Sunday, December 29
Shadow

Author: Auwal Abubakar

Hoto: An kama mutane na 9 saboda yin kashi a bainar jama’a

Hoto: An kama mutane na 9 saboda yin kashi a bainar jama’a

Duk Labarai
Hukumar kula da muhalli ta jihar Legas ta sanat da kama mutane 9 saboda yin kashi a bainar jama'a. Kwamishinan muhalli na jihar, Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan inda yace sun dukufa dan ganin sun hana fitsari da kashi a bainar jama'a a Legas dan tabbatar da tsaftar garin. Ya kara da cewa a baya sun kama mutane 17 saboda yin kashi da fitsari a bainar jama'a da kuma kin amfani da gadar sama da aka ware dan mutane.
Hoto: Dan shekaru 15 ya tsallaka gidan makwabtansu yawa yarinya me shekaru 14 fyade

Hoto: Dan shekaru 15 ya tsallaka gidan makwabtansu yawa yarinya me shekaru 14 fyade

Duk Labarai
Lamarin ya farune a jihar Ebonyi inda yaron dan gidan wani sojane, ya tsallaka gidan makwabta. Yayi karo da yarinyar tana bacci inda ya dauki tabarya ya maka mata sannan ya mata fyade. Hayaniya tasa mutane suka kai dauki inda aka kamashi. Lamarin ya farune ranar 28 ga watan Augusta na shekarar 2024. Tuni dai aka kama yaron inda ita kuma yarinyar aka kaita Asibiti.
Bashi ya mana katutu wanda hakan ke barazana ga wadata Najeriya da man fetur>>NNPCL

Bashi ya mana katutu wanda hakan ke barazana ga wadata Najeriya da man fetur>>NNPCL

Duk Labarai
Kamfanin mai na kasa,NNPCL ya koka da cewa bashin masu kawo man fetur ya mai yawa. Kamfanin ya tabbatar da hakan ne ta bakin me magana da yawunsa, Olufemi Soneye inda yace kamfanin na fama da matsalar bashin masu kawo mai. Yace hakan na barazana ga wadata kasarnan da man fetur. Saidai ya bayyana cewa, NNPC ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan ganin ta ci gaba da gudanar da aiki a matsayin babbar me wadata kasarnan da Man fetur.
Tsaka Mai wuya: Da wuya Osimhen ya bugawa Napoli wasa a wannan shekarar

Tsaka Mai wuya: Da wuya Osimhen ya bugawa Napoli wasa a wannan shekarar

Duk Labarai
Rikicin dan wasan Najeriya, Victor Osimhen da kungiyarsa ta Napoli ya kara kamari inda a yanzu babu tabbacin zai bugawa kubgiyar wasa a wannan kakar duk da yake cewa har yanzu yana kungiyar bai samu tafiya Chelsea kamar yanda ya so ba. Osimhen dai yaki yin atisaye da kungiyar da tunanin cewa zai barta amma sai ciniki bai kaya ba na komawa Chelsea. Hakanan kungiyar Napoli ta buga wasanta na farko da Parma kuma ba'a ga Osimhen a ciki ba wanda dama bai buga wasannin Preseason ba. Kungiyar ta Napoli dai tuni ta baiwa Remolu Lukaku lamba 9 da Victor Osimhen ke goyawa. A yanzu dai an dakatar da Osimhen daga duka wasanni da atisayen kungiyar ta Napoli kuma bai san makomarsa ba.
Buhari Bai Taba Son Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Bai Taba Amincewa Da Osinbajo Ba – Sule Lamido

Buhari Bai Taba Son Tinubu A Matsayin Shugaban Ƙasa Ba, Bai Taba Amincewa Da Osinbajo Ba – Sule Lamido

Duk Labarai
Daga: Abbas Yakubu Yaura Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba son shugaba Bola Tinubu ya gaje shi ba a matsayin shugaban kasa. Lamido ya kuma ce Buhari bai taba amincewa da tsohon mataimakinsa Yemi Osinbajo ya gaje shi ba, ya kara da cewa tsohon shugaban kasar yana son tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan ne ya gaje shi. Lamido ya ci gaba da cewa, babu wanda ya isa ya zama shugaban kasa saboda Tinubu mutum ne jajirtacce kuma mai son kansa. Da yake magana da jaridar Tribune, Lamido ya ce: “Kafin taron, shi (Tinubu) yana Abeokuta, jihar Ogun, inda ya yi takama da cewa lokaci ya yi da zai mulki Najeriya. Shi kuwa Buhari saboda butulci yana kallo. Bai taba son Tinubu ba. Akwai wanda yake so. “Bai ma aminta da nas...