Farashin dala a kasuwar Chanji a yau na cewa, a kasuwar Gwamnati ana sayar da Dalar akan Naira 1,448.68
Yayin da a kasuwar bayan fage kuma ake sayar da ita akan Naira 1,449.56.
Tsohon gwamna jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai na ci gaba da shan Yabo saboda yanda yake Hidimtawa mahaifiyarsa da ya kai aikin Umrah.
An ganshi yana turata a cikin keken Guraku.
https://www.tiktok.com/@niima30/video/7583343970944552212?_t=ZS-92Eaw70KsHB&_r=1
Wani dan kudu da ya ga wani matashi daga jihar Katsina a cikin bola yana nema roba ya fitar dashi ya masa fadan cewa abinda yake bai kamata ba.
Matashin ya ce yana neman Roba ne saidai dan kudun yace masa cuta da zata sameshi zata mai illa.
Dan kudun na ta shan Yabo a wajan mutane.
https://twitter.com/NuhuSada0/status/2000331759758791144?t=uG8O1iY7rTr2GmNtysAsCA&s=19
Attajirin dan kasuwa, BUA ya rabawa ma'aikatan sa makudan kudade.
Ya baiwa ma'aikata 5 Biliyan 1 kowannensu.
Wasu Biyar din kuma an basu Naira Miliyan 500 kowannensu.
Sannan wasu da yawa sun samu kyautar Naira Miliyan 20 har zuwa Naira Miliyan 5.
Jimullar ma'aikata 510 ne ya rabawa Dala Miliyan $20.6
Wannan matashin me suna Ejibo ya shafe shekaru 6 da watanni 3 a gidan yari kamin daga baya aka gano bashi da laifi.
Dan uwansa ne ya wallafa a shafinsa na sada zumunta yana alhinin abi .
An hango motocin yakin neman zaben gwamnan jihar Gombe na Malam Isa Ali Pantami sun fara bayyana.
Bidiyon motocin ya bayyana a kafafen sada sumunta inda ake ta sam barka.
https://twitter.com/abba_hamani/status/2000294529539395735?t=_lfL6XBccmHio3XtxGy1aQ&s=19
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami ya koka da cewa EFCC sun hanashi Beli.
Hakan na zuwane bayan da EFCC ta kamashi tana bincikensa kan zargin almundahanar makudan kudade.
Daga cikin kudaden da ake zargin Malami da cinyewa hadda kudaden Abacha da aka kwato.
Masoyan Naziru Ahmad Sarkin Waka sun bayyana jin dadinsu bayan da suka ga gwanin nasu Attajirin Naj,Aliko Dangote ya kirashi sun dauki hoto.
A kwanannan ne da aka daura auren wani dan uwan Dangoten wanda Naziru Sarkin Waka da Nazifi Asnanic suka yi waka tare a wajan taron.
https://www.tiktok.com/@mc_sharinah/video/7583447766697790740?_t=ZS-92E1CsD8ozp&_r=1
Matar Sheikh Zakzaky ta bayyana cewa, masu rokon a yafewa Buhari suna kara ja mai Azabane a qabarinsa.
Tace ita idan ta tashi daga bacci da dare kamin ta fara Sallah sai ta fara Tsynewa marigayi tsohon shugaban kasar
Ta bayyana hakane a wata hira da aka yi da ita.
https://www.tiktok.com/@real_dadson/video/7583499258813222165?_t=ZS-92DzV5fnXij&_r=1
A baya dai Sheikh Zakzaky yace ba zasu yafewa Buhari ba.
Bayanan sirri sun fito da suka bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince a karawa dogarinsa mukami zuwa Brigadier General.
Sannan kuma a barshi ya ci gaba da gadinsa, kamar yanda wata wasika da Nuhu Ribadu ya aikawa shugaban sojoji ta bayyana.
An dai bayyana cewa, Wasikar ta sirri ce, saidai zuwa Yanzu Gwamnati bata ce uffan ba akanta.
Rahotanni dai sun ce idan hakan ta tabbata to an saba doka domin za'awa dogarin na shugaba Tinubu karin mukami ne fiye da sauran abokan karatunsa.