Kalli Bidiyo: Matashi daga Arewa me karatun Qur’ani ya zarta Mawaki Davido mabiya a Tiktok
Matashi daga Arewa me amfani da sunan Youngalajerh8 a Tiktok dake Karanta Qur'ani ya samu mabiya sama da shahararren mawakin Najeriya, Davido.
Younalajerh8 ya kai mabiya Miliyan 9 a Yayin da shi kuma Davido ke da mabiya Miliyan 8.8.
Hakan yasa mutane da yawa fadin cewa ba sai mutum yayi abin banza ba kamin ya daukaka a Tiktok.
https://www.tiktok.com/@youngalajerh8/video/7530169409021758727?_t=ZS-8yYO9wzk9Ef&_r=1








