Tuesday, November 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Bidiyon: Wata mata ta kai Malamin Addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Tukur Almanar Berekete Family kan zargin ya musu kwacen Fili ita da ‘ya’yanta

Bidiyon: Wata mata ta kai Malamin Addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Tukur Almanar Berekete Family kan zargin ya musu kwacen Fili ita da ‘ya’yanta

Duk Labarai
Wata mata ta kai babban malamin addinin Islama dake Kaduna, Sheikh Tukur Almanar gaban gidan talabijin din Brekete Family inda take zargin shi da matarsa sun mata kwacen Fili. Tace Mijinta ne ya sayi Filin ya barwa 'ya'yansa mata Gado inda ita kuma matar Almanar daga baya aka kaita aka sayar mata da filin. Tace amma an je wajan Sarki da ya sayarwa da matar Almanar fili yace shi ba filin marayunnan ne ya sayar mata ba, wanine amma ita ta dage tace wannan