Faston Da yace za’a yi tashin Qiyama ranar 25 ga watan Disamba yace ba’a mai wahayin shekarar da hakan zai faru ba
Fasto Ebo Noah na kasar Ghana wanda yace an masa wahayin wai za'a yi tashin qiyama ranar Kirsimeti yace ranar kawai aka gaya masa banda shekarar.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi bayan da ranar Kirsimeti ta zo ta wuce amma ba'a yi tashin Qiyamar ba inda wasu suka fara kiransa da makaryaci.
https://www.tiktok.com/@jakebeatzgh/video/7587152814820855060?_t=ZS-92ZPDyqfn4S&_r=1








