Ji bayani Dalla-Dalla: DA KYAR JAMI’AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA
DA KYAR JAMI'AN TSARO SUKA KWACI MADAGWAL A HANNUN MABIYA KWANKWASIYYA DUK KUWA DA CEWA YA TUBA.
Rahotanni daga Jihar Kano sun bayyana bayyana cewar sai dai aka hada da jami'an tsaro aka ceci Dan wasan barkwanco Ali Art-work Wanda aka fi sani da Madagwal.
Madagwal ya fada komar Yan Kwankwasiyya ne jiya Lahadi lokacin daya sake zuwa karbar darikar Kwankwasiyyar, a hannun Ubanta Injiniya Rabiu Musa, a wani taro da suka gudanar na bikin Sallah a Jihar.
Kafin Yanzu bayan ficewar sa a shekararun baya Madagwal ya koma suka da jefa kalaman batanci ga Rabiu Musa Kwankwaso da sauran Magoya bayan sa.
Haka Kuma ya sha chachchakar salon Mulkin Abba Kabir Yusuf, tare da bukatar cewar Kwankwaso ya yiwa Gwamnatin Jihar Kano kakagida shi yasa baa tabuka abun a zo a gani.
Wannan ya Saka ...








