Wednesday, March 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Akwa-Ibom bisa zargin satar Naira Biliyan 700

EFCC ta kama tsohon Gwamnan Akwa-Ibom bisa zargin satar Naira Biliyan 700

Duk Labarai
Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Akwa-Ibom, Udom Emmanuel bisa zargin satar Naira Biliyan 700 a yayin mulkinsa. Tsohon Gwamnan ya shiga komar EFCC ne a yayin da yace ofishin hukumar dan amsa gayyatar da suka masa kan zargin Rashawa da cin hanci. Wata kungiyar dake yaki da Rashawa da cin hanci me suna (NACAT) ce ta shigar da korafi akan tsohon gwamnan. Kungiyar ta yi korafin cewa, tsohon gwamnan ya karbi Naira Tiriliyan 3 a zamanin da yayi mulki tsakanin shekarun 2015 da 2023 daga gwamnatin tarayya. Saidai ya tafi ya bar jiharsa da bashin Naira Biliyan 500 sannan akwai ayyukan da ake yi na jihar na Naira Biliyan 300 wanda bai biya ba sanan ana zargin yayi sama da fadi da naira Biliyan 700. Zuwa yanzu dai hukumar EFCC bata ce uffan kan w...
Farashin gangar man fetur a kasuwar Duniya ya fado kasa inda hakan kewa hanyar samun kudin Gwamnatin Najeriya barazana

Farashin gangar man fetur a kasuwar Duniya ya fado kasa inda hakan kewa hanyar samun kudin Gwamnatin Najeriya barazana

Duk Labarai
Farashin gangar man fetur na Bonny Light wanda Najeriya ke sayarwa a kasuwar Duniya ya fadi kasa zuwa Dala $73.53 akan kowace ganga. A baya, 15 ga watan Janairu ana sayar da gangar man akan dala $84.02 kowace ganga wanda hakan ya nuna an samu asarar dala $10.6 a farashin bayan fadduwarsa. Hakan zai iya zama barazana ga hanyar samun kudin gwamnatin Najeriya dan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025. An shirya kasafin kudinne akan kiyasin farashin kowace gangar man fetur din za'a sayar da ita akan dala $75 inda ake tsammanin rika samun gangar man miliyan 2.06 kullun. Ana tsammanin samun kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N36.35 wanda kuma kaso 56 na cikin kudin ana tsammanin su fito ne daga hadahadar man fetur. Hakan na nuna cewa farashin kasuwar man a yanzu yayi kasa d...
Ni da kwankwaso bama gaba, muna zama Inuwa daya mu tattaunawa batutuwa>>Malam Ibrahim Shekarau

Ni da kwankwaso bama gaba, muna zama Inuwa daya mu tattaunawa batutuwa>>Malam Ibrahim Shekarau

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shakarau ya bayyana cewa shi da tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso basa gaba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi ta kafafen sada zumunta. Malam Ibrahim Shekarau yace yawanci matsalolin da suka faru tsakaninsa da Kwankwaso ba laifin ko daya daga cikinsu. Yace misa a APC, NNPP ce ta kawo kaso 60 cikin 100 na wakilan Jam'iyyar daga Kano amma da aka tashi saboda Kwankwaso yana Gwamna sai aka bashi kaso mafi tsoka. Yace a PDP ma abinda ya faru kenan. https://www.tiktok.com/@usmansolo/video/7477899548837367045?_t=ZM-8uQDuHsBZji&_r=1 Ya kara da cewa, suna zama inuwa daya da Kwankwaso su tattauna batutuwa.
Hukumar ‘yansandan Abuja ta ce tsohon shugaban hukumar Immigration David Shikfu Parradangba garkuwa aka yi dashi ba, ya mutu ne a dakin Otal bayan sun shiga shi da wata mata

Hukumar ‘yansandan Abuja ta ce tsohon shugaban hukumar Immigration David Shikfu Parradangba garkuwa aka yi dashi ba, ya mutu ne a dakin Otal bayan sun shiga shi da wata mata

Duk Labarai
A dazu ne dai muka samu rahoto daga jaridar The National cewa tsohon shugaban hukumar shigi da fici, Immigration me suna David Shikfu Parradang an yi garkuwa dashi kuma an kasheshi. Saidai sabbin bayanai da hukumar 'yansandan Abuja suka fitar sun ce ba a yi garkuwa dashi ba. Bayanan sun ce David Shikfu Parradang ya je otal din Joy House Hotel dake Area 3 inda ya biya kudin daki na kwana daya dubu 22. Ya shiga otal dinne da misalin karfe 12 na yamma da bakar mota kirar Mercedes Benz. Jim kadan bayan shigarsa sai ya baiwa me karbar baki dake aiki a otal din umarnin ta shigo masa sa wata bakuwa da yayi. Da misalin karfe 4 na yamma bakuwar ta fita ta tafi abinta. Da Misalin karfe 4 na dare sai ga abokinsa soja yana nemansa, ko da suka shiga dakin sai suka tarar dashi a zaune ka...
Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba>>Inji Dan Jarida Sam Omatseye

Buhari bai so Tinubu ya zama shugaban kasa ba>>Inji Dan Jarida Sam Omatseye

Duk Labarai
Dan Jarida, Sam Omatseye ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai so Tinubu ya zama ahugaban kasa ba. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. Yace tun a shekarar farko aka so a samu matsala tsakanin Buhari da Tinubu amma saboda Buharin na tunanin zarcewa, shiyasa ba'a yi fadan ba. Yace cire tsohon gwamnan Edo, Adams Oshiomhole daga mukamin shugaban APC na daya daga cikin dabarun hana Bola Ahmad Tinubu zama shugaban kasa da Gwamnatin Buhari ta bijiro dasu. Yace hakanan akwai wasu gwamnoni ma da basu so Tinubu ya zama shugaban kasa ba.
Da Duminsa: Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na shirin soke dokar data halasta auren jinsi na ‘yan Luwadi da Magido a kasar Amurka

Da Duminsa: Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump na shirin soke dokar data halasta auren jinsi na ‘yan Luwadi da Magido a kasar Amurka

Duk Labarai
'Yan Jam'iyyar Republican dake mulki a kasar Amurka a majalisar kasar na shirin soke dokar amincewa da auren jinsi na 'yan Luwadi da madigo a kasar. A watan Janairu ne aka fara samun wanna kira daga 'yan majalisar jihar Idaho inda suka nemi kotun kolin kasar data sake duba dokar da ta yi a shekarar 2015 data halasta auren jinsi. Bayan su, an sake samun wasu 'yan majalisar daga jihohin Michigan, Montana, North Dakota da South Dakota suma suna kiran kotun kolin data sake duba wannan hukunci nata. Dama dai tun a ranar da aka bayyana cewa, Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasar Amurka aka rika samun 'yan Luwadi da madigo da yawa na kuka suna cewa sun shiga uku inda wasu suka bar kasar ta Amurka saboda sun san shugaban kasar, Donald Trump baya shiri dasu. Tuni dai shugaba Tru...