Monday, February 23
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Nine kadai zan iya kawowa kasarnan ci gaba, Hadakar Atiku, El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi taron mutanene wanda ke son kansu kawai ba son Al’umma ba>>Inji Tinubu

Nine kadai zan iya kawowa kasarnan ci gaba, Hadakar Atiku, El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Peter Obi taron mutanene wanda ke son kansu kawai ba son Al’umma ba>>Inji Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana hadakar da manyan 'yan Adawa suka yi da taron wanda damuwa tawa yawa. Ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Bayo Onanuga. Hakan na zuwane bayan da Atiku Abubakar, Nasiru Ahmad El-Rufai, Rotimi Amaechi, Peter Obi, Kayode Fayemi da sauransu suka hada kai suka ce zasu kayar da Tinubun a zaben shekarar 2027. Sanarwar ta fadar shugaban kasa ta bayyana hadakar 'yan Adawar da cewa masu son kansu ne kawai ba masu kishin al'umma ba. Ya kuma bayyana cewa ci gaban kasa ne Bola Ahmad Tinubu ya saka a gaba, kuma shi kadai ne zai iya kawo ci gaban dan haka ba zai bari wasu taron sakarkaru su dauke masa hankali game da aikin da yake ba.
A karshe dai bayan da ya sha suka, Shima Kwankwaso ya fitar da Nasa Allah wadai din ga dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

A karshe dai bayan da ya sha suka, Shima Kwankwaso ya fitar da Nasa Allah wadai din ga dakatarwar da Shugaba Tinubu yawa Gwamnan jihar Rivers

Duk Labarai
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin amincewarsa da dakatar da gwamnan jihar Rivers da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi. Saidai bayyana ra'ayin nasa na zuwane bayan da ake ta tambayar ina ya shigene yayin da ake jin ta bakin manyan 'yan Adawa akan lamarin? Kwankwaso yace ya dakata ne ya ga wanda ke da ruwa da tsaki a cikin lamarin sun yi abinda ya dace shiyasa yayi shiru bai ce komi ba da farko. Saidai yace a yanzu yana Allah wadai da wannan mataki inda yace majalisar tarayya ta zama 'yan amshin shata da ba'a taba samun kamarsu ba a tarihin mulkin Najeriya. Yace sune ya kamata su rika dawo da shugaban kasa kan hanya idan ya aikata ba daidai ba amma gashi sun zama 'yan amshin shata. Kwankwaso yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya mayar da ...
Tonon silili: An gano cewa Dala Biliyan $3 aka rabawa Sanatoci suka amince da dakatar da gwamnan jihar Rivers, inda wasu sanatocin suka samu dala dubu 10 wasu suka samu dala dubu 5

Tonon silili: An gano cewa Dala Biliyan $3 aka rabawa Sanatoci suka amince da dakatar da gwamnan jihar Rivers, inda wasu sanatocin suka samu dala dubu 10 wasu suka samu dala dubu 5

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, dala Miliyan $3 ce aka ware aka rabawa sanatocin Najeriya dan su amince da dakatarwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yawa gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara. Rahoton yace a gidan Kakakin majalisar, Godswill Akpabio aka raba wadannan kudade a tsakannin ranekun Talata da Laraba. Rahoton yace wasu daga cikin sanatocin sun samu dala dubu $10 inda wasu suka samu dala Dubu $5 ya danganta da girman mukamin sanata. Rahoton ya kara da cewa Akpabio ya kira wasu sanatoci musulmai zuwa gidansa shan ruwa inda anan ne ya basu kasonsu, saidai wasu sanatoci ciki hadda tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal basu amsa wannan gayyata ba. Rahoton yace Wike ne ya baiwa Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio kudaden da aka raba.
Shugaba Tinubu ya godewa Majalisar Tarayya saboda amincewa da dakatar da Gwamnan Rivers da suka yi

Shugaba Tinubu ya godewa Majalisar Tarayya saboda amincewa da dakatar da Gwamnan Rivers da suka yi

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya godewa Majalisar tarayya bisa amincewa da dakatar da gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara da yayi. Shugaban yace yana godiya musamman ga shuwagabannin majalisar, Kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio dana majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas. Sannan yace yana godiya ga sauran manyan 'yan majalisar dama duka 'yan majalisar. Shugaban ya kuma ce yana godiya ga 'yan Najeriya da suka bashi goyon baya bisa wannan lamari. Ya bayyana cewa yana fatan nan da wata 6 din da aka dakatar da gwamnan da majalisar a samu sulhu tsakanin wadanda basa jituwa. Shugaba Tinubu yace fadan jihar Rivers yana barazanane ga tattalin arzikin Najeriya shiyasa suka dauki matakin da suka dauka. Ya sha Alwashin ci gaba da hada kai da majalisar tarayya dan kawo ci gaba ...
A watan Maris matasa masu bautar kasa zasu fara karbar Alawus din Naira dubu 77>>Inji NYSC DG

A watan Maris matasa masu bautar kasa zasu fara karbar Alawus din Naira dubu 77>>Inji NYSC DG

Duk Labarai
Hukumar kula da masu bautar kasa a Najeriya, NYSC ta baiwa matasa masu bautar kasar tabbacin cewa, a watan Maris zasu fara ganin karin Alawus zuwa Naira 77,000. Shugaban hukumar, Brigadier General Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da matasan masu bautar kasa a ranar Alhamis. An yi taron ganawar ne a Wuse da Garki a Abuja. Brigadier General Nafiu ya bayar da tabbacin cewa Gwamnatin tarayya da Hukumar ta NYSC na kokarin ganin sun jiyawa matasan masu bautar kasa dadi.
Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Majalisar Dattawa ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Rivers

Duk Labarai
Majalsiar Dattawa ta amince da dokar ta-ɓaci da shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ayyana a kan jihar Rivers a ranar Talata. Majalisar dai ta shiga tattaunawar sirri bayan da shugaban majalisar Godswill Akpabio ya karantar wasiƙar a zauren. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele ne ya karanta buƙatar shiga tattaunawar ta sirri bisa dogaro da doka mai 135 ta kundin majalisar. Shugaban marasa rinjaye, Sanata Abba Moro ne ya amince da shiga ganawar sirrin. Da ma dai majalisar wakilai ta amince da wannan dokar ta ta-ɓaci a ranar Alhamis.
Hukumar Nimet ta gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya

Hukumar Nimet ta gargaɗi kan ɓullar cutar sanƙarau a Najeriya

Duk Labarai
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya Nimet ta yi gargaɗin cewa wasu jihohin arewacin ƙasar na ƙara fuskantar barazanar ɓarkewar cutar sanƙarau. Nimet a cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X, ta ce jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauchi da Yobe da Gombe da kuma Borno su ne suka fi fuskantar barazanar. Hukumar ta kuma ce alamomin cutar sanƙarau sun haɗa da zazzaɓi mai zafi da ciwon kai mai tsanani da riƙewar wuya da amai, sai rashin son kallon haske da ruɗewa da kuma ƙuraje. Nimet ta kuma ƙara da cewa ana iya kamuwa da cutar da hanyar mu'amula da masu ɗauke da cutar da kuma shiga cunkoso, inda ta buƙaci alumma su yi rigakafi su wanke hannu su kuma gujewa kusantar masu cutar su kuma rufe bakinsu da hanci. Hukumar ta kuma yi kira ga alumma da...
Har yanzu Hoton Gwamna Fubara na rataye a fadar Gwamnatin jihar Rivers duk da dakatar dashi da shugaba Tinubu yayi

Har yanzu Hoton Gwamna Fubara na rataye a fadar Gwamnatin jihar Rivers duk da dakatar dashi da shugaba Tinubu yayi

Duk Labarai
Wanda shugaban kasa, Bola Ahmad ya baiwa rikon kwaryar gwamnan jihar Rivers, Vice Admiral Ibokette Ibas ya koma jihar ya shiga gidan gwamnatin jihar bayan da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya rantsar dashi a Abuja. Saidai wani abu da aka lura dashi shine har yanzu hoton Fubara na nan a sagale a matsayin gwamnan jihar a Ofishin gwamnan.
Kuma Dai: Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Kuma Dai: Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila tawa Sanata Godswill Akpabio tonon silili

Duk Labarai
Sanata Natasha Akpoti ta je kafar Skynews ta kasar Ingila inda ta yiwa Sanata Godswill Akpabio tonon silili. A can ma dai ta sake bayyana yanda Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata. Ta musanta ikirarin Majalisar Dattijai na cewa an dakatar da itane saboda rashin biyayya ga dokokin majalisar inda tace me yasa sai da ta gabatar da korafi akan sanata Godswill Akpabio ne sannan za'a dakatar da ita? Sanata Natasha ta bayyana cewa ta yi ta kai korafi dan neman yiwa mutanenta aiki amma sai sanata Godswill Akpabio yaki amincewa. Tace har mijinta saboda abokin Sanata Godswill Akpabio ne ya rika rokonsa akan ya amince da wasu kudirori data kai majalisar amma ya kiya sai yace sai nan gaba.
Kalli Hotuna:Yanda Wani dan Siyasa a jihar Kogi ya rabawa mutanen mazabarsa tayar mashin dan su dogara da kansu

Kalli Hotuna:Yanda Wani dan Siyasa a jihar Kogi ya rabawa mutanen mazabarsa tayar mashin dan su dogara da kansu

Duk Labarai
Wani Dan siyasa a jihar Kogi wanda dan majalisa ne me suna, Hon. Idowu ibikunle ya dauki hankalin Duniya bayan da aka ga yana rabawa mutanen mazabarsa Tayar mashin dan su dogara da kansu. https://www.youtube.com/watch?v=GRU9hUEaYq8&pp=0gcJCfcAhR29_xXO Abin dai ya baiwa mutane da yawa mamaki inda suke tambayar ta yaya tayar mashin zata taimaki mutum.