Friday, February 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bìndìgù Sama da Dubu uku sun bace a hannun ‘yansandan Najeriya

Bìndìgù Sama da Dubu uku sun bace a hannun ‘yansandan Najeriya

Duk Labarai
Majalisar tarayya ta tuhumi shugaban 'yansandan Najeriya, (IGP),  Kayode Egbetokun bisa bacewar Bindigu 3,907 a hannun 'yansandan. Hakanan an masa tambayoyi game da aikata ba daidai ba da kudi a shekarar 2019. Shugaban 'yansandan da farko ya baiwa majalisar hakuri kan rashin amsa gayyatar da suka masa. Sannan ya wakilta mataimakinsa, AIG Suleiman Abdul ya wa 'yan majalisar jawabi kan tambayoyin batan kudaden da suke masa. Saida ya kasa bayar da gamsashshiyar amsa game da bacewar Bindigun inda suka nemi a shiga tattaunawar sirri a kori 'yan jarida daga dakin taron. Saidai 'yan majalisar sun ki amincewa da wannan kira inda suka ce shugaban 'yansandan ya kkma ya nemo amsar tambayoyin da suka masa.
Kalli Hotuna: Ana zargin Gwamnan Najeriya da dirkawa wata ‘yar Fim ciki

Kalli Hotuna: Ana zargin Gwamnan Najeriya da dirkawa wata ‘yar Fim ciki

Duk Labarai
Juna-biyun da na ke ɗauke da shi ba shi da alaƙa da wani gwamna - Jaruma Nengi Nengi Hampson, tsohuwar jaruma a shirin fim na gasar Big Brother Naija (BBNaija), ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sadarwa cewa tana dauke da juna biyu da wani gwamna a Najeriya ya yi mata. Jaridar TheCable ta rawaito cewa rahotannin farko sun yi ikirarin cewa jarumar mai shekara 27 ta haifi jariri ga wani gwamna mai shekara 65 kuma har ta zama matarsa ta biyar. A wani rubutu da ta wallafa kwanan nan a shafin X, Nengi ta bayyana takaicinta game da wannan jita-jita, tana mai cewa da ta sani ma da ta kau da kai daga jita-jitar. Sai dai ta ce dole ta yi magana saboda abin ya shafi mutanen da ta ke girmamawa sosai. Jarumar ta jaddada cewa ba za ta bari wannan jita-jita ta bata rayuwarta ko t...
Matsin Tattalin Arziki yayi yawa, ‘Yan Najeriya ba zasu iya biya ba>>Majalisar Tarayya tacewa Ministan sadarwa maza a dakatar da karin kudin kiran waya da ake shirin yi

Matsin Tattalin Arziki yayi yawa, ‘Yan Najeriya ba zasu iya biya ba>>Majalisar Tarayya tacewa Ministan sadarwa maza a dakatar da karin kudin kiran waya da ake shirin yi

Duk Labarai
Biyo bayan karin kudin kiran waya dana data da kamfanonin sadarwa suka yi, majalisar tarayya ta yunkuro dan dakatar da karin. Hukumar sadarwa ta kasa, NCC tuni ta amincewa kamfanonin sadarwar su kara kaso 50 cikin 100 na kudin da suke caji. Saidai kungiyoyin fafutuka da suka hada dana Kwadago, NLC da TUC sun ce basu amince da wannan kari ba. 'Yan majalisar ta wakilai a ranar Talata sun baiwa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani umarnin ya dakatar da kari kudin kiran wayar inda suka ce 'yan Najeriya ba zasu iya biya ba musamman a wannan yanayi na matsin tattalin arziki. Sai ranar Litinin me zuwa ne ya kamata a fara yin karin kudin kiran dana data, amma MTN a matsayin kamfanin sadarwa mafi girma a Najeriya Tun a wannan satin sun fara kara kudin kira. A wata hira da ja...
Mafi yawancin Gwamnoni na barin jihohinsu ne su je Abuja su tare>>Inji NLC

Mafi yawancin Gwamnoni na barin jihohinsu ne su je Abuja su tare>>Inji NLC

Duk Labarai
Shugaban kungiyar Kwadago ta NLC, Joe Ajero ya koka da cewa, mafi yawanci gwamnonin Najeriya kan bar jihohinsu su je Abuja su tare. Yace hakan na faruwane a yayin mutanen jihohin wadannan gwamnonin ke fama da wahalar rayuwa. Ya bayyana hakane a wajan taron karawa juna sani da ya faru a Lokaja jihar Kogi. Ajaero ya bayyana cewa, sun ziyarci yankuna 5 na Najeriya amma mafi yawanci duk sun iske gwamnonin basa nan sun tafi Abuja. An yi taron na NLC ne a Lokoja dan ma'aikatan jihar su bayyana matsalolinsu dan a kaiwa Gwamnan jihar.
Shugaban ‘yansandan Najeriya ya hana ‘yansandan rike Bìndìgà idan suna sanye da kayan gida

Shugaban ‘yansandan Najeriya ya hana ‘yansandan rike Bìndìgà idan suna sanye da kayan gida

Duk Labarai
Shugaban 'yansandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin cewa, daga yanzu kar dansandan daya sake rike Bindiga indai yana sanye da kayan gida. Ya kuma gargadi 'yansandan su kiyaye kada su rika take hakkin dan Adam dan kuwa aikinsu shine kare hakkokin al'umma. Ya bayyana hakane a yayin wani taro da aka yi a jiya inda yace ya samu korafe-korafe da yawa game da take hakkokin al'umma da wasu 'yansandan ke yi. Sannan Shugaban 'yansandan yace duk wanda aka kama da karya wadannan dokoki zai dandana kudarsa. Ya bukaci 'yansandan su gudanar da aikinsu bisa doka dan kare mutuncin hukumar ta 'yansanda.
Kalli Sojar Najeriya data kirkiro Jirgin saman yaki na farko

Kalli Sojar Najeriya data kirkiro Jirgin saman yaki na farko

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun samu nasara babba inda suka hada jirgin yaki na farko kuma wadda ta kerashi sojar sama ce me suna Lieutenant Nkemdilim Anulika Ofodile. Sojar dai ta yi karatu kimiyyar sararin samaniyane kuma an sajawa jirgin saman yakin data kirkiro sunan Tsaigumi Tactical UAV. Wannan nasara ba karamin abin ci gaba bane a hukumar sojojin Najariya dama Najeriya baki daya.
Ina shan Tabar wìwì ta Naira Miliyan 2 kullun>>Inji Mawakin Najeriya, Odumodublvck

Ina shan Tabar wìwì ta Naira Miliyan 2 kullun>>Inji Mawakin Najeriya, Odumodublvck

Duk Labarai
Shahararren mawakin Gambara dan Najeriya me suna Tochukwu Gbubemi Ojogwu wanda aka fi sani da Odumodublvck ya bayyana cewa, a kullun yana shan tabar wiwi ta Naira Miliyan 2 wanda hakan na nufin a sati yana shan ta naira Naira miki 14 kenan. Ya bayyana hakane a yayin da shahararren me wasan barkwanci, Carter Efe ke hira dashi. Wannan bayani nashi ya baiwa mutane mamaki matuka. Mawakin dai ya kara da cewa, matsin rayuwar da ake fama da uta a Najeriya ko a jikinsa.