Wednesday, January 7
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Kalli Hotuna: Jami’in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Kalli Hotuna: Jami’in Tsaron Gidan yari ya kashe abokin aikinsa saboda abinci a jihar Bauchi

Duk Labarai
Marigayi Aliyu Abubakar Ciroma. Jami'in tsaron gidan yari a garin Burra dake karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi ya kashe abokin aikinsa sabosa Abinci. Lamarin ya farune tsakanin Aliyu Abubakar Chiroma da Abokin aikinsa, Kabiru Abubakar wadanda suka jami'an tsrone na gidan yari koma kowa ya sansu Abokan junane. Ranar da abin zai faru sun je cin abinci tare sai Chiroma ya ciro abincin nasa inda Kabiru yace zai ci, anan rigima ta kaure tsakaninsu inda Chiroma yace ba zai ci mai abinci ba. A hakane sai Kabiru yawa Ciroma karo da kai, inda nan take ya fadi baya motsi. An garzaya dashi babban Asibitin Burra inda likitoci suka tabbatar ya mutu. Tuni aka kama Kabiru. Shugaban karamar hukumar Ningi, Hon Nasiru Zakari ya tabbatar da faruwar lamarin inda shima kakakin hukumar gid...
Ji abinda Bello Turji yayi bayan da yaga sojoji sun kashe me gidansa

Ji abinda Bello Turji yayi bayan da yaga sojoji sun kashe me gidansa

Duk Labarai
Tun bayan da sojojin Najeriya suka kashe Buzue gidan Bello Turji, Turjin ya aka rasa inda ya shige. Rahotanni sun bayyana cewa a yanzu haka, Bello Turji da mayakansa sun canja maboya. A baya suna zaunene a wani guri dake kusa da Tsafe. Amma yanzu sun tashi daga nan inda suka koma Munhaye duk a cikin jihar ta Zamfara. Babban me kawo rahotanni akan harkar tsaro, Zagazola makamane ya bayyana hakan.
Bidiyo: Kalli Yanda Sojan Ruwa wanda matarsa taje Berekete Family akan an daureshi yaki bayar da Bindigar sa

Bidiyo: Kalli Yanda Sojan Ruwa wanda matarsa taje Berekete Family akan an daureshi yaki bayar da Bindigar sa

Duk Labarai
Bidiyon sojan ruwa, Seaman Haruna wanda matarsa taje Brekete Family tana korafin an daureshi tsawon shekaru 6 ya bayyana inda aka ga yanda yaki bayar da Bindigarsa. Haruna Sojan ruwane amma sojojin kasa ne suka zo zasu kwace masa bindiga. Dalilin da yasa kenan yaki amincewa. https://twitter.com/ZagazOlaMakama/status/1836705544880390546?t=4bL54sBRrLWaVWsvPzIWag&s=19 A bidiyon an ga yanda yake kokawa da sojojin yayin da suke kokarin kwace masa Bindigar amma yaki. Daga karshe dai an kwace Bindigar aka kaishi aka daure.
Matawalle na da hannu a aikin ƴan fashin jeji, in ji Gwamnan Zamfara

Matawalle na da hannu a aikin ƴan fashin jeji, in ji Gwamnan Zamfara

Siyasa
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa magabacinsa, Bello Matawalle, na da hannu dumu-dumu a aiyukan ƴan fashin jeji da suka addabi jihar. Jaridar PUNCH ta rawaito cewa da ya ke magana a wani shirin siyasa na gidan talabijin na TVC a daren jiya Laraba, gwamnan ya yi ikirarin cewa, bisa bayanan da su ka samu, magabacinsa ya jagoranci gwamnatin da ke hada kai da ƴan fashin jeji su na aikata ta'addanci. Lawal ya kuma zargi gwamnatin da ta shude a karkashin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne karamin ministan tsaro da karkatar da kudaden jihar da kuma yin sakaci da harkar tsaro a jihar. “Eh, akwai batutuwa da yawa a baya daga gwamnatin da ta gabata. A gaskiya, bari in fadi wannan sarai: da nine shi (Matawalle) zan yi murabus in fuskanci duk wani zargi da ake min, haka...
Sheikh Nura Khalid Ya Halarci Taron Mabiya Shi’a Mai Taken ‘Makon Hadin Kai’

Sheikh Nura Khalid Ya Halarci Taron Mabiya Shi’a Mai Taken ‘Makon Hadin Kai’

Duk Labarai
Taro ne dai wanda shugaban mabiya Shi'a na Nijeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky ke jagoranta, an gudanar da shine a jiya Laraba a Abuja, inda ake gudnarwa domin haɗa kan malamai daga ɓangarori daban-daban dake fadin kasa baki daya, kama daga musilmai da Kìrìstòcì, inda kowane banhare ke amsa gayyata tare da yin jawabai da suke da alaƙa da haɗin kai da zaman lafiya. An gabatar da taron ne a Abuja inda malamin ya yi Magana akan Soyayyar Manzon Alĺàh SAW tare da amfanin hadin kai. Me za ku ce? Daga Abba Abdulaziz Fari Funtua
Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

