Tinubu Mutum Ne Mai Tausayin Bai Ji Daɗin Halin Da Aka Shiga Kan Tsadar Man Fetur Ba - Cewar Fadar Shugaban Kasa.
Fadar shugaban ƙasar ta ƙara da cewar, Shugaba Tinubu yana tausayin 'yan Najeriya, daga China ya umarci a wadata ƙasa da man fetur don samawa talaka sauƙin nemansa
Me zaku cev?
Na Samu Manyan Kyaututtuka Daga Wajen Manyan Murane A Yayin Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa Ta, Shi Ya Sa Bikin Ya Ɗauki Hankulan Jama'a A Kafar Sada Zumunta, Cewar Jarumar Samha M. Inuwa
Wane fata zaku yi mata?
Idan Ka Ce Mun Karbi Milyąɲ 16 Kai Kuma Ka Karbi Tálíyą, Ka Ga Kenan Ko A Nan Malumta Ta Yi Rana, Martanin Shéikh Umar Zaria Ga Masu Zargin Gwamnati Ta Tòshewa Malamái Baki Da Kudi Kan Matsalolin Nąjeriya.
Me za ku ce?
Gwamnatin tarayya ta fara siyar da metric ton 30,000 na nikakken shinkafa ga al'ummar Najeriya akan farashin naira n40,000 akan kowanne buhu mai nauyin kilo 50.
A ranar Alhamis ne a Abuja Ministan Noma, Abubakar Kyari ne ya kaddamar da rabon tallafin shinkafar kan wannan farashin.
Shin ko shinkafar tazo gare ku a halin yanzu ?
Dan jarida daga kasar Ghana, AbdulHakim Auwal ya kafa tarihin zama wanda yafi dadewa yana rungume da bishiya.
Dan shekaru 23 ya shafe awanni 24 da mintuna 21 yana rungume da bishiyar.
Hakan yasa ya shiga kundin tarihin Duniya na Guinness World Record.
Wanda ke rike da wannan matsayi a baya 'yar kasar Uganda ce me suna Faith Patricia Ariokot wadda ta yi awanni 16 tana rungume da bishiyar.
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni bai bar gidansa dake Abuja dan komawa jiharsa ba duk da kisan da 'yan Boko Haram sukawa mutane da yawa a jihar tasa.
Hakan yasa yake ta shan suka daga ciki da wajen jihar.
Dama dai tun a baya akwai rahotannin dake bayyana cewa,Gwamnan daga Abuja yake gudanar da mulkin jihar wanda hakan ya jawo suka gareshi.
Kingiyar ISWAP tace itace ke da alhakin kai harin inda tace ta kai harinne bayan da mutanen garin suka baiwa sojoji bayanan sirri wanda suka kai ga kashe membobinta.
Mutane da yawa dai daga jihar sun rika amfani da kafafen sada zumunta domin bayyana rashin jin dadinsu kan halin da gwamnan ya nuna.
Maraba Da Watan Mauludin Shugaba Sallallahu Alaihi Wasallam! Ya Allàh Ka Hore Mana Watan Máụludi Da Abun da Ya Ƙunsa, Ka Buɗe Mana Manyan Taskoki Na Arziƙi Domin Mu Yi Hidima Cikin Wànnan Watan Mai Albarka, Cewar Ɗan Ƙasar Chana, Masanin Hausa, Malam Murtala Zhang
Wane fata zaku yi masa?