Thursday, January 15
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Bidiyon: Kalar Gaisawar da shugaba Traore yayi da Wakilan Najeriya da suka je bashi hakuri ta dauki hankula

Kalli Bidiyon: Kalar Gaisawar da shugaba Traore yayi da Wakilan Najeriya da suka je bashi hakuri ta dauki hankula

Duk Labarai
A jiyane wakilan Gwamnatin Najeriyar suka je kasar Burkina Faso dan baiwa shugaba Ibrahim Traore Hakuri kan jirgin Najeriya da ya shiga kasar da sojoji 11 ba tare da izini ba. Kalar Gaisuwar da suka yi da shugaba Traore ta dauki hankula sosai. Saidai wasu 'yan Najeriya sun rika mamakin wai hakuri kawai kasar ta Burkina Faso ke son Najeriya ta bata kamin a saki sojojin. A jiyan dai an saki sojojin na Najeriya bayan ziyarar wakilan Najeriyar. Wani abu da ya kara daukar hankalin mutane shine yanda wakilan suka shaidawa Gwamnatin kasar Burkina Faso cewa kalamai marasa dadi da wasu 'yan Najeriya suka rika fadi akan kasar Burkina Faso ba da yawun Gwamnati bane. https://www.tiktok.com/@livenewsafricamedia/video/7584915107885452558?_t=ZS-92JiX2eTWfB&_r=1 https://twitter.c...
Kalli Bidiyon Gwanin Ban tausai: Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta fashe da kuka yayin da take bayar da labarin irin wahalar data sha a gidan tsohon mijinta kamin su rabu

Kalli Bidiyon Gwanin Ban tausai: Tauraruwar fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta fashe da kuka yayin da take bayar da labarin irin wahalar data sha a gidan tsohon mijinta kamin su rabu

Duk Labarai
Tauraruwar Fina-finan Hausa, Samha M. Inuwa ta bayar da labarin irin wahalar data sha a gidan mijinta kamin su rabu. Samha ta bayyana hakane a wani Tiktok live da aka yi da ita. Tace fada suka yi da Budurwar mijinta kuma mijin nata ya goyi bayan Budurwarsa ya juya mata baya a matsayin matarsa. https://www.tiktok.com/@a_e_s28/video/7584430583263104276?_t=ZS-92JCSPDgPwn&_r=1 https://www.tiktok.com/@a_e_s28/video/7584883908110535957?_t=ZS-92JCvo7fOZE&_r=1
Buhari har yayi Mulkinsa ya gama bai kama kowa ba, kuma baisa a kama kowa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Buhari har yayi Mulkinsa ya gama bai kama kowa ba, kuma baisa a kama kowa ba>>Inji Tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad

Duk Labarai
Tsohon Hadimin Shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai kama kowa ba kuma bai sa a kama kowa ba har yayi mulkinsa ya gama. Ya bayyana hakane a martanin da yakewa Dawisu, Watau Salihu Tanko Yakasai da yace Buhari ya kamashi. Bashir yace idan dai Dawisu zai ce an kamashi a zamanin Mulkin Buhari zai yadda amma maganar cewa Buhari yasa an kamashi ba gaskiya bane. https://twitter.com/BashirAhmaad/status/2001370109445562762?t=pvR-855gABYzJoFn1hwUeA&s=19
Kalli Hotunan yanda ganawar Wakilan Najeriya da shugaban kasar Burkina Faso ta kasance

Kalli Hotunan yanda ganawar Wakilan Najeriya da shugaban kasar Burkina Faso ta kasance

Duk Labarai
Wadannan wakilan Gwamnatin Najeriya ne karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje Yusuf Tuggar inda suka gana da shugaban kasar Burkina Faso, Ibrahim Traore. Sun mikawa Shugaba Traore da sakon shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na nuna goyon bayan gwamnatinsa. Sannan sun bayar da hakuri game da shiga kasar Burkina Faso da jirgin Najeriyar yayi. Sun bayyana muhimmancin ci gaba da dangantaka tsakanin Najeriya da kasar Burkina Faso.
Da Duminsa: EFCC sun kulle gidan da matar Malami, Diyar Tsohon shugaban kasa take ciki

Da Duminsa: EFCC sun kulle gidan da matar Malami, Diyar Tsohon shugaban kasa take ciki

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun kulle gidan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami inda matarsa, diyar tsohon shugaban kasa, Fatima Buhari take. Jam'iyyar ADC ce ta bayyana hakan inda ta zargi Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da wulakanta Buhari ta wannan hanya. Ana zargin Malami da Almundahanar kudade da yawa ciki hadda kudaden Abacha da aka kwato daga kasashen waje.
Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa bayan da Dangote ya zargeshi da kashe dala Miliyan $7 wajan kai ‘ya’yansa kasar Switzerland karatu

Da Duminsa: Shugaban Hukumar NMDPRA, Engr. Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa bayan da Dangote ya zargeshi da kashe dala Miliyan $7 wajan kai ‘ya’yansa kasar Switzerland karatu

Duk Labarai
YANZU-YANZU: Farouk Ahmed yayi murabus daga mukaminsa na shugaban hukumar mai ta NMDPRA Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen sababbin shugabannin NUPRC da NMDPRA domin amincewa, bayan murabus ɗin Engr. Farouk Ahmed da Gbenga Komolafe. Sabbin waɗanda aka naɗa su ne Oritsemeyiwa Eyesan da Engr. Saidu Aliyu Mohammed. Farouk dai shine ke rikici da Aliko Dangote Me zaku ce?
Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Da Duminsa: Najeriya ta aika da wakilai na musamman kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za’a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu

Duk Labarai
Najeriya ta aika da wakilai na musamman zuwa kasar Burkina Faso dan a tattauna yanda za'a sako sojojin Najeriya 11 da jirginsu C-130. Wadanda aka aika din daga ma'aikatar harkokin kasashen waje ne da kuma ma'aikatar tsaro ta kasa. Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya jagoranci tawagar. Zasu tattauna maganar sasanci tsakanin kasashen biyu da kuma inganta tsaro.