INNA LILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN: Mahaifin Abale Ya Rasu.
Za a yi jana'izarsa bayan sallar la'asar a Darmanawa Royal City a Kano.
Allah Ya gafarta masa.
Lauyoyin Jihar Zamfara Sun Goyi Bayan Gayyatar Gwamna Dauda A Gaban Majalisa Kan Ŕikicin Majalisar Ďokoki.
Kungiyar lauyoyin Jihar Zamfara ta bayyana goyon bayanta ga matakin da Majalisar Wakilai ta Nijeriya ta dauka na gayyatar Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, da shugabannin majalisar dokokin jihar domin su bayyana kan rikicin da ke kara tsananta a majalisar dokokin jihar da kuma tabarbarewar tsaro a fadin jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya.
Wannan kungiya, wadda ke da matsayi a fannin kare doka da tsarin mulki, ta bayyana kiran a matsayin matakin da kundin tsarin mulki ya amince da shi, bisa tanade-tanaden sashe na 88 da 89 na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda ya ba Majalisar Tarayya damar gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi jama’a da kuma kiran jami’ai mas...
Gwamnatin Kenya ta bayyana jifa da takalmi da aka yi wa shugaban ƙasar, William Ruto a wani gangamin siyasa a ranar Lahadi, a matsayin “abun kunya”.
Bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya bugi hannun shugaban ƙasar na hagu, a yayin da ya ke magana.
https://twitter.com/citizentvkenya/status/1919295562660098502?t=JznCzRShAKV-GnuJ17gZpg&s=19
Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura, ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran a kama waɗanda suka aikata hakan.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce “me zai faru idan dukkanmu muka fara jifar juna da takalma? Wane tarbiyya muke koya wa ƴaƴan mu?” Ya kuma buƙaci a girmama muƙamin shugaban ƙasa.
Kafofin watsa labarai a Kenya na bayar da rahoton cewa an kama mutum uku dangane da lam...
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, na cewa kimanin mutum 11 wasu ‘yan bindiga suka kashe a garuruwan Zamfarawa da Dogon Hayi da kuma Ɗan Kurmi.
Harin ya zo ne mako ɗaya bayan da ƴanbindigar suka karɓi harajin da ya kai naira miliyan 60, wanda suka tilastawa dagatai tattara waɗannan kuɗi daga wajen jama’a.
Sai dai, duk da haka sun ci gaba da kai wa mutanen hare-hare.
Jihar ta Zamfara dai ta sha fama da hare-haren ƴanbindiga waɗanda ke garkuwa domin neman kuɗin fansa.
Duk da irin ƙoƙari da gwamnati ke cewa tana yi na daƙile ayyukansu - hakan ya citura saboda yadda suke ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ce ta fara bincike kan mutuwar wasu ƙananan yara biyar a garin Agyaragu cikin ƙaramar hukumar Obi a jihar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Ramhan Nansel, ya fitar yau Litinin a birnin Lafia.
Sanarwar ta ce an gano gawawwakin yaran ne a cikin lalatacciyar motar da ke ajiye a gidan wani Mista Abu Agyeme.
Ta ce tuni kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed ya umarci gudanar da cikakken bincike don tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.
A ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne, wani magidanci ya kai rahoto ga 'yansanda cewa an gano ƙananan yara kwance shame-shame ba sa motsi a cikin wata lalatacciyar mota da ke yashe a harabar wani gida.
Yaran waɗanda shekarunsu suka kama...
Rundunar ƴansanda a jihar Jigawa ta ce ta kama wani matashi da ake zargi da sassara mahaifinsa har lahira.
Lamarin ya faru ne a safiyar yau Litinin a garin Sara da ke karamar hukumar Gwaram.
Tuni aka yi jana'izar mahaifin matashin - inda shi kuma yake tsare a wajen ƴansanda.
Mai magana da yawun ƴansanda jihar SP Lawan Shi'isu Adam, ya shaida wa BBC cewa jami'ansu sun tarar da mahaifin cikin jini lokacin da suka isa gidansa.
"Yaron ya sassare mahaifin nasa a kafaɗarsa, ya kuma yanka maƙogoronsa har zuwa kirjinsa. Nan da nan aka ɗauke shi zuwa asibiti a Birnin Kudu inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa," in ji SP Lawan Shi'isu.
Ya ce an yi ƙoƙarin an kama matashin da kuma addar da ya yi amfani da ita wajen sare mahaifin nasa.
Kakakin ƴansandan ya ƙara da cewa yanzu suna ...
Wani yaro dan shekaru 13 da ya kamu da soyayya ya dauki hankula inda aka ji mahaifiyarsa na mai fada.
Mahaifiyar dai tace ta raba wannan soyayya.
https://twitter.com/MuhammadBa30385/status/1919148028918681668?t=3khYYKTQ76YgdUY5zEk5FQ&s=19
Inda tace zata je gidan su yarinyar.
Wannan wani barawon waya ne da rahotanni suka bayyana cewa ya zura hannu ne cikin mota zai saci wayar inda fasinjan dake cikin kotar suka kamashi.
https://twitter.com/Minikothe3rd/status/1919342570993279438?t=U0b9Qif9O70H_pbHXpHm3Q&s=19
An ga dai yanda aka rika marinshi.
Gwamnatin Kano Ta Ware Naira Miliyan 670 Don Siyan Motoci Ga Sunusi Lamido Sanusi, Duk Da Kalubalen Da Al’umma Ke Fuskanta.
A wani lamari da ke kara daukar hankalin jama’a, gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ware zunzurutun kudi har Naira ₦670,000,000 don sayen motoci na alfarma ga tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi.
Bincike ya nuna cewa kudaden za su fito ne daga asusun jihar Kano da kananan hukumomi 44, inda kowace karamar hukuma za ta bayar da ₦15,227,272 domin cika adadin kudin. Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata takarda mai lamba MLG/SNSNTLGD/166T/6 da aka fitar ranar 25 ga Maris, 2025. Kamfanin da aka ba kwangilar siyan motocin shi ne Sottom.
Wannan yunkuri na zuwa ne a daidai lokacin da jama’ar Kano ke fuskantar manyan ma...
Matashiya me suna Fatima ta bayyana cewa, Idai mace tagari kake nema to gani kasamu. Saboda ni nasan kaina.
Saidai wasu sun ce mata yabon kai Jahilci ne.