Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya isa jihar Anambra inda yake ziyarar aiki a yau, Alhamis.
Shugaban iya isa filin sauka da tashin jiragen sama na Chinua Achebe dake jihar inda ya samu tarbar gwamnan jihar, Charles Soludo da 'yan majalisar jihar da sauran dattawan jihar.
Shugaba Tinubu kuma ya samu ya tsaya an masa taken Najeriya inda sojoji suka yi harbi sama dan girmamashi.
Bayannan kuma, Shugaba Tinubu ya shiga motar da aka tanada dan shi tare da Gwamnan jihar inda zai zarce dan fara kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta gudanar.
Yanzu-Yanzu: Duka ƴan majalisun adawa na tarayyar daga jihar Katsina sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Waɗanda suka sauya shekar sun haɗa da Honorable Salisu Yusuf Majigiri na mazaɓar Mashi/Dutsi, Honorable Aliyu Iliyasu na mazaɓar Batsari/Safana/Danmusa, Honorable Abdullahi Balarabe Dabai na mazaɓar Bakori/Danja.
Dukkan su sun bayyana rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar PDP a matsayin dalilin sauya shekar ta su.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya maka Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a kotu, yana zargin ta da wallafa kalaman ɓatanci a cikin wata wasikar bada haƙuri da aka danganta da ita — Wasikar da ke ɗauke da wata magana mai cin mutunci da ke cewa “ta yi kuskuren tunanin cewa kujerarta a Majalisa ta samu ta hanyar zaɓe, ba ta hanyar jima’i ba.”
Rahotanni sun bayyana cewa wannan ƙara ta samo asali ne daga wata wallafa da ke yawo a kafafen sada zumunta, wadda aka danganta da Sanata Natasha, inda ta nemi gafara daga Shugaban Majalisar bisa wasu maganganu da ake cewa ta furta a baya. A cikin wannan wasikar, an ambaci cewa ta “yi kuskuren ɗauka cewa ta samu kujera ne ta hanyar sahihin zaɓe.”
Lauyoyin Akpabio sun ce wannan magana ta wallafa ra’ayi mai matuƙar cin mutunci da b...
Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa kasar ta harbo jiragen yakin makwabciyarta, India guda 25.
Hakan na zuwane yayin da lamura ke kara kazancewa tsakanin kasashen Biyu.
Kasar India ce dai ta fara harbawa Pakistan makami wanda ya kashe mutane farar hula.
Kasar ta Pakistan tuni ta mayar da martani.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.
Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba.
Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.
Ambasada Nuhu ya ce "hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al'umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma", in ji shi.
"...
Ministan tsaron Najeriya, Mohamamd Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba.
Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam'an tsaron ƙasar.
A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Najeriya suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar.
Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jihar Laraba ministan tsaron na Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya ce sakae dabarun yaƙi da mastaalr tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar.
"Idan ka yi taron ƙasa kan tsaro, mutane za su zo, su fadi abin da suke so, mu ...
Bayan tsawon lokaci ba a ji ta bakinsa ba dangane da faruwar al'amuran siyasa, tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ɓara inda ya yi gargaɗin cewa "abu ne mai haɗari ɗora Najeriya a kan turbar jam'iyya guda ɗaya".
Ba kasafai dai ake jin bakin Goodluck Jonathan ba a al'amura kasancewarsa mutum mai kawaici da rashin son yawan magana.
To sai dai a ranar Larabar nan, tsohon shugaban na Najeriya yayin wata lacca da aka shirya a Abuja domin tuna wa da marigayi Edwin Clerk, dattijo ɗan ƙabilar Ijaw wanda ya rasu yana da shekara 97, Jonathan ya ja hankalin gwamnati da jam'iyya mai mulki ta APC da ake zargi da mayar da ƙasar ƙarƙashin tsarin jam'iyya guda.
Kalaman Goodluck Jonathan
Tsohon shugaba Goodluck Jonathan ya ce duk wnai yunƙurin mayar da Najeriya kan tsarin jam'i...
Labari Mai Dadin Ji: Gawurtacen Dan Bindiga SAGIDI Ya Bakunci Lahira.
Sagili wani babban Ɗan Bindiga ne da ya shahara wajen yi ma al'umma kisan gilla.
Yana zaune a dajin Wuya dake Karamar Hukumar Anka,
Yana cikin yaran marigayi Kachalla Jijji Ɗan Auta wanda ya addabi Hananan Hukumomin Anka, Mafara, da Yammacin Kanoma.
Gwamnatin Kano Ta Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye a Kafafen Watsa Labarai
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana dakatarwa nan take ga dukkan shirye-shiryen siyasa da ake yadawa kai tsaye a kafafen watsa labarai na jihar.
An bayyana wannan mataki ne yayin taron tattaunawa na kowane lokaci da ake gudanarwa a Ma’aikatar Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, wanda Kwamishinan Yada Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranta tare da shugabannin kafafen yada labarai.
A cewar wata sanarwa da Daraktan Harkokin Musamman na ma’aikatar, Sani Abba Yola, ya sanyawa hannu, an dauki wannan mataki ne don dakile yada kalaman da za su iya haifar da fitina da barazana ga zaman lafiya da daidaiton al’adu da addini a jihar.
“Ba mu dauki wannan mataki don murkushe ‘yan adawa ba,” in ji ...