Wednesday, March 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà’àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà’àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Duk Labarai
Najeriya ce ta zo matsayi na 6 a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan ta'addanci a Duniya a shekarar 2025. A shekarun 2023 da 2024 Najeriya tana matsayi na 8 ne. Kasar Burkina Faso ce ta zo a matsayi na farko sai kuma kasar Pakistan na biye mata baya inda kasar Syria ta zo ta 3. Mali ce ta 4 sai kasar Nijar ta 5 sai Najeriya ta zo ta 6. Hakanan rahoton yace an samu yawan mutanen da aka kashe ta sanadiyyar ta'addanci a Najeriya wanda yawansu ya kai mutane 565 jimulla.
An sako daliban jami’an da aka yi gàrkùwà dasu a Makurdi

An sako daliban jami’an da aka yi gàrkùwà dasu a Makurdi

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, daliban jami'ar University of Agriculture Makurdi ta jihar Benue da aka yi garkuwa dasu an sakosu. Garkuwa da daliban ya jefa makarantar cikin yanayin damuwa wanda sai da yasa aka kulle makarantar har na tsawon mako guda. https://www.youtube.com/watch?v=I2vvoBY9v7E?si=3IqJB8_RA4UOnFlq Sako daliban yasa an barke da murna a makarantar. kalli Bidiyon lamarin a nan
Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

Duk Labarai
Gwamnatin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ƙaddamar ta tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman a faɗin jihar. Cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta ftitar, ta ce tallafin - wanda ya ƙunshi rabon kuɗi - zai shafi masu buƙata ta musamman duka ƙananan hukumomin jihar. Yayin da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce tallafin zai shafi cibiyoyi 27 na masu buƙata ta musamman a fadin jihar. Gwamnan kuma yi kira ga waɗanda za su amfana da tallafin su bayar da haɗin kai domin kauce wa turmutsitsi a wajen raba tallafin
Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin Natasha

Kwamitin Majalisar Dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin Natasha

Duk Labarai
Kwamitin ɗa'a da ladabtarwa da sauraron ƙorafin jama'a na majalisar dattawan Najeriya ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar kan zargin shugaban majalisar, Godswill Akpabio da neman yin lalata da ita. Kwamitin ya bayyana ƙorafin da cewa ''ya zo gaban kwamitin a mace'', saboda rashin bin ƙa'ida wajen shigar da shi. A yayin zaman sauraron ƙorafin, shugaban kwamitin Sanata Neda Imasuen, ya karanto doka ta 40 cikin dokokin majalisar dattijai, inda ya bayyana cewa Sanata Natasha ta sanya hannu kan ƙorafin da kanta maimakon ta bai wa wani ya shigar da shi a madadinta, lamarin da ya lalace. Ya kuma ƙara da cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin na gaban kotu a yanzu haka, wanda ya sa ba za a iya tattauna su ba kuma majalisar ba ta da hurumin sauraron su. Tuni d...
Mai Ɗaukar Hoton Da Ya Lashe Kambun Bajinta Na (Guinness World Record) Sa’idu Abdulrahman Ya Gana Da Captin Ahmed Musa

Mai Ɗaukar Hoton Da Ya Lashe Kambun Bajinta Na (Guinness World Record) Sa’idu Abdulrahman Ya Gana Da Captin Ahmed Musa

Duk Labarai
Matashin mai sana’ar ɗaukan hoto ɗan asalin Jihar Yobe, wanda ya samu nasarar lashe kambun bajinta na Duniya kan sana’arsa, (Guinness World Record In Photography), Sa’idu Abdulrahman, ya gana da fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Najeriya, Captin Ahmed Musa MON. Ganawar wadda ta gudana a jiya, matashin ya gabatar wa Captin ɗin kundin nasa na bajinta da ya samu bayan da ya yi nasarar ɗaukan hotuna 897 cikin mintuna 60. Sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da rawar da za su taka wajen tallafa wa masu tasowa cikin ayyukan fasaha a Najeriya ta yadda su ma za su samu damar bayyanawa Duniya irin tasu ƙwarewar. Matashin ya yaba da yadda ya samu Ahmed Musa a matsayin mutum mai nasara a Duniyar ƙwallon ƙafa wanda kuma a kullum yake ƙoƙarin tallafawa masu tasowa da...
Ba zamu saurareki ba, Majalisar Dattijai ta yi watsi da korafin Sanata Natasha Akpoti akan Sanata Godswill Akpabio  na zargin ya nemeta da lalata

