NDLEA ta kama wata mata da ta ɓoye ƙwayoyi a cikin al’aurar ta
NDLEA ta kama wata mata da ta ɓoye ƙwayoyi a cikin al'aurar ta.
An kama wata mata mai suna Ihensekhien Miracle Obehi da ta rufe kanta da hijabi don fitar da kwayoyi iri daban-daban zuwa kasar Iran ta hanyar boye su a cikin al'aurarta, cikinta da kuma jakarta.
Jami'an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) su ka damke ta a filin jirgin sama na Port Harcourt, Jihar Rivers.
Obehi, wadda ta sanya hijabi don guje wa binciken tsaro, an cafke ta a zauren tashi na filin jirgin a ranar Lahadi, 3 ga Mayu, 2025, yayinda take ƙoƙarin hawa jirgin Qatar Airline zuwa Iran ta hanyar Doha, bayan samun bayanan sirri.
Bayan an bincike ta, an gano tanada kwayoyi guda uku da ta saka a al'aurarta, da wasu manyan kunsoshin kwayoyi guda biyu da aka ɓoye a cikin jakarta, sanna...








