Tuesday, December 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Nine zan lashe zaben shugaban kasa na 2027 saboda PDP ta mutu murus>>Kwankwaso

Nine zan lashe zaben shugaban kasa na 2027 saboda PDP ta mutu murus>>Kwankwaso

Duk Labarai
Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jami'iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa,shine zai lashe zaben shekarar 2027 saboda PDP ta mutu. Ya bayyana hakane a Katsina bayan kaddamar da ofishin jam'iyyar a kan hanyar IBB Way. Kwankwaso yayi kira ga mutanen jam'iyyarsa da kada su yadda a yaudaresu da Taliya da kudi yayin zabe inda ya jawo hankalinsu kan su ci gaba da aiki tukuru dan ci gaban jam'iyyar.
Ji Ainahin dalilin da yasa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa

Ji Ainahin dalilin da yasa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa me magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa na wucin gadi inda yace zai taci hutun sai abinda hali yayi. Ya bayyana dalilin cewa, wani daga cikin iyalansa ne ba lafiya shiyasa ya dauki wannan mataki duk da yake bai masa dadi ba. Saidai a binciken da jaridar Daily Nigerian ta gudanar, ta gano cewa ba haka abin yake ba. Jaridar tace wasu na kusa da shugaban kasa ne suka fara sakawa Ajuri ido kan cewa mukaman da yake rike dasu sun masa yawa kuma sun ci karo da aikinsa na matsayin me magana da yawun shugaban kasa. Dan hakane suka bukaci ya zabi daya daga cikin mukaman da yake rike dasu ya ajiye sauran, jaridar tace na hannun damar shugaban kasar, sun dauka cewa zai ajiye aikin magana da yawun shugaban kasa ne amma sai ya zabi ya ci ga...
Hoto:Kodai Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya sayi jirgin ruwanne? An hango wani jirgin ruwa da tutar Najeriya a kasar Faransa

Hoto:Kodai Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya sayi jirgin ruwanne? An hango wani jirgin ruwa da tutar Najeriya a kasar Faransa

Duk Labarai
An hango jirgin ruwa da tutar Najeriya a kasar Faransa. Wani jirgin ruwa ya dauki hankulan 'yan Najeriya bayan da aka hangoshi da tutar Najeriya a kasar Faransa. Bidiyon jirgin ruwan ya rika jawo sosai a shafukan sada zumunta inda aka rika bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai. Babban dalilin hakan shine a baya, shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu ya bayyana aniyar sayen jirgin ruwa,saidao da suka ta yi yawa ya fasa. Ganin wannan bidiyon yasa da yawa suka fara tunanin kodai Shugaban kasar har ya sayi jirgin ruwanne? Saidai hadimin Shugaban kasar ta fannin kafafen yada labarai, Otega Ogra ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labaran da ake yadawa cewa jirgin ruwan mallakin gwamnatin Najeriya ne. Ya bukaci a yi watsi da wannan jita-jita.
Dalilin da yasa man fetur dina ya zama fari ba kalar wanda aka Saba gani ba>>Dangote

Dalilin da yasa man fetur dina ya zama fari ba kalar wanda aka Saba gani ba>>Dangote

Duk Labarai
Shugaban rukunin kamfanin Dangote,Aliko Dangote ya bayyana dalilin da yasa man fetur dinsa ya zama fari ba kamar wanda aka saba gani ba. Dangote ya bayyana hakane bayan ganawa da manema labarai. Yace man matatar man fetur dinsa ya zama farine saboda zai fi zama me lafiya wanda ba zai cutar da muhalli ba ba kamar wanda aka saba gani ba. Yace kuma man fetur dinsa zai zama wanda baya cutar da ababen hawan mutane ba kamar wanda aka Saba amfani dashi ba.
Sojojin Najeriya 196 sun ajiye aiki saboda cin hanci da rashin gwarin gwiwar yin yaki

Sojojin Najeriya 196 sun ajiye aiki saboda cin hanci da rashin gwarin gwiwar yin yaki

Duk Labarai
Sojojin Najeriya 196 ne suka ajiye aiki saboda rashin gwarin gwiwar yin yaki da kuma cin hanci da rashin lafiya. Sojojin sun bukaci ajiye aikin ne bisa radin kansu inda suka mika bukatarsu ga shugaban sojojin Najeriya, Lt Gen Taoreed Lagbaja. Hakanan Shugaban sojojin ya bayyana amincewarsa akan ajiye aikin nasu. Majiyar Sahara Reporters tace sojojin duka masu kananan mukamai ne kuma sun bayyana ra'ayin shiga aikin soja a kasashen Amurka da Turai.

Gyaran nono da man kadanya

Amfanin Man Kadanya, Nono
Wasu bayanai sun nuna cewa man kadanya yana sanya nonon mace ya kara cikowa kuma ya mike sosai ko ya tashi tsayen, haka kuma a wani kaulin yana maida tsohuwa yarinya. Watau yana hana fatar nonon tsufa da wuri. Akwai hanyoyi biyu da wasu bayanai na gargajiya sukace ana amfani dasu wajan gyaran nono da man kadanya. Na farko shine, ana hadashi da man wanke baki watau Makilin a shafa akan nono zuwa wani lokaci a wanke. A bayani na biyu kuma, an samo cewa ana samun man kadanya ko man kade shi kadai a rika shafashi akan nono a hankali kamar ana mai tausa. Saidai duka wadannan bayanai basu da inganci a wajan likitoci, hanyoyi ne na gargajiya na gyaran nono a gida. Abinda ya tabbata shine, idan nononki na kaikayi, zaki iya shafa man kade, yana maganin kaikayin nono da kaikayin ka...