Thursday, March 26
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Daga karshe Malam dogo dai ya hadu mataimakin shugaban kasa a fadar gwamnati, kuma ya cika burinshi na shan fura da sugar har ma ya samu karin coke da kuma jarin sana’a na Naira Miliyan biyu

Daga karshe Malam dogo dai ya hadu mataimakin shugaban kasa a fadar gwamnati, kuma ya cika burinshi na shan fura da sugar har ma ya samu karin coke da kuma jarin sana’a na Naira Miliyan biyu

Duk Labarai
Daga karshe Malam dogo dai ya hadu mataimakin shugaban kasa a fadar gwamnati, kuma ya cika burinshi na shan fura da sugar har ma ya samu karin coke da kuma jarin sana'a na Naira Miliyan biyu. https://www.tiktok.com/@kashim_shettima_bmk/video/7501855169555025157?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7501855169555025157&source=h5_m&timestamp=1746728715&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7496016997063755575&share_link_id=662a895f-b05b-45cb-a1dc-41cfd2f2c006&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_bt...
Robert Prevost ne sabon fafaroma

Robert Prevost ne sabon fafaroma

Duk Labarai
Fadar Vatican ta sanar da cewa Robert Prevost ne sabon fafaroma, wanda zai maye gurbin Fafaroma Francis. Shi ne fafaroma na farko daga ƙasar Amurka wanda zai jagoranci cocin na Katolika na duniya. Zai yi amfani da sunan Leo a muƙamin - wanda shi ne fafaroma na 14 da ya yi amfani da sunan (Pope Leo XIV). Sabon Fafaroman mai shekara 69 ya shafe shekaru yana ayyukan addini a ƙasar Peru. A watan Satumban 2023 ana naɗa shi a muƙamin babban limamin Cocin Katolika wato ''Cardinal'. Ana kallon Robert Prevost a matsayin mutum mai matsakaicin ra'ayin. Za mu ci gaba da sabnta wannan labari...
Tumaki sun fi mutane yawa a ƙasar New Zealand – Rahoto

Tumaki sun fi mutane yawa a ƙasar New Zealand – Rahoto

Duk Labarai
Awaki sun fi mutane yawa a ƙasar New Zealand - Rahoto. Kididdigar da Hukumar Gwamnatin New Zealand ta fitar ta nuna cewa har yanzu yawan awaki ya fi na mutane a kasar. Duba da yawa tumaki har miliyan 23.6 da kuma yawan mutane da ya kai miliyan 5.3, akwai kimanin tumaki 4.5 ga kowane ɗan New Zealand, kamar yadda ƙididdiga ta nuna. Bisa kididdigar da aka yi, wannan ya ragu daga tumaki 22 nan ga kowane mutum a cikin 1982, lokacin da noman tumaki don nama da ulu ya kasance mafi girma a New Zealand.
Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni”>>Inji Wannan tsohon Abokin nasa

Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni”>>Inji Wannan tsohon Abokin nasa

Duk Labarai
Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni" Wasu Zasuce Karya nakeyi ko Sharri nake masa, amma kuje Ku Tambayeshi Waye Haruna masta, Bazai Taba mantawa ba, domin Bayan yadawo daga makarantar Allo baida wani abokin da suke Tare kullum sai Ni, Kudin Da Zai fara zuwa Studio Ya Rera waka Ni na bashi Aro ₦2500, Tun bayan fara wakarsa Yabar unguwar mu, Duk irin neman da zan masa nayi Domin ya Sakamun irin taimakon da nayi masa, amma baya Daukan waya Tun A baya cen, Yanzu ma banida Number da ake samun sa" Duniya kenan Kayiwa Mutum Rana yayi maka Dare.
Ji yanda aka kai Amarya da Uwar gida Asibiti bayan da suka sha maganin kayan Mata da ya fi karfinsu dan su burge mijinsu

Ji yanda aka kai Amarya da Uwar gida Asibiti bayan da suka sha maganin kayan Mata da ya fi karfinsu dan su burge mijinsu

Duk Labarai
An kai Uwargida da Amarya Asibiti bayan da suka sha maganin kayan mata dan su burge mijin su. Lamarin ya farune a garin Dakwa dake yankin Bwari na babban birnin tarayya, Abuja. Sun sha wannan maganin ne bayan da mijinsu yayi sabuwar Amarya dan su ma ya ji su zanzan. Mijin ya je jiharsa ta Zamfara inda ya karo auren mata ta 3. Da yake gayawa manema labarai yanda lamarin ya faru, mijin me suna Musa Muhammad yace yana dayan gidansa sai aka kirashi aka ce matansa sun kwanta basu da lafiya. Yace da ya je sai ya gansu suna ta birgima a kasa cikinsu na ciwo, yace da farko ya kira wata Nurse ce dan ta dubasu, inda ta saka musu karin ruwa. Yace amma abin yaki ci yaki cinyewa, dole aka kaisu Asibitin madalla inda likitoci suka ce maganin matan da suka sha ne har ya fara lalata musu...
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Duk Labarai
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo. Rundunar ƴansandan jihar Imo ta rage wa wani ɗansanda mai muƙamin Sajan, Anayo Ekezie mukamin sa saboda cin zarafin wani dattijo. Wani faifan bidiyo na yadda wasu ƴansanda ke cin zarafin wani mutum a kan hanyar Owerri zuwa Aba ya bazu a kwanakin baya. Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, Henry Okoye, a jiya Laraba, ya tabbatar da cewa an gano ‘yansandan tare da tsare su. Ya ce an samu ƴansandan uku da lamarin ya shafa, inda ya kara da cewa an rage wa Ekezie mukami zuwa Kofur, yayin da aka ja wa sauran biyun kunne.