Ba zamu saurareki ba, Majalisar Dattijai ta yi watsi da korafin Sanata Natasha Akpoti akan Sanata Godswill Akpabio na zargin ya nemeta da lalata

Duk Labarai
Kwamitin da'a na majalisar Dattijai yayi watsi da korafin da Sanata Natasha Akpoti ta shigar gabansa inda take zargin cewa, kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya nemeta da lalata. Sanata Natasha Akpoti a zaman majalisar a jiya, Laraba ta gabatar da korafi a hukumance gaban majalisar inda kakakin majalisar Godswill Akpabio wanda shine take zargi da neman yin lalata da ita yace mata ta mika takardar korafin inda a karshe yace a kai takardar gaban kwamitin da'a na majalisar. Saidai a zaman Kwamitin da'a na majalisar, shugaban Kwamitin, Sanata Neda Imasuen ya bayyana cewa ba zasu saurari korafin na Sanata Natasha Akpoti ba saboda maganar na kotu. Yace a dokar majalisa, duk maganar dake kotu, kwamtinsu ba zai tattaunata ba. Saidai kamin a tashi daga zaman majalisar, Sanata ...
Kalli Bidiyon yanda Sanata Natasha Akpoti ta kunyata kakakin majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio a yayin zaman majalisar a yau, Laraba

Kalli Bidiyon yanda Sanata Natasha Akpoti ta kunyata kakakin majalisar dattijai Sanata Godswill Akpabio a yayin zaman majalisar a yau, Laraba

Duk Labarai
A yau a hukumance, Sanata Natasha Akpoti ta kunyata kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio inda ana zaune a majalisar ta tashi tsaye ta gabatar da korafinta na cewa ya nemi yin lalata da ita. Tace tana gabatar da korafin take mata hakkinta da neman yin lalata da ita da kakakin majalisar yayi. Tace idan za'a iya tunawa a Gidan talabijin na Arise TV ta yi wannan zargi. Tace to yau gashi ta kawo a hukumance tana zargin kakakin majalisar. Bayan ta gama jawabinta, ta nemi kakakin majalisar ya bata umarnin gabatar masa da takardar zargin, inda yace ya bata umarni. Haka ta taka tinkis-tinkis ta je gaban sandar majalisar ta rusuna sannan ta ajiye takardar korafin a gaban kakakin majalisar. Ya bayar da umarnin a mikawa kwamitin ladaftarwa na majalisar da takardar korafin...
Ƴansanda sun kama wata mata bisa zargin kàshè kishiyarta a Bauchi, bayan ta kkàsheta, ta kuma watsa mata ruwan zafi sannan ta tattara buhu ta cinnawa gawar wuta

Ƴansanda sun kama wata mata bisa zargin kàshè kishiyarta a Bauchi, bayan ta kkàsheta, ta kuma watsa mata ruwan zafi sannan ta tattara buhu ta cinnawa gawar wuta

Duk Labarai
Rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Bauchi ta ce ta kama wata mata mai suna Fatima Mohammed kan zargin kashe kishiyar mai suna Hajara Isa hanyar shaƙeta a gidan mijinsu. Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, Ahmed Wakil ya fitar ranar Talata ya ce tuni rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan lamarin. Ya ce mijin matan - Sale Isa - ne ya kai ƙorafi wajen ƴansanda a ranar Talata. Wakil ya ce bayan fara gudanar da bincike ƴansanda suka kama matar mai suna Fatima Mohammed mai shekara 28, wadda daga baya ta amsa laifinta a lokacin ƴansanda suke tuhumarta. “A lokacin da ake tuhumarta ta amsa laifinta inda tace shaƙe kishiyartata ta yi, har sai da ta mutu'', in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa ''bayan ta kashe ta, ta yi ƙoƙarin yin ɓadda-bami, ta yadda ba ...
Karya Sanata Natasha take min mamana ta min tarbiyya me kyau, bana cin zarafin mata>>Sanata Godswill Akpabio

Karya Sanata Natasha take min mamana ta min tarbiyya me kyau, bana cin zarafin mata>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Sanata Godswill Akpabio kakakin majalisar dattijai ya bayyana cewa, Karya sanata Natasha Akpoti ke masa da tace ya nemi yin lalata da ita. Ya bayyana hakane a zaman majalisar na ranar laraba. Inda yace shi bai taba cin zarafin kowace mace ba a rayuwarsa ya kara da cewa shi har kyautar girmamawa aka bashi saboda kare hakkin mata. Sanata Natasha Akpoti dai ta zargi kakakin majalisar dattijan da neman yin lalata da ita shiyasa baya bata damar gabatar da ayyukan ci gaba a majalisar.