Saturday, December 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

An fitar da jadawalin kasashen Duniya 40 da suka fi farin ciki amma babu Najeriya a ciki

An fitar da jadawalin kasashen Duniya 40 da suka fi farin ciki amma babu Najeriya a ciki

Duk Labarai
Jadawalin kasashen Duniya da mutanensu suka fi farun ciki guda 40 kenan wanda kafar kungiyar World Happiness Report suka wallafa, saidai babu Najeriya a ciki. World's happiest countries. Finland Denmark Iceland Sweden Netherlands Costa Rica Norway Israel Luxembourg Mexico Australia New Zealand Switzerland Belgium Ireland Lithuania Austria Canada Slovenia Czechia UAE Germany United Kingdom United States Belize Poland Taiwan Uruguay Kosovo Kuwait Serbia Saudi Arabia France Singapore Romania Brazil El Salvador Spain Estonia Italy (World Happiness Report)
Da yiyuwar Tinubu ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba idan Amurka ta saki bayanai kan safarar miyagun kwayoyi da tace yayi-Inji Chief Eze Chukuemeka

Da yiyuwar Tinubu ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba idan Amurka ta saki bayanai kan safarar miyagun kwayoyi da tace yayi-Inji Chief Eze Chukuemeka

Duk Labarai
Da yiyuwar Tinubu ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba idan Amurka ta saki bayanai kan safarar miyagun kwayoyi da tace yayi. Ana zargin dai Shugaban kasa Tinubu da wasu mutane 3 a shekarun 90s sun yi safarar kwayoyi a birnin Chicago na Jihar Illinois ta kasar Amurka. An yi shari'a dan yanke musu hukunci amma ba'a san inda aka kwana ba Lauyoyi da ma sauran masu fafutuka na ta neman hukumar FBI da DEA su saki bayanai kan lamarin amma sai jan kafa suke inda lamarin ya dauki shekaru. Wasu dai na zargin akwai wata kullalliya a kasa game da kin fitar da bayanan.
Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa

Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna ‘Katsina babu ƙorafi’ ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa

Duk Labarai
Ba da yawuna aka kafa allon da ke nuna 'Katsina babu ƙorafi' ba a Katsina ~ Dikko Raɗɗa. Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yace a matsayinsa na gwamna, bai da masaniya dangane da kafa wani allo da ke nuna cewa Al'ummar Jihar ba su da ƙorafi bisa ga salon Mulkin shugaba Tinubu ba. Hasalima Gwamnan yace, sun gabatar ma shugaba Tinubu ƙwararan ƙorafe-ƙorafe har guda 3 da ke buƙatar a magance masu, wanda suka haɗa da Matsalar tsaro, kammala wuta mai amfani da hasken Rana, da kuma fadada filin sauka da tashin jirage na Umar Musa Yar'adua da ke Katsina. Bayan haka ya ja hankalin masu suka da su riƙa tantance labarin da suka gani a kafafen sada zumunta domin tabbatar da asalin labarin, kafin sukar wanda baya da masaniya a kai. Daga Lukman Aliyu
Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu

Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu

Duk Labarai
Tashin Hankali: Wata Amarya ta yiwa Ango yankan rago a Kano kwana 9 da aurensu. Rahotannin da ke shigo wa Jaridar Arewa yanzu haka sun tabbatar da cewa ana zargin wata amarya da yiwa Angonta yankan rago a daren jiya Litinin, a jihar Kano. Lamarin ya faru a unguwar Farawa da ke cikin birnin Kano. Bayanai sun tabbatar da cewa Amaryar ta fara shayar da shi guba ne a Lemu, daga bisani ta yi masa yankan rago kamar yadda ta Dala FM ta ruwaito. Hakazalika wani rahoton ya ce an yi masu auren zumunci ne a ranar 27 ga watan Afrilu, wanda yau kimanin kwana 9 kenan. Zuwa yanzu jami'an tsaron yan sanda sun samu nasarar kama Amaryar domin bincike. Jaridar Arewa
Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata

Likitocin Abuja za su tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata

Duk Labarai
Kungiyar ƙananan likitoci a Najeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar ta sanar da fara yajin aikin gargadi na kwanaki uku daga yau Talata, bayan korar ma’aikatan lafiya 127 da hukumar kula da ma’aikatan birnin na FCT ta yi. An yanke shawarar shiga yajin aikin ne bayan wani taron gaggawa da kungiyar likitocin ta gudanar a asibitin Asokoro ranar Litinin, kamar yadda kafar talabijin ta Channels TV ta ruwaito. Shugaban ƙungiyar likitocin, Dr. George Ebong, ya bayyana korar a matsayin maras tushe da kuma "rashin imani", yana mai buƙatar gaggauta dawo da ma’aikatan bakin aiki tare da biyansu albashin watan Afrilu. Dr. Ebong ya kuma buƙaci shugaban hukumar kula da ma’aikatan Abuja, Emeka Ezeh, da ya yi murabus daga mukaminsa. Ya yi gargaɗin cewa idan Ministan Abuja Nyesom Wi...
An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda

An gurfanar da wata mata Harira Muhammad a gaban babbar kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Post Office a jihar Kano, bisa zargin ta da auren maza biyu a lokaci guda

Duk Labarai
Ita dai Hariri ta kwashe tsawon watanni 6 basa zaune waje ɗaya da mijinta na farko Sagiru Shuaibu Tudun Murtala, sai dai ya ce ranar da ya ziyarci gidanta, ya tarar da ita kwance a gadonsu na aure da wani, lamarin da ya sa ya sanar da makwabta abin da ke faruwa. A lokacin da ta ke kare kanta game da zargin da mijinta na farko ya yi, Hariri ta musanta cewa akwai igiyar aure tsakaninta da shi, amma sai dai da alkalin kotun mai shari'a Khadi Munzali Tanko Soron-Dinki ya umarce ta data yi rantsuwa da Al-Qur'ani sai ta janye kalamanta. Shi kuwa a nasa ɓangaren, Bello Abdullahi Ƴankaba mijin Harira na biyu, ya shaida wa kotun cewa ya aureta ne a hannun kawunta Abdullahi Umar kan sadaki naira dubu ɗari. Bayan kammala jin dukkanin ɓangarorin, mai shari'a Khadi Munzali Tanko...
BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa

BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa

Duk Labarai
BABBAR MAGANA: Daga Kai Sadaki Shi Da Abokinsa Suka Aure Yaya Da Kanwa. {"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Daya daga cikin Angwayen, Umar Khalipha ne ya tabbatar da hakan.