Monday, February 16
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Matatar man fetur din Dangote zata fara fitar da man fetur din zuwa kasashen Africa guda 7

Matatar man fetur din Dangote zata fara fitar da man fetur din zuwa kasashen Africa guda 7

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Matatar man fetur ta Dangote zata fara fitar da man fetur din zuwa kasashen Africa 7. A yanzu dai matatar ta shirya tsaf dan fara fitar da man fetur din zuwa kasashen South Africa, Angola, da Namibia. Sannan kuma tana tattaunawa da kasashen Niger Republic, Chad, Burkina Faso da Central Africa Republic dan fara kai musu man fetur din. Hakana wata majiya tace akwai karin kasashe da ake sa ran zasu bayyana son daukar man fetur din na Dangote. Misali kasar Ghana ma an bayyana cewa tana son fara magana da Dangote dan fara sayen man fetur dinsa. Shugaban hukumar kula da man fetur ta kasar Ghana,Mustapha Abdul-Hamid ya bayyana cewa fara siyen man fetur din daga hannun Dangote zai sa su daina sayen man fetur din daga kasashen Turai
Farashin kayan abinci ya tashi a kasuwannin Duniya

Farashin kayan abinci ya tashi a kasuwannin Duniya

Duk Labarai
Farashin kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Duniya inda suka yi tsadar da ba'a taba ganin irin ta ba a cikin watanni 18. Abinda yafi daukar hankali shine farashin man girki. Farashin man girkin ya karu da kaso 7.3 wanda ba'a taba ganin irin wannan tsada ba a cikin shekaru 2 da suka gabata. shi kuma Sukari ya tashi da kaso 2.6 Sai madara ta tashi da kaso 2.5 Farashin Namane kawai ya bai sauka ba.
Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja

Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja

Duk Labarai
Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja {"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Malama Hajara Kenan Wacce Ta Gina Katafaren Sabon Masallaci A Unguwar Ndeshi Dake Karamar Hukumar Mokwa A Jihar Neja Wace fata za ku yi mata?
Karanta Abubuwa 13 game da Kudirin Harajin da Shugaba Tinubu ya nace sai ya aiwatar duk da Kwamitinsa na tattalin arziki shun bashi shawarar kada ya aiwatar da kudirin

Karanta Abubuwa 13 game da Kudirin Harajin da Shugaba Tinubu ya nace sai ya aiwatar duk da Kwamitinsa na tattalin arziki shun bashi shawarar kada ya aiwatar da kudirin

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi fatali da shawarar kwamitinsa na tattalin Arziki da suka ce masa kada ya aiwatar da kudirin gyaran haraji inda yace sai yayi. Kakakin shugaban kasar,Bayo Onanuga ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar. Ga abubuwa 13 game da kudirin dokar da ya kamata ku sani: Canja tsarin karbar haraji na mutum gudaguda ga 'yan Najeriya a ciki da wajen kasar inda tsarin zai koma na zamani. Daina Karbar Haraji daga hannun masu fitar da kaya zuwa kasar waje dan karfafa fitar da kayan Najeriya zuwa kasuwannin Duniya. Daina karbar Haraji daga kananan 'yan Kasuwa. Ba za'a karbi Haraji ba a hannun masu daukar Mafi karancin Albashi ba, sannan ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu za'a rage musu Haraji zuwa kaso 90. Ba za'a rika karb...
ƊAN DUNIYA: An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki

ƊAN DUNIYA: An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki

Duk Labarai
An kori mutumin da ake zargi da keta haddin matan aure kusan 400 a kasar Equatorial Guinea daga aiki Shugaban kasar Equatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo, ya sanar da korar Baltasar Ebang Engonga daga shugabancin hukumar kula da binciken kudi ta kasar biyo bayan zargin fitar wasu faya-fayan bidiyo na keta haddin wasu matan manyan mutane a kasar. Shugaban kasar ya sanar da nada Zenón Obiang Obiang Avomo a matsayin sabon shugaban hukumar bayan sallamar Baltasar.
‘Yansanda a jihar Katsina sun dakile yunkurin gàrkùwà da mutane inda suka kubutar da mutane 21

‘Yansanda a jihar Katsina sun dakile yunkurin gàrkùwà da mutane inda suka kubutar da mutane 21

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta sanar da cewa ta dakile yunkurin garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina inda ta kubutar da mutane 21. Kakakin 'yansandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitr ga manema labarai inda yace sun samu wannan nasara ne a aikin da suka yi tare da sojoji da kuma 'yan Bijilante. Yace sun dakile yunkurin garkuwa da mutanen ne a Ka’ida, Unguwar One Boy, da Danmarke quarters duka a Jibia ranar 7 ga watan Nuwamba. Yacw maharan sun kai harinne inda su kuma suka kai dauki cikin gaggawa inda aka shafe awa guda ana bata kashi. Yace 'yan Bindigar sun tsere daga wajan ba shiri. Yace sun kubutar da mutane 16 saidai 5 daga ciki sun samu raunukan bindiga. Yace jami'in Bijilante daya da jami'in hukumar t...