Thursday, February 19
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Najeriya ta lalace, sai an sha wuya kamin ta dawo daidai>>Kashim Shettima

Najeriya ta lalace, sai an sha wuya kamin ta dawo daidai>>Kashim Shettima

Duk Labarai
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana cewa, Najeriya ta samu matsalar rashin kula a baya dan haka gyaranta sai an sha wuya. Ya bayyana hakane ta bakin wakilinsa, Hakim Baba Ahmad a yayin da ya wakilceshi zuwa taron karfafa Dimokradiyya a Abuja jiya. Ya kara da cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yana sane da irin halin matsin rayuwa da al'ummar Najeriya ke ciki kuma zai dauki matakin gyara a inda ya kamata. Ya kara da cewa, Gwamnatinsu da Bola Ahmad Tinubu ke jagoranta zata ci gaba da yaki da rashawa da cin hanci da tada komadar tattalin arziki da ci gaba da goyon bayan zaben gaskiya.
Hukumar Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata

Hukumar Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma’aikata

Duk Labarai
Hukumar Gwamnatin tarayya ta Federal Civil Service Commission ta sanar da daukar sabbin ma'aikata wanda za'a cike guraben ayyuka da yawa. Me magana da yawun hukumar Taiwo Hassan ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin. Hukumar ta bukaci 'yan Najeriya dasu cike bayanansu dan samun gurbin aiki da ake nema. Shafin da za'a bi dan cike bayanai shine: https://recruitment.fedcivilservice.gov.ng Shafin zai kasance a bude har nan da zuwa ranar 10 ga watan Maris. Hakanan hukumar tace masu bukata ta musamman da masu nakasa ma na iya neman wannan aiki.
Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Na samu karin Lafiya sosai bayan dana sauka daga Mulkin Najeriya>>Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari

Duk Labarai
Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, ya samu karin lafiya sosai bayan da ya sauka daga kan mulkin Najeriya. Shugaban ya bayyana hakane a wajan taron Jam'iyyar APC a jihar Katsina. Yace duk da kokarin da yayi na gyaran kasarnan amma ya fuskanci suka daga mutane da yawa. Yace wadanda basa kusa da Gwamnati basu san yanda ake gudanar da mulki da matsalar mulkin ba. Yace bayan da ya sauka, mutane dake kai masa ziyara sun bayyana cewa, a yanzu yafi lafiya fiye da sanda yake kan mulki. Buhari ya baiwa shuwagabanni shawarar su ji tsoron Allah.
Ni kiristane amma har yanzu ina taba addinin gargajiya da tsafe-tsafe>>Inji tsohon shugaban kasa Obasanjo

Ni kiristane amma har yanzu ina taba addinin gargajiya da tsafe-tsafe>>Inji tsohon shugaban kasa Obasanjo

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, shi kiristane amma har yanzu yana taba addinin gargaji na bautar wani gunki da ake cewa Ifa. Obasanjo yace kamin zuwan addinin kiristanci da Musulunci suna da Ifa kuma duk wnda ya zagi Ifa zai ce shi wawane. Ya bayyana cewa, shi bai wasa da al'ada saboda abincinmu, tufafi da yaren Yarbawa duk suna da muhimmanci a wajansa.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da ‘yan Bìndìgà

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana dalilin da yasa yayi sulhu da 'yan Bindiga a jiharsa. Gwamnan ya bayyana hakanne a hirar da BBChausa ta yi dashi. Ya bayyana cewa, yayi sulhu da 'yan Bindigar ne saboda ko da mutum daya aka kashe sai Allah ya tambayeshi. Ya kara da cewa, Basu baiwa 'yan Bindigar ko sisi ba sannan kuma sun saki wadanda suka yi garkuwa dasu. Yace harkar kasuwanci da noma na ci gaba da habaka tun bayan lamarin.
Gwamnati na da arzikin da za ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen Tinubu ko mai yawan su – Minista

Gwamnati na da arzikin da za ta ɗauki nauyin tafiye-tafiyen Tinubu ko mai yawan su – Minista

Duk Labarai
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na da arzikin da za ta iya daukar nauyin tafiye-tafiyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yawan yi zuwa kasashen waje tun bayan hawansa mulki. Tafiye-tafiyen da Tinubu ke yi zuwa kasashen waje na shan suka daga al'ummar ƙasar duba da matsalar tattalin arziki da ake fama da ita. Sai dai da ya ke magana a shirin 'Politics Today' na Channels TV, Tuggar ya ce Tinubu, sabanin korafe-korafen da ake yi, har ma yana bukatar kara tafiye-tafiyen saboda mahimmancin dabarunsa da kuma amfanin da su ke da shi ga kasar. Ministan ya bayyana cewa, Tinubu zai iya karfafa alaka da sauran shugabannin kasashen duniya ne kawai a yunkurinsa na dora kasar nan kan turba mai kyau ta hanyar yin tattaki zuwa ƙasashen.. Ya ce, “Wannan korafe-korafen ba su ...
‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hari Abuja

‘Yan Bìndìgà sun sake kai mummunan hari Abuja

Duk Labarai
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, 'yan Bindiga sun sake kai hari Abujar. 'Yan Bindigar wanda ake zargin masu garkuwa da mutanene sun kai harinne a Cikakore dake Kubwa a gundumar Bwari. Kuma sun sace wani mutum da matarsa da dansa da wasu karin mutane 2. Wasu shaidu da suka shaida lamarin sun bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun kai su 30 rike da bindigar AK47 inda suka shiga gidan Adefija Micheal Akinropo suka saceshi da matarshi da dansa da dan uwansa. Shaidan ya kara da cewa, 'yansanda daga ofishin 'yansandan Byazin police station sun halarci wajan inda yace wanda suka yi garkuwa da mutanen basu tuntubi kowa ba zuwa 'yanzu. Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa ta tuntubi kakakin 'yansandan Abuja, Josephine Adeh kan lamarin inda tace tana kan hanya am...
SANATA BARAU JIBRIL NE YAKE ASSASA DUK WATA FITINA A JIHAR KANO

SANATA BARAU JIBRIL NE YAKE ASSASA DUK WATA FITINA A JIHAR KANO

Duk Labarai
Shahararren ɗan jaridar nan, Jaafar Jaafar ya zargi mataimakin shugaban majalissar dattijai Sanata Barau Jibrin da hannu cikin fitintinu masu nasaba da siyasa da ke faruwa a Jihar Kano. Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito Jaafar Jaafar na zarge-zargen ne ta cikin shirin "Fashin Baƙi" da suka saba gabatarwa mako-mako. A cewar Jaafar "Mutane da yawa suna tunanin Ganduje ne, Wallahi Barau ya fi hannu a wannan masifar. Suna shirya gidoga ne su faɗa wa shugaban ƙasa cewa mutane sun dawo daga rakiyar gwamnati mai ci a Jihar Kano ba sa son ta idan ta yi taro aka gani da jama’a da yawa ya soke wannan zargi. Kusan duk wannan abubuwan da ake ƙullawa Wallahi da hannunsu. Ko ɗansanda za a kawo Kano sai wanda suke so wanda zai kare muradunsu. Muna da bayanan sirri". Jaafar Jaafarya ce. Me zaku ce?...