Saturday, July 11
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni”>>Inji Wannan tsohon Abokin nasa

Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni”>>Inji Wannan tsohon Abokin nasa

Duk Labarai
Ina Bin Rarara Bashin ₦2500 Kuma Sai ya Biya Ni" Wasu Zasuce Karya nakeyi ko Sharri nake masa, amma kuje Ku Tambayeshi Waye Haruna masta, Bazai Taba mantawa ba, domin Bayan yadawo daga makarantar Allo baida wani abokin da suke Tare kullum sai Ni, Kudin Da Zai fara zuwa Studio Ya Rera waka Ni na bashi Aro ₦2500, Tun bayan fara wakarsa Yabar unguwar mu, Duk irin neman da zan masa nayi Domin ya Sakamun irin taimakon da nayi masa, amma baya Daukan waya Tun A baya cen, Yanzu ma banida Number da ake samun sa" Duniya kenan Kayiwa Mutum Rana yayi maka Dare.
Ji yanda aka kai Amarya da Uwar gida Asibiti bayan da suka sha maganin kayan Mata da ya fi karfinsu dan su burge mijinsu

Ji yanda aka kai Amarya da Uwar gida Asibiti bayan da suka sha maganin kayan Mata da ya fi karfinsu dan su burge mijinsu

Duk Labarai
An kai Uwargida da Amarya Asibiti bayan da suka sha maganin kayan mata dan su burge mijin su. Lamarin ya farune a garin Dakwa dake yankin Bwari na babban birnin tarayya, Abuja. Sun sha wannan maganin ne bayan da mijinsu yayi sabuwar Amarya dan su ma ya ji su zanzan. Mijin ya je jiharsa ta Zamfara inda ya karo auren mata ta 3. Da yake gayawa manema labarai yanda lamarin ya faru, mijin me suna Musa Muhammad yace yana dayan gidansa sai aka kirashi aka ce matansa sun kwanta basu da lafiya. Yace da ya je sai ya gansu suna ta birgima a kasa cikinsu na ciwo, yace da farko ya kira wata Nurse ce dan ta dubasu, inda ta saka musu karin ruwa. Yace amma abin yaki ci yaki cinyewa, dole aka kaisu Asibitin madalla inda likitoci suka ce maganin matan da suka sha ne har ya fara lalata musu...
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo

Duk Labarai
Rundunar Ƴansanda ta rage wa wani ɗansanda matsayi bisa azabtar da wani dattijo a jihar Imo. Rundunar ƴansandan jihar Imo ta rage wa wani ɗansanda mai muƙamin Sajan, Anayo Ekezie mukamin sa saboda cin zarafin wani dattijo. Wani faifan bidiyo na yadda wasu ƴansanda ke cin zarafin wani mutum a kan hanyar Owerri zuwa Aba ya bazu a kwanakin baya. Kakakin rundunar ƴansanda ta jihar, Henry Okoye, a jiya Laraba, ya tabbatar da cewa an gano ‘yansandan tare da tsare su. Ya ce an samu ƴansandan uku da lamarin ya shafa, inda ya kara da cewa an rage wa Ekezie mukami zuwa Kofur, yayin da aka ja wa sauran biyun kunne.
Shugaban Hukumar Alhazai (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan tare da rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar, sun sauƙa a filin jirgin sama na Port Harcourt domin shirin tashin jirgin farko na Alhazan bana da za a yi gobe a Owerri, fadar gwamnatin jihar Imo

Shugaban Hukumar Alhazai (NAHCON) Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan tare da rakiyar wasu daga cikin manyan jami’an hukumar, sun sauƙa a filin jirgin sama na Port Harcourt domin shirin tashin jirgin farko na Alhazan bana da za a yi gobe a Owerri, fadar gwamnatin jihar Imo. NAHCON Information.
Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Nan da shekarar 2045 zan rabar da gaba dayan kudina, ban so in mutu a matsayin me kudi>>Inji Me Kudin Duniya, Bill Gates

Duk Labarai
Hamshakin me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa, nan da shekaru 20, watau 2045 zai Rabar da gaba dayan kudinsa. Bill Gates ya bayyana hakane a shafin Gidauniyarsa ta Bill and Melinda Gates wadda suka kafa a shekarar 2000. Daga baya Wallen Buffet ya shiga tafiyar. Ya bayyana hakane yayin bikin cikar gidauniyar shekaru 25 da kafuwa. Hakanan a shekaru 25, Bill Gates ya bayar da Tallafin da ya kai na dalar Amurka Biliyan 100 kyauta. Yace nan da shekaru 20 din zai nunka yawan kudin da yake bayarwa tallafi har sai kudin sa sun kare gaba daya, bai bayyana cewa zai barwa 'ya'yansa ko sisi ba. Bill Gates wanda shine me kamfanin Microsoft yace zaftare tallafin da kasashe masu kudi suka yi wanda a baya suke baiwa kasashe matalauta abin damuwa ne. Yace baya so idan ya mutu a ri...