Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bayan da taje majalisar Dinkin Duniya, Kafar Skynews da BBC, Sanata Natasha ta kuma je gidan yada labarai na DW inda a can ma tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Bayan da taje majalisar Dinkin Duniya, Kafar Skynews da BBC, Sanata Natasha ta kuma je gidan yada labarai na DW inda a can ma tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Duk Labarai
Da alama dai Sanata Natasha Akpoti bata da shirin hakura da maganar zargin nemanta da lalata da sanata Godswill Akpabio yayi ba. A ci gaba da neman hakkinta, a yanzu ta bayyana a kafar yada labarai ta DW inda a can ma ta bayyana irin zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio. Sanata Natasha Akpoti a baya dai ta yi irin wannan bayyana a kafar Skynews da BBC. Hakanan ta je majalisar Dinkin Duniya. Da alama dai so take sai ta karade duka kafafen yada labarai na Duniya da wannan zargi nata.
An bayyana dan siyasa daya tal dake kayarwa da shugaba Tinubu gaba a zaben 2027

An bayyana dan siyasa daya tal dake kayarwa da shugaba Tinubu gaba a zaben 2027

Duk Labarai
A yayin da ake fuskantar zaben shekarar 2027 an bayyana dan siyasa daya tilo da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ke shakkar karawa dashi a shekarar 2023. Wani dan kasuwa, Stephen Akintayo ne ya bayyana hakan inda yace Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ne ke kayarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gaba. Ya bayyana cewa, idan aka hada Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai a matsayin mataimakinsa, Tinubu ba zai iya bacci ba.
Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Duk Labarai
Sanatoci 3 ne kacal suka ciri tuta inda suka ki amincewa da dakatar da gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi. A jiya ne dai majalisar dattijai data wakilai suka hada baki suka amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa Gwamnan Rivers. Saidai an bayyana sanatoci Seriake Dickson, da Enyinnaya Abaribe, da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a matsayin wadanda suka ki amincewa da wannan aniya ta shugaba Tinubu. Rahoton yace wadannan sanatoci ficewa suka yi daga zauren majalisar kamin kakakin majalisar ya bayyana amincewa da kudirin.
Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri

Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri

Duk Labarai
Idan Har Ɗan El-Rufai Bai Yarda Da SDP Ba, Wane Ɗan Nijeriya Ne Mai Hankali Zai Yarda Da Wannan Jam’iyya, Inji Reno Omokri. Nasir el-Rufai yana gayyatar Waziri Atiku Abubakar, Peter Obi, Rotimi Amaechi, da Kayode Fayemi su shiga jam’iyyar SDP tare da shi. Amma kawai wàwà ne zai amince da irin wannan gayyata, alhalin ma ɗansa, Bello El-Rufai, bai bar APC ya bi mahaifinsa ba. Daga Muhammad Kwairi Waziri
Kotu ta hana INEC shirya zabe dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Kotu ta hana INEC shirya zabe dan yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, babbar Kotun tarayya dake Lokoja ta hana yiwa Sanata Natasha Akpoti kiranye. Kotun tace kada hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sake ta amince da bukatar shiryawa sanata Natasha Akpoti kiranye. Wani me suna Anebe Jacob Ogirima ne da wasu mutane hudu daga mazabar ta Sanata Natasha Akpoti suka shigar da bukatar a gaban kotun. Mai shari'a Justice Isa H. Dashen ta amince da bukatar tasu. Sannan an dage sauraren karar sai nan da 6 ga watan Mayu. A baya dai Bidiyo da hotuna aun bayyana na mutanen mazabar Sanata Natasha Akpoti inda aka ga ana shirya zaben yi mata kiranye. Sanata Natasha Akpoti ta fara samun matsala ne tun bayan da ta zargi kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio da neman ta da lalata.
Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka, Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Sanata Godswill  Akpabio tonon silili inda tace harfa gaya mata yayi wai mijinta na morewa dan da gani tana juya masa kugunta da kyau

Kalli Bidiyo: Cikin sheshshekar kuka, Sanata Natasha Akpoti ta sake yiwa Sanata Godswill Akpabio tonon silili inda tace harfa gaya mata yayi wai mijinta na morewa dan da gani tana juya masa kugunta da kyau

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti a hirar da aka yi da ita a kafar BBC ta bayyana cewa bata san me yasa wasu 'yan Najeriya basa gane irin halin da take ciki ba. Tace tana son ta samu guri ne da zata yi aiki ba tare da ana nemanta da lalata ba. Tace Sanata Godswill Akpabio har ce mata ya taba yi mijinta na morewa dan da gani tana juya masa duwawunta da kyau. Sanata Natasha Akpoti tace mata da yawa daga kasashen Africa daban-daban sun kirata inda suka rika gaya mata cewa suma suna fuskantar irin wannan cin zarafi a guraren aikinsu. Tace maganar cewa bata bi dokar majalisa bane yasa aka dakatar da ita ba gaskiya bane. kalli Bidiyon hirar anan
Addini Sauki Gareshi:Ko Tuntunbe ka yi zaka iya ajiye Azumi>>Inji Young Sheikh

Addini Sauki Gareshi:Ko Tuntunbe ka yi zaka iya ajiye Azumi>>Inji Young Sheikh

Duk Labarai
Young Sheikh dake Tafsirin Azumin watan Ramadan a birnin Zazzau na jihar Kaduna ya bada fatawar cewa ko tuntube mutum yayi zai iya ajiye Azumi. Yace ko ciwo mutum yaji ma zai iya ajiya Azumin dan an ce wanda bashi da lafiya ko matafiyi an sauwaka masa ya ajiye azumi idan Ramadan ya wuce ya rama. Yace wannan hukunci shima zai iya hawa kan wanda yayi Tuntube. Kalli Bidiyon anan
Ku gama hauragiyarku, Tabbas, Babu tantama Tinubu ne zai sake zama shugaban kasa a 2027>>Inji Shugaban APC, Ganduje

Ku gama hauragiyarku, Tabbas, Babu tantama Tinubu ne zai sake zama shugaban kasa a 2027>>Inji Shugaban APC, Ganduje

Duk Labarai
Shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa 'yan Adawa su gama duk wata hadaka da zasu yi, Tabbas Tinubu ne zai sake zama shugaban kasa a shekarar 2027. Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawu sa, Oliver Okpala. Ganduje yace hadakar SDP, Labour Party da PDP babu inda zata je dan kuwa kowane daga cikinsu yana da ra'ayi dabanne dan haka ba zasu samu matsaya ba. Ya bayyana 'yan Adawar a matsayin masu son kansu maimakon kishin al'umma.
Karyace:Fubara ya mayarwa da shugaba Tinubu martani bayan da yace bai tabuka komai ba yayin da aka kaiwa Bututun man fetur din Najeriya hari

Karyace:Fubara ya mayarwa da shugaba Tinubu martani bayan da yace bai tabuka komai ba yayin da aka kaiwa Bututun man fetur din Najeriya hari

Duk Labarai
Gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar, Simi Fubara ya bayyana cewa ba gaskiya bane ikirarin da shugaban kasa yayi na cewa bai tabuka komai ba kan matsalar tsaron da ta kunno kai a jihar. Ya kuma karyata ikirarin shugaban kasar na cewa ya rushe majalisar jihar Rivers ba tare da gina wata ba. A martanin da ya mayar ta hannun me magana da yawunsa,Nelson Chukwudi Gwamna Fubara ya bayyana cewa, abin mamakine fadar shugaban kasar na magana akan abinda basu da masaniya akansa. Yace ko da yake ya dora Alhakin hakan akan masu baiwa shugaban kasar bayanai wanda sune suka kasa bashi bayana da ya kamata yayi amfani dasu wajan yin shawara. Fubara yace maganar da tsohon gwamnan jihar, kuma ministan Abuja a yanzu, Nyesome Wike yayine tasa aka kai harin. Yace ...