Tuesday, December 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

In ka ga dama ka tara duka Gwamnonin Najeriya a APC idan ‘yan Najeriya suka ki zabenka dole ka sauka>>El-Rufai ga Tinubu

Duk Labarai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya mayar da martani kan yanda Gwamnoni ke rububin komawa jam'iyyar APC. El-Rufai yace idan gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta ga dama, ta tara duka 'yan Adawa a jam'iyyar APC idan 'yan Najeriya suka ki zabensa dole ya sauka. El-Rufai yace kuma hadakar da suke ta 'yan Adawa tsaf cikin sauki zasu iya kawar da gwamnatin Tinubu ba tare da Gwamna ko daya ba. El-Rufai ya bayyana hakane yayin ganawa da 'yan Jarida a Kano, ranar litinin inda yace Idan Tinubu ya ga dama ya tara duka Gwamnonin Najeriya a APC amma idan 'yan Najeriya suka ki zabarsa shikenan ta kare. A jiyane dai APC ta karbi gwamnan jihar Delta daya canja sheka daga PDP. Hakanan Shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yace akwai karin gwamnoni da zas...
Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Gwamnoni da yawa zasu dawo APC Saboda Tinubu na mulki na Adalci>>Inji Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da tabbacin cewa, Gwamnoni da yawa zasu sake komawa jam'iyyar. Ya bayyana hakane a wajan taron karbar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da ya koma jam'iyyar ta APC. Ganduje ya jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda shugabanci na gari da yake samarwa a Najeriya. Ganduje yace a yanzu suna da gwamnoni 22 kenan a jam'iyyar APC inda yace mutane su saka ido su gani akwai karin gwamnonin da zasu dawo APC nan gaba.
Ku baiwa Zuciyarku hakuri ko tana so ko bataso ku sake zaben mu, saboda mu samu kammala gyaran da muka fara, idan kuka zabi wani shugaban kasa, ba Tinubu ba, za’a samu babbar matsala dan zai dakatar da duka ayyukan ci gaban da ya fara ne>>Gwamnatin Tinubu ta roki ‘yan Najeriya

Ku baiwa Zuciyarku hakuri ko tana so ko bataso ku sake zaben mu, saboda mu samu kammala gyaran da muka fara, idan kuka zabi wani shugaban kasa, ba Tinubu ba, za’a samu babbar matsala dan zai dakatar da duka ayyukan ci gaban da ya fara ne>>Gwamnatin Tinubu ta roki ‘yan Najeriya

Duk Labarai
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta mika kokon bararta ga 'yan Najeriya cewa su sake zabenta dan ta sami ta kammala gyaran da ta dauko na tattalin arziki. Gwamnatin tace idan aka zabi wani shugaban kasa wanda ba tituba, za'a samu matsala dan kuwa zai zo ya dakatar da dukkanin ayyukan da shugaba Tinubun ya fara ne. Ministan harkokin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na channels TV. Keyamo yace duk wani dan APC ko yana so ko bayaso ya kamata ya ajiye son zuciya ya yi aiki tukuru dan ganin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sake darewa kan mulki. Yace ta hakane kawai zai samu damar kammala ayyukan ci gaba da ya fara dan kuwa a baya an ga yanda idan aka zabi sabon shugaban kasa yake dakatar da ayyukan ci gaba n...
Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Abin Kunya:Wata Daya da gama gyaran Matatar Man fetur ta Warri ta sake lalacewa duk da kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar Man fetur ta Warri da gwamnati ta kashe Dala Miliyan $897m wajan gyaranta ta sake lalacewa. Rahoton yace ko da aka kammala gyaran, matatar man ta fara aiki a watan Nuwamta na shekarar data gabata ne kuma kaso 40 cikin 100 na matatar ne ke aiki. Saidai a ranar January 25, 2025 an sake kulle matatar ta daina aiki saboda ta kara lalacewa. An yi wannan gyaranne a karkashin shugabancin Tsohon shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari wanda tuni ya ajiye aiki. Wannan lamari yasa ana sukar kamfanin na NNPCL da gazawa.
A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

