Ɓangaren Kwankwaso ba shi da hurumin korar mu daga NNPP saboda su ba halastattun shuwagabannin Jam’iyya bane- Kawu Sumaila
Ƴan majalisar dokokin Najeriya da jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar sun yi watsi da matakin jam'iyyar, tare da bayyana ta a matsayin wadda "ba ta halasta ba".
A yau Litinin ne shugaban jam'iyyar NNPP a jihar ta Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya sanar da dakatar da ƴan majalisar huɗu daga jam'iyyar bisa zargin su da ayyukan "zagon ƙasa".
A a tattaunawarsa da BBC, Sanata Kawu Sumaila ya ce "ita kanta wannan jam'iyyar da waɗanda suka yi sanarwar, kotu tana cajin su da cewa su ba halastattun shugabannin jam'iyya ba ne, don haka ba su da iko ko damar ɗaukar wannan mataki."
A game da batun gayyatar da shugaban jam'iyyar ta NNPP ya bayyana a lokacin sanar da dakatar da ƴan majalisar, Sumaila ya ce "gayyata ce kawai ta zumunci... shi ke nan yanzu jam'iyya sai ta hana ka gayyaci...






