Tuesday, November 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Khadija Muhammad na ƙoƙarin tona asirin wani a Kannywood — amma ta ƙi bayyana sunansa!

Duk Labarai
Jarumar Kannywood Khadija Muhammad ta bayyana cewa tana ƙoƙarin tona asirin wani mutum a Kannywood da take zargin ya ƙi biyan ta hakkinta.Abin da ya ƙara ɗaukar hankalin mutane shi ne yadda ta yi wasu bayanai da suka sa mutane ke ƙoƙarin gano wanda take magana a kansa. Wasu ma sun ƙagu ta saka hotonsa ko ta ambaci sunansa, amma har yanzu Khadija ba ta bayyana sunan mutumin ba. Sai dai a cikin bayaninta, ta yi masa wata siffa mai ban dariya, inda ta ce “shi ya sa yake da ƙaton tumbi, ashe duk haƙƙinmu a ciki yake.” Ku a ganinku, ya kamata Khadija ta bayyana sunan mutumin da take zargi, ko ta nemi hakkinta ta hanyar da ta dace ba tare da tona sunansa a kafafen sada zumunta ba?

Kalli Bidiyon yanda shugaba Tinubu ke zuwa Ofis a kafa

Duk Labarai
A jiyane dai labarai suka karade kafafen sada zumunta cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a kasa yake zuwa ofis daga gidansa a Villa. Shugaban hukumar tattara Haraji ta kasa, NRS, Adedeji ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi dashi. A yau kuma sai aka tashi magoya bayan shugaban kasar suna yada Bidiyon da ikirarin cewa shine yake takawa da kafa zuwa ofishinsa. https://twitter.com/i/status/2086824986879119551

Kalli Bidiyon: Wanda suke rike da matata sub kirani, na kaiwa ‘yansanda Rahoton amma sun ce min wai kawai in je in biya kudin da aka nema dan a sako min iyalina>>Inji Ishaq Major

Duk Labarai
Tauraron dan Gwagwarmaya, Ishaq Major ya bayyana cewa, wadanda suke rike da matarsa da dansa sun kirashi. Yace ya je wajan 'yansanda dan kai musu korafi. Amma sai suka ce wai ya je ya biya kudin da aka nema dan a sako masa iyalinsa. https://www.tiktok.com/@ishaq..major/video/7672436110856932628?_r=1&_t=ZS-98mHvg7O2OC

Dalibin Jami’ar Federal University Dutse Jihar Jigawa ya dauki hankula

Duk Labarai
Wani dalibin Jami'ar Federal University Dutse jihar Jigawa ya dauki hankula bayan da aka ganshi a manyan motoci irin na 'yan siyasa. Hakanan an ganshi tare jami'an tsaron 'yansanda dana sojoji suna take masa baya. Ana kiran cewa idan jami'an tsaron gaskene ya kamata a hukuntasu. Idan kuma na Bogene ya kamata a hukuntasu da yin sojan Gona. https://twitter.com/i/status/2086779942470037717