Sunday, February 22
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai a tarihi

Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Premier na wata karo bakwai a tarihi

Duk Labarai
Ɗan wasan Liverpool, Mohamed Salah ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan gasar Premier na wata-wata karo na bakwai a tarihin. Mohamed Salah ya lashe kyautar watan Fabrairu a matsayin ɗan wasan da ya fi hazaƙa a watan, bayan da bajintar da ya yi a watan, a ƙoƙarin da ƙungiyarsa ke yi na lashe gasar Premier. Ɗan wasan na ƙasar Masar ya ci ƙwallo shida, ciki har da biyu da ya zura a ragar Bournmouth da wanda ya zura a ragar Manchester City a watan, sannan ya taimaka aka ci huɗu. Mo Salah ya samu kyautar ne bayan doke Beto da Jean-Philippe Mateta da Yankuba da Djed Spence da kuma Dominik Szoboszlai. Da wannan nasara, a yanzu Salah ya kamo tarihin da Sergio Aguero da Harry Kane suka kafa na cin kyautar sau bakwai. Sannan ya zarta Steven Gerrard da Cristiano Ronaldo waɗanda suka ci k...
Wata mata ta kkàshè kishiyarta a jihar Jigawa

Wata mata ta kkàshè kishiyarta a jihar Jigawa

Duk Labarai
Hukumomin ƴansanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun cafke wata mata bisa zarginta da kashe kishiyarta ta hanyar zuba mata ruwan zafi. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Buju da ke ƙaramar hukumar Dutse babban birnin jihar Jigawa, kuma bayanai na cewa matar ta rasa ranta ne sakamakon rashin jituwar da ta kaure tsakaninta da abokiyar zamanta. Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam ya shaida wa BBC cewa matar ‘yar shekara 20 ta watsa wa abokiyar zamanta tafasasshen ruwan zafi ne, sakamakon taƙaddamar da ta kaure tsakaninsu. SP Shi’isu Adam ya ce marigayiyar ta samu mummunan ƙuna, inda aka kai ta asibiti daga baya kuma ta rasu a can. Mai unguwar ƙauyen, Malam Kabiru Abbas ya shaida wa BBC cewa bayan ƙura ta lafa, wadda aka watsa wa ruwan zafin, kafin ...
El-Rufai ya bude shafin TikTok, ya samu mabiya 200,000 cikin Awa 24

El-Rufai ya bude shafin TikTok, ya samu mabiya 200,000 cikin Awa 24

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bude shafi a dandalin sada zumunta na TikTok. Cikin awa 24 kacal da budewa, El-Rufai ya samu sama da mabiya 200,000, yayin da bidiyon sanarwarsa ya tara masu kallo miliyan 1.9 da kuma sharhi (Comment )sama da 21,000. A cikin bidiyon, El-Rufai ya bayyana cewa shafinsa na TikTok zai mayar da hankali kan ra’ayoyinsa a siyasa da kuma sabuwar jam’iyyarsa, SDP. "Wannan shine kawai shafina na gaskiya a TikTok. Ku biyo ni domin kallon bidiyo, yin sharhi da tattaunawa kan siyasar Najeriya da ayyukan sabuwar jam’iyyarmu, SDP. Maraba da ku," in ji shi.
Da Ban cire tallafin man fetur da daukar matakai masu tsauri ba da Najeriya ta talauce saboda shuwagabannin da suka gabata wadaka suka yi da dukiyar daya kamata a gina Al’umma>>Tinubu

Da Ban cire tallafin man fetur da daukar matakai masu tsauri ba da Najeriya ta talauce saboda shuwagabannin da suka gabata wadaka suka yi da dukiyar daya kamata a gina Al’umma>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewada bai cire tallafin man fetur ba da daukar tsauraran matakai na gyaran tattalin arzikin ba da Najeriya ta talauce. Yace amma matakan da ya dauka hadi da goyon baya da hakurin da 'yan Najeriya suka yi masa yasa a yanzu gashi an fara cin amfanin abin. Yace Farashin kayan abinci ya sauka musamman a cikin watan Ramadana sannan kuma gashi Darajar Naira na ta farfadowa a hankali. Shugaban ya bayyana hakane a yayin da ya karbi bakuncin 'yan majalisa da suka yi aiki tare a lokacin yana dan majalisa. Ya kuma bayyana tsarin Dimokradiyya a matsayin tsari mafi kyawu wanda shine yake kawowa kasa ci gaba.
Mata tasa ‘yansanda sun kama mijinta saboda ya kara aure

Mata tasa ‘yansanda sun kama mijinta saboda ya kara aure

Duk Labarai
Wata mata a jihar Legas tasa 'yansanda sun kama mijinta aun kulle bayan da ya kara aure. Mutumin me suna Charles Chiawa an tsareshi a ofishin 'yansanda kamar yanda matarsa, Uche Chiawa ta bukata. Sun shafe shekaru 20 da yin aure inda Charles yace sun fara samun matsala ne bayan da ya kara aure har ya haihu da amaryarsa. Yace yana da damar kara aure saboda auren gargajiya aka musu shi da uwar gidansa. Saidai matar tasa Uche tace ba auren gargajiya kadai suka yi ba, hadda na kotu kuma tace yana yawan dukanta ne shiyasa tasa a tsareshi. Rahoton yace uwargidan mutumin na da alaka da wata DPO na 'yansanda wanda hakanne ya bata damar sawa a daureshi. Amaryarsa ta je ofishin 'yansandan inda ta nemi a sakeshi amma aka ki bata belinsa aka koreta. Saidai da aka nemi jin ta baki...
Ji yanda Wani mutum ya yanke jiki ya fadi ya mùtù a akin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin ficewa daga dakin

Ji yanda Wani mutum ya yanke jiki ya fadi ya mùtù a akin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin ficewa daga dakin

Duk Labarai
Wani mutum dan kimanin shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi ya mutu a dakin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin fita daga dakin. Lamarin ya farune a sabuwar Kutunku dake Gwagwalada a baban birnin tarayya, Abuja. Lamarin ya farune ran Asabar da misalin karfe 5 na yamma inda karuwar data ga haka ya ruga ta sanar da manajansu. Manajan ya garzaya dakin inda ya gane mutumin me suna Ajayi Nicholas inda ya yi gaggawar sanar da 'yan uwansa dake yankin. An garzaya dashi Asibiti inda acan likitoci suka tabbatar da ya mutu 'Yansanda sun je wajan inda suka gudanar da bincike kuma tuni aka kai gawar wanda ya mutun makwanci.
Abinda sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa mutane su fara jin tsoron baiwa mata matsayin siyasa>>Sanata Godswill Akpabio

Abinda sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa mutane su fara jin tsoron baiwa mata matsayin siyasa>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Sanata Godswill Akpabio wanda shine kakakin majalisar dattijai ya bayyana cewa, abinda Sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa a fara jin tsoron baiwa mata mukaman siyasa. Ya bayyana hakanne inda yace yanzu da Kamala Harris ta yi irin wannan abin da Sanata Natasha Akpoti ta yi da zata kai matsayin mataimakiyar shugaban kasa? Yace amma yana kira ga mutane da kada laifin wani ya shafi wani, yace yana da 'ya'ya mata 4 yana son a goyi bayansu da basu dama su kai matsayi babba dama sauran mata na Najeriya.
Allah Sarki:Ji yanda wata mata ta yanke jiki ta fadi ana tsaka da tafsirin Azumin watan Ramadana

Allah Sarki:Ji yanda wata mata ta yanke jiki ta fadi ana tsaka da tafsirin Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Wata mata me suna Maman Zainab dake da kimanin shekaru 42 ta yanke jiki ta fadi ta rasu a yayin da ta halarci wajan tafsirin Azumin watan Ramadana. Lamarin ya farune a Masallacin Gawu dake Abaji a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Unguwar me suna Ismail Bala ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin. Inda yace abin ya farune ranar Talata da misalin karfe 11:23 na safe. Matar dai ta bar gida lafiya Qalau inda makwabtanta 3 suka rakata zuwa wajan Tafsirin saidai ana tsaka da Tafsirin, ta gayawa na kusa da ita cewa tana jin jiri. Ta mike zata tashi sai ta yanke jiki ta fadi. Sauran matan sun dauke zuwa Asibiti a Gawu Babangida inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu. Likita ya bayyana hawan jini a matsayin abinda yayi sanadiyyar mutuwar ta. Tuni aka...