba. Kasar Israyla a baya itace take shigewa Amurka gaba akan kowane lamarin da ya shafi hulda da kasashen Gabas ta tsakiya, saidai a yanzu gashi an yi maganar makamashin nokiliya tsakanin Amurka da Saudiyya babu ita. Hakanan Amurka ta yi sulhu da mayakan kasar Yemen wanda shima ba'a saka kasar Israela cikin tattaunawar ba, a wasu rahotanni ma ance Amurkar bata ce kada mayakan Yemen su kaiwa kasar Israela hari ba a tattaunawar, ita dai kada a taba kadarorin ta. ...
Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba

Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba

Duk Labarai
Shugaba Tinubu yace ya matsawa yan Najeriya ne saboda komai ya daidaita, kuma talaka zai sha jar miya nan bada dadewa ba. Shugaba Tinubu yace tsare-tsaren sa na cire tallafin man fetur da sauransu da suka sa mutane cikin halin dauwa, nan gaba a'a ga amfaninsu. Shugaban yace tuni an fara ganin Amfanin wadannan tsare-tsaren saboda farashin kayan Masarufi sun fara sauka. Tun bayan da shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dai aka shiga tsadar rayuwa a Najeriya wadda har yanzu ba'a dawo daidai ba.
YANZU YANZUHukumar EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, akan zargin wawure Naira biliyan 528

YANZU YANZUHukumar EFCC zata binciki ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, akan zargin wawure Naira biliyan 528

Duk Labarai
EFCC Ta Yi Alkawarin Bincikar Matawalle akan zargin wawure sama da Naira biliyan 528. Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta yi alkawarin gudanar da bincike kan zargin karkatar da kudi da aka yi wa Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, biyo bayan wani koke da jam’iyyar All Progressives Congress Young Leaders Alliance (APC-YLA) ta gabatar. Zarge-zargen dai na zargin Matawalle da wawure sama da Naira biliyan 528 a lokacin da yake Gwamnan Jihar Zamfara. Wannan tabbacin ya zo ne a wata zanga-zangar da aka gudanar ranar Juma’a a hedikwatar EFCC da ke Abuja, inda shugaban jam’iyyar APC-YLA Convener, Mohammed Ireji, da sauran masu zanga-zangar suka bukaci a sake bude shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa Matawalle. Ireji ya nuna shakku kan jinkirin...
Duk da doka ta bukaci hakan, Ma’aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Duk da doka ta bukaci hakan, Ma’aikatan Gwamnatin ciki hadda shugaban kasa, Tinubu, Kashim, da Akpabio sun ki bayyana kadarorin da suka mallaka, kuma an kasa hukuntasu

Duk Labarai
Dokar da'ar Ma'aikatan gwamnatin Najeriya, CCB ta bukaci dukun wani ne rike da mukamin siyasa ko masu hidima masa su bayyana kadarorin da suka mallaka kamin su hau mulki da kamin su saka. Dokar kuma ta tanadi cewa dole su bayyana kadarorin da matansu ko mazansu idan macece suka mallaka da wanda 'ya'yansu wanda basu yi aure ba suka mallaka. Saidai da yawa basa bin wannan doka kuma an kasa hukuntasu. Cikin wadanda basu bi wannan doka ba hadda shuwagabannin Najeriya, watau Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio. Hakan na zuwane duk da kiraye-kirayen kungiyoyin fafutuka na neman su bayyana kadarorin nasu. Ookar dai ta tanadi bayyana kadarorin ne dan tsaftace aikin gwamnati da satar dukiyar Talaka da kuma hana ra...
Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Da Duminsa: Gwamnonin Arewa zasu Gana a Kaduna game da matsalar tsaron da ta addabi yankin

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnonin Arewacin Najeriya zasu gana a Kaduna saboda tattaunawa matsalar tsaro da ta addabi yankin. Rahoton yace hadimin gwamnan jihar Gombe, Ismaila Misilli ne ya bayyanawa manema labarai na Punchng hakan inda yace gwamnan Gomben shine ya kira wannan taron a matsayinsa na shugaban Gwamnonin Arewan. Yace idan dai ba an canja ba, a yau, Asabar ne za'a yi wannan taro a Kaduna kuma matsalar tsaron yankin ce babban abinda za'a tattauna.
Mutanen Jihar Zafara sun yabawa Shagaba Tinubu saboda hàlàkà shuwagabannin ‘yan Bìndìgà

Mutanen Jihar Zafara sun yabawa Shagaba Tinubu saboda hàlàkà shuwagabannin ‘yan Bìndìgà

Duk Labarai
Mazauna Karamar Hùkumar Talata Mafara Šùn Yabawa ShugabaTinubu Da Matawalle Kán Hallaka Ŕìķakkun 'Ýan Bìñdiga Jijji Da Kachallah Sagili. Mazauna karamar hukumar Talata Mafara da ke jihar Zamfara sun bayyana godiya mai yawa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Ministan kasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya Dr Bello Matawalle, Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, da Babban hafsan hafsoshin Nijeriya Janar Christopher Musa, bisa irin gudummawar da suka ba da wajen kawar da wasu manyan shugabannin 'yan bindiga a Arewa maso Yammacin Nijeriya da ma sauran sassan kasar. Aikin da aka kaddamar domin fatattakar Jajji Dan Auta da Kachallah Sagili ya samu yabo daga al’umma a matsayin wata babbar nasara da ke nuni da dawowar zaman lafiya a yankin da ake fama da rikici....
Yadda Mala’iku Suka Kai Ni Aljannah Har Na Gana Da Tsohon Abokina Kafin Na Dawo, Inji Godwin Ugeelu Bayan Gawarsa Ta Miƙe A Jihar Nassarawa

Yadda Mala’iku Suka Kai Ni Aljannah Har Na Gana Da Tsohon Abokina Kafin Na Dawo, Inji Godwin Ugeelu Bayan Gawarsa Ta Miƙe A Jihar Nassarawa

Duk Labarai
Yadda Mala’iku Suka Kai Ni Aljannah Har Na Gana Da Tsohon Abokina Kafin Na Dawo, Inji Godwin Ugeelu Bayan Gawarsa Ta Miƙe A Jihar Nassarawa. Godwin Ugeelu, wani mai maganin gargajiya mazaunin Jihar Nasarawa ya farka ya fito daga akwatin gawa kwana biyu bayan mutuwarsa a ranar da za a birne shi. Daga bisani, Ugeelu ya bada labarin dukkan abin da ya gano a yayin da aka kai shi 'Aljanna' da kuma dalilin da yasa Ubangiji ya bashi damar dawowa duniya. Godwin Ugeelu ya ce: "Na gode wa Ubangiji da ya sake bani wata rayuwar bayan ɗanɗana mutuwa. Abin ala'jabi ne yadda Allah ya sake bani wata damar rayuwa don in bauta masa in kuma yadda sakonsa." "Tafiya ta zuwa Aljanna mai sauƙi ne. Na ruɗe kan abin da Ubangiji ya min. Abin da zan iya tunawa shine mantuwa ta kama ni lokacin da n...