A kokarin da masana kimiyya ke yi na Gano karshen Kasar da muke takawa, sun samu ci gaba inda suka yi nisa sosai a hakar da suke yi amma har yanzu basu kai karshen kasar ba

Duk Labarai
Masana kimiyya sun sanar da samun gagarumar ci gaba a kokarin da suka shafe shekara da shekaru suna yi na ganin sun gano karshen kasar da muke takawa. Masanan dai suna haka ce kamar yanda ake haka rijiya dan gano karshen kasa. A wannan karin sun ce sun yi haka a karkashin kasa da nisanta ya kai mita 1,268, wannan ba karamin ci gaba bane lura da cewa a farko burinsu shine su yi hakar da nisanta bai wuce mita 200 ba. Dalilin su na ci gaba da hakar shine sun ga lamarin yana da dauki ba kamar yanda suka yi tsammanin zasu sha wahala ba Saidai har yanzu basu kai karshen kasa ba. Kasar Amurka ce dai ke daukar nauyin wannan aiki, saidai ta dakatar da bayar da kudin gudanar da aikin wanda hakan ke barazana ga ci gaban aikin.
Hankula sun tashi bayan da Masu kutse suka kwashewa mutane kudinsu a Bankin Union Bank har Naira Biliyan 9.3

Hankula sun tashi bayan da Masu kutse suka kwashewa mutane kudinsu a Bankin Union Bank har Naira Biliyan 9.3

Duk Labarai
Rahotanni sun ce masu kutse sun kwashewa Kwastomomi kudadensu har Naira Biliyan 9.3. Rahoton yace bankin na ta kokarin ganin ya dawo da wadannan kudade da aka sace. Sannan tuni aka rufe wasu asusun ajiya da ake tsammanin na da alaka da satar. Lamarin ya farune ranar 23 ga watan Maris da ya gabata. Bankin a ranar 2 ga watan Afrilu ya nemi kotu ta bashi damar kulle wasu asusun banki da suka ce har yanzu ana amfani dasu wajan satar kudaden. Ba wannan ne karon farko ba, Watanni 15 da suka gabata sai da babban bankin Najeriya CBN ya rushe hukumar gudanarwar bankin kan irin wannan lamari
Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Sarakunan Inyamurai sun ce Tinubu ne zabinsu a 2027

Duk Labarai
Sarakunan yankin Inyamurai sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu alkawarin samar masa akalla kaso 70 cikin 100 na kuri'un da za'a kada a yankunansu. Sarakunan wanda basaraken Abia, Eze Nnamdi yake jagoranta sun bayyana hakane yayin da suka kaiwa mataimakin kakakin majalisar dattijai, Benjamin Kalu ziyara a gidansa dake Abia Sunce babban dalilin ziyararsu shine dan mika godiya ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bisa kafa ma'aikatar raya yankinsu. Sannan sun kuma Godewa Sanata Kalu saboda kokarin da yayi na kafa wannan ma'aikata.
Ji Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Ji Yadda ma’aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsìraìcìn abokan aikinsa mata a Najeriya, ya nadi Bidiyo 400

Duk Labarai
Yadda ma'aikacin banki ya riƙa naɗar bidiyon tsiraicin abokan aikinsa mata a Najeriya. Rundunar ƴansanda a jihar Legas da ke Najeriya ta ce za ta gurfanar da tsophon ma'aikacin bankin Access wanda ake zargi da ɗaukar hotunan tsiraicin abokan aikinsa mata. Wannan na zuwa ne bayan wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Litinin inda ya bayyana cewa ya miƙa batun zargin ɗaya daga cikin ma'aikatansu a ɓangaren hulɗa da abokan cinikayya, na ɗaukar hotunan tsiraici ga hukumomi. Sanarwar da suka wallafa a shafin sada zumunta ta ce bankin zai bai wa hukumomi haɗin kai, kuma bankin zai ci gaba da kare mutuncin ma'aikatansa. Bayani da ya fita a makon da ya gabata ya nuna cewa wani ma'aikacin bankin Access ya naɗi bidiyoyin abokan aikinsa mata a cikin ban-ɗaki ba tare da saninsu ba....