Monday, July 6
Shadow

Author: Bashir Ahmed

El-Rufai ya bude shafin TikTok, ya samu mabiya 200,000 cikin Awa 24

El-Rufai ya bude shafin TikTok, ya samu mabiya 200,000 cikin Awa 24

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bude shafi a dandalin sada zumunta na TikTok. Cikin awa 24 kacal da budewa, El-Rufai ya samu sama da mabiya 200,000, yayin da bidiyon sanarwarsa ya tara masu kallo miliyan 1.9 da kuma sharhi (Comment )sama da 21,000. A cikin bidiyon, El-Rufai ya bayyana cewa shafinsa na TikTok zai mayar da hankali kan ra’ayoyinsa a siyasa da kuma sabuwar jam’iyyarsa, SDP. "Wannan shine kawai shafina na gaskiya a TikTok. Ku biyo ni domin kallon bidiyo, yin sharhi da tattaunawa kan siyasar Najeriya da ayyukan sabuwar jam’iyyarmu, SDP. Maraba da ku," in ji shi.
Da Ban cire tallafin man fetur da daukar matakai masu tsauri ba da Najeriya ta talauce saboda shuwagabannin da suka gabata wadaka suka yi da dukiyar daya kamata a gina Al’umma>>Tinubu

Da Ban cire tallafin man fetur da daukar matakai masu tsauri ba da Najeriya ta talauce saboda shuwagabannin da suka gabata wadaka suka yi da dukiyar daya kamata a gina Al’umma>>Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewada bai cire tallafin man fetur ba da daukar tsauraran matakai na gyaran tattalin arzikin ba da Najeriya ta talauce. Yace amma matakan da ya dauka hadi da goyon baya da hakurin da 'yan Najeriya suka yi masa yasa a yanzu gashi an fara cin amfanin abin. Yace Farashin kayan abinci ya sauka musamman a cikin watan Ramadana sannan kuma gashi Darajar Naira na ta farfadowa a hankali. Shugaban ya bayyana hakane a yayin da ya karbi bakuncin 'yan majalisa da suka yi aiki tare a lokacin yana dan majalisa. Ya kuma bayyana tsarin Dimokradiyya a matsayin tsari mafi kyawu wanda shine yake kawowa kasa ci gaba.
Mata tasa ‘yansanda sun kama mijinta saboda ya kara aure

Mata tasa ‘yansanda sun kama mijinta saboda ya kara aure

Duk Labarai
Wata mata a jihar Legas tasa 'yansanda sun kama mijinta aun kulle bayan da ya kara aure. Mutumin me suna Charles Chiawa an tsareshi a ofishin 'yansanda kamar yanda matarsa, Uche Chiawa ta bukata. Sun shafe shekaru 20 da yin aure inda Charles yace sun fara samun matsala ne bayan da ya kara aure har ya haihu da amaryarsa. Yace yana da damar kara aure saboda auren gargajiya aka musu shi da uwar gidansa. Saidai matar tasa Uche tace ba auren gargajiya kadai suka yi ba, hadda na kotu kuma tace yana yawan dukanta ne shiyasa tasa a tsareshi. Rahoton yace uwargidan mutumin na da alaka da wata DPO na 'yansanda wanda hakanne ya bata damar sawa a daureshi. Amaryarsa ta je ofishin 'yansandan inda ta nemi a sakeshi amma aka ki bata belinsa aka koreta. Saidai da aka nemi jin ta baki...
Ji yanda Wani mutum ya yanke jiki ya fadi ya mùtù a akin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin ficewa daga dakin

Ji yanda Wani mutum ya yanke jiki ya fadi ya mùtù a akin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin ficewa daga dakin

Duk Labarai
Wani mutum dan kimanin shekaru 31 ya yanke jiki ya fadi ya mutu a dakin karuwa bayan ya kammala abinda yake yana shirin fita daga dakin. Lamarin ya farune a sabuwar Kutunku dake Gwagwalada a baban birnin tarayya, Abuja. Lamarin ya farune ran Asabar da misalin karfe 5 na yamma inda karuwar data ga haka ya ruga ta sanar da manajansu. Manajan ya garzaya dakin inda ya gane mutumin me suna Ajayi Nicholas inda ya yi gaggawar sanar da 'yan uwansa dake yankin. An garzaya dashi Asibiti inda acan likitoci suka tabbatar da ya mutu 'Yansanda sun je wajan inda suka gudanar da bincike kuma tuni aka kai gawar wanda ya mutun makwanci.
Abinda sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa mutane su fara jin tsoron baiwa mata matsayin siyasa>>Sanata Godswill Akpabio

Abinda sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa mutane su fara jin tsoron baiwa mata matsayin siyasa>>Sanata Godswill Akpabio

Duk Labarai
Sanata Godswill Akpabio wanda shine kakakin majalisar dattijai ya bayyana cewa, abinda Sanata Natasha Akpoti ta yi zai sa a fara jin tsoron baiwa mata mukaman siyasa. Ya bayyana hakanne inda yace yanzu da Kamala Harris ta yi irin wannan abin da Sanata Natasha Akpoti ta yi da zata kai matsayin mataimakiyar shugaban kasa? Yace amma yana kira ga mutane da kada laifin wani ya shafi wani, yace yana da 'ya'ya mata 4 yana son a goyi bayansu da basu dama su kai matsayi babba dama sauran mata na Najeriya.
Allah Sarki:Ji yanda wata mata ta yanke jiki ta fadi ana tsaka da tafsirin Azumin watan Ramadana

Allah Sarki:Ji yanda wata mata ta yanke jiki ta fadi ana tsaka da tafsirin Azumin watan Ramadana

Duk Labarai
Wata mata me suna Maman Zainab dake da kimanin shekaru 42 ta yanke jiki ta fadi ta rasu a yayin da ta halarci wajan tafsirin Azumin watan Ramadana. Lamarin ya farune a Masallacin Gawu dake Abaji a babban birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Unguwar me suna Ismail Bala ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin. Inda yace abin ya farune ranar Talata da misalin karfe 11:23 na safe. Matar dai ta bar gida lafiya Qalau inda makwabtanta 3 suka rakata zuwa wajan Tafsirin saidai ana tsaka da Tafsirin, ta gayawa na kusa da ita cewa tana jin jiri. Ta mike zata tashi sai ta yanke jiki ta fadi. Sauran matan sun dauke zuwa Asibiti a Gawu Babangida inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu. Likita ya bayyana hawan jini a matsayin abinda yayi sanadiyyar mutuwar ta. Tuni aka...
Allah Sarki: Kalli Hotunan Mahaddacin Qur’ani da ‘yan Bìndìgà suka yi garkuwa dashi da iyayensa a jihar Katsina

Allah Sarki: Kalli Hotunan Mahaddacin Qur’ani da ‘yan Bìndìgà suka yi garkuwa dashi da iyayensa a jihar Katsina

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Matashin Hafizin Ku'rani Kuma Ɗalibin Aji Uku A Sashen Koyan Aikin Likita Na Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria, Abdulsalam Rabi'u Faskari Kenan Da Ƴan Bìñďìģa Suka Sace Da Mahaifinsa Da Wasu Yayyansa Akan Hanyarsu Ta Komawa Gida Faskari, Bayan Gwamna Dikko Radda Ya Karrama Shi A Ranar Talata Da Ta Gabata Allah Ya Kuɓutar Da Su Cikin Aminci! Daga Jamilu Dabawa
Gwamnatin Buhari ce mafi muni a Tarihin Najeriya amma naga Alamar Gwamnatin Tinubu na neman yin abinda yafi muni>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Gwamnatin Buhari ce mafi muni a Tarihin Najeriya amma naga Alamar Gwamnatin Tinubu na neman yin abinda yafi muni>>Tsohon Shugaban kasa, Obasanjo

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da cewa, itace gwamnati mafi muni a tarihin Najeriya. Ya bayyana hakane a cikin wani sabon littafinsa da ya rubuta me suna “Nigeria: Past and Future.” inda yace amma yaga Gwamnatin Tinubu ta kama hanyar zarce ta Buhari wajan zama mafi muni. Obasanjo ya rubuta littafinne a yayin da ya cika shekaru 88 da haihuwa. Ya bayyana aikin gina titin Lagos zuwa Calabar da ake kashe ...
Buhari ya watsawa El-Rufai kasa a ido inda yace, Ina nan daram a jam’iyyar APC – Buhari

Buhari ya watsawa El-Rufai kasa a ido inda yace, Ina nan daram a jam’iyyar APC – Buhari

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce har yanzu shi ɗan APC ne, kuma ya fi so a rinƙa alaƙanta shi da jam'iyyar. Wannan dai ya biyo bayan wata tattaunawa da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi da BBC ranar Alhamis inda ya ce "sai da Buhari ya amince sannan na bar jam'iyyar APC zuwa SDP." Buhari ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da tsohon kakakinsa, Garba Shehu ya fitar, inda ya ce ba ya so ya bar kowa a cikin ruɗani game da inda yake, domin a cewars...
Ƴan bìndìgà sun sace wanda ya lashe gasar karatun al-Qur’ani ta Najeriya

Ƴan bìndìgà sun sace wanda ya lashe gasar karatun al-Qur’ani ta Najeriya

Duk Labarai
Ƴan bìndìgà sun sace mutumin da ya zama zakaran gasar karatun al'qur'ani ta bana tare da danginsa a kan hanyar Faskari zuwa ƴankara a jihar Katsina. Shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Hon Musa Ado Faskari ya shaida wa BBC faruwar lamarin, inda ya ce ƴanbindigar sun sace Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da mahaifinsa da ƴan'uwansa a lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun halarci fadar gwamnatin Katsina inda gwamna ya karrama gwarzon. Hon. Musa Faskari ya ce gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umaru Radda ne ya gayyaci , Abdulsalam Rabi’u Faskari tare da iyalansa ciki har da mahaifinsa a ƴan'uwansa, domin karrama shi bisa nasarar da ya samu ta zama gwarzon gasar karatun al-qur'ani da aka kammala a jihar Kebbi. ''A kan hanyarsu ta komawa gida ne, sun baro Funtua a kan hanyar F...