Karanta Jadawalin manyan gurare 7 da aka sakawa sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu tun bayan da ya hau mulki
Tun daga 29 ga watan Mayu na shekarar 2023 bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zama shugaban Najeriya, an sakawa manyan gurare na gwamnati guda 7 sunansa.
Daga cikin abubuwan da aka sakawa sunan Shugaban kasar akwai tituna, Barikin sojoji, dakunan taro da sauransu.
Wata kungiyar rajin kare hakkin bil'adama me suna (NEFGAD) ta bayyana hakan a matsayin abinda bai dace ba dan ya sabawa aikin gwamnati.
Ga jadawalin gurare 7 da aka sakawa sunan shugaban kasar kamar haka:
Babban Filin Jirgin sama na jihar Naija.
A ranar March 10, 2024 ne gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya sakawa babban filin sauka da tashin jiragen jihar dake Minna sunan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Titun Abuja Southern Parkway.
A ranar May 28, 2024 ne bayan kammala titin Abuja Southern Parkway...