Matar Shugaba Tinubu Ta Bada Gudummuwar Naira Milyan 500 Ga Al’ummar Maiduguri

labaran tinubu ayau, Siyasa
Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayar da gudunmuwar Naira miliyan 500 ga gwamnatin jihar Borno ta hanyar shirinta na Renewed Hope Initiative domin tallafawa wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Maiduguri. Uwargidan mataimakin shugaban kasa Hajiya Nana Shettima ta wakilci uwargidan mataimakin shugaban kasa kuma mataimakiyar shugaban kungiyar Renewed Hope Initiative, Uwargidan shugaban kasar ta jajantawa al'ummar Borno bisa bala'in da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyi da rayuwa ¹. A yayin bayar da gudummawar a gidan gwamnati, Hajiya Nana Shettima ta yaba wa Gwamna Farfesa Babagana Umara Zullum bisa gaggauwa da gaggawar da ya dauka kan bala’in da kuma tallafin da aka ba wa wadanda abin ya shafa. Gwamnan ya nuna godiya ga Sanata Oluremi Tinubu bi...
Kwankwaso Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan Hamsin Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno

Kwankwaso Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan Hamsin Ga Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Borno

Rabiu Musa Kwankwaso
Daga Abubakar Shehu Dokoki Ɗan Takarar Shugaban ƙasa, ƙarkashin Tutar Jam'iyyar NNPP a zaɓen daya gabata na 2023 Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bada wannan tallafin ne a wata ziyara ta musamman da ya kai jihar Borno domin jajanta musu bisa ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyyar raba ɗaruruwan mutane da gidajensu. Kwankwaso ya miƙa wannan tallafi ne ta hannun Gwamnatin Jihar Borno.
Ganin Bidiyon babiana tsirara ya jawo cece-kuce a Tiktok, Kalli Bidiyon martaninta

Ganin Bidiyon babiana tsirara ya jawo cece-kuce a Tiktok, Kalli Bidiyon martaninta

Babiana
Fitowar Bidiyon Tauraruwar Tiktok Babiana tsirara ya jawo cece-kuce a kafar Babiana dai ta yi suna sosai wajan kawo labarai akan abubuwan dake faruwa na yau da kullun musamman akan wanda mutane basa kyautawa. A wannan karin sai ga Bidiyonta ya fito tsirara wanda da yawa suka bayyana da cin zarafi a garet. Wasu sun yabama karfin gwiwarta inda wasu suka bata shawarar ta kai maganar kotu. Bidiyo ya bayyana na Babiana inda ta yi martani kan wannan Bidiyo nata da ya fita. https://twitter.com/arewablog_/status/1836500067991117929?t=iOz1mbCCglYjQ83JPVXb9g&s=19 Da alama dai Babiana ta nuna ko a jikinta.
Rikicin Aminu J Twon, Ordinary President da matar soja, Waye me gaskiya?

Rikicin Aminu J Twon, Ordinary President da matar soja, Waye me gaskiya?

Duk Labarai
Matar soja Seaman Haruna Abbas ta dauki zafi sosai akan neman taimakon da Aminu J. Town yace ya mata inda ta yi ikirarin cewa ba da saninta bane. Hakanan Shima Ordinary President, Ahmad Isah wanda ta je gidan talabijin da rediyonsa wajan neman hakkin mijinta, ya dauki zafi duk da dai yawa Aminu J. Town Nasiha. Hakanan a bangaren Aminu J. Town, shima bai dauki abin da sauki ba inda yayi zargin cewa ana son bata masa suna. Aminu J. Town dai ya bayyana cewa an nemi ya tarawa matar sojan ruwa, Seaman Haruna Abbas wadda ta kai kara gidan talabijin na Ordinary president inda tace an tsareshi tsawon shekaru 6 ba tare da hukunci ba kan zargin yayi yunkurin kashe ogansa. J Town yace yayi kokarin neman lambar matar inda ya kira dan neman izinin tara mata taimakon. Ga bidiyon wayar da ...
Wahala ta yi yawa, A tausayawa Talakawa>>Tsohon Shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya roki Gwammati

Wahala ta yi yawa, A tausayawa Talakawa>>Tsohon Shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya roki Gwammati

Duk Labarai
Tsohon shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya gayawa Gwamnati cewa wahalar da ake ciki a kasarnan ta yi yawa. Ya bayyanawa manema labarai cewa,mutane da yawa a yanzu basu da kudi inda kudin mota da sauran ababen hawa suka karu ga kudin makarantar yara ya karu kuma mutane basa iya cin abinci sau 3 a rana. Yace shi da wasu masu fada a ji sun baiwa gwamnatin tarayya shawarar yanda za'a fita daga cikin halin da ake ciki. Daya daga cikin hanyoyin kamar yanda yace sune gwamnatin ta sayi abinci ta rika sayarwa a farashi me sauki. Ya kuma bayar da shawara ga masu shirin yin zanga-zangar tsadar rayuwa ta ranar 1 ga wata October da kada a tayar da hankali a yi ta cikin lumana.