Sunday, January 18
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyon ya bayyana ana ta Allah wadai da wannan malamar da ta yiwa wannan dalibin nata me shekaru 16 fàdyè

Bidiyon ya bayyana ana ta Allah wadai da wannan malamar da ta yiwa wannan dalibin nata me shekaru 16 fàdyè

Duk Labarai
Anata Allah wadai da wata malamar makaranta me suna Zvikomborero Maria Makedenge me shekaru 33 bayan samunta da yiwa dalibinta me shekaru 16 fyade. Bidiyon yanda lamarin ya faru ya karade shafukan sada zumunta saidai saboda tsiraici da aka nuna a cikin Bidiyon hutudole ba zai iya kawo muku shi ba. Rahotanni dai sun ce an kama malamai kuma har an yanke mata hukuncin zaman gidan kaso. Lamarin ya farune a wata Makarantar Sakandare dake kasar Zimbabwe.
Kalli Bidiyon yanda Sojojin Sama suka yi amfani da lema suka fice daga cikin jirgin yàkìn su da ya kama da wùtà a jihar Naija

Kalli Bidiyon yanda Sojojin Sama suka yi amfani da lema suka fice daga cikin jirgin yàkìn su da ya kama da wùtà a jihar Naija

Duk Labarai
Jirgin sama na rundunar sojojin sama ta Najeriya yayi hadari a jihar Naija. Jirgin ya tashi ne a sansanin sojin dake Kainji inda jim kadan da tashinsa ya samu matsala. Jirgin na daukene da sojojin sama biyu amma sun samu damar ficewa daga ciki kamin ya fadi. shugaban sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya jinjinawa kokarin da sojojin suka yi na karkatar da jirgin bai fada kan mutane ba. Yace sojojin na cikin koshin lafiya kuma ana kara duba lafiyarsu. https://twitter.com/NTANewsNow/status/1997385557052465459?t=Od8X2KFZohUvyG6rg9_6tA&s=19
Wani Rahoto yace An fi shan giya a jihohin Arewa

Wani Rahoto yace An fi shan giya a jihohin Arewa

Duk Labarai
Wani Rahoto daga kafar Statisense yace wai jihohin Arewa ne suka fi shan giya. Rahoton yace jihohin Arewa maso yamma ne akan gaba. Sai jihohin Arewa ta tsakiya na biye musu baya. Sai Jihohin Arewa maso gabas. Sai jihohin Yarbawa na Kudu maso yamma. Sai jihohin Kudu maso kudu. Sai Jihohin Kudu maso yamma. HEAVY ALCOHOL CONSUMERS — 2024 Zone — Male | Female in 1,000 population:North West — 624 | 30 *North Central — 140 | 56North East — 66 | 298South West — 40 | 46South South — 24 | 63South East — 15 | 25 NB : asterisk means insufficient sample size #Statisense(NDHS 2024)
Da Duminsa: Wani Jirgin Sojojin Saman Amurka ya sauka a Najeriya

Da Duminsa: Wani Jirgin Sojojin Saman Amurka ya sauka a Najeriya

Duk Labarai
Rahotanni daga Abuja sun bayyana cewa wani jirgin sojojin saman Amurka daya taso daga kasar ta Amurka me suna, A US Air Force C-37B ya sauka a Abuja. Jirgin ya saukane a daren jiya. Bayan Awanni 4 Jirgin ya kuma tashi zuwa kasar Ghana. Brant Philip me kawo rahoto akan harkar tsaro a Afrika ne ya ruwaito wannan labari. https://twitter.com/BrantPhilip_/status/1997243829930561958?t=7g_arf0RZhpWPaLJqC8kHA&s=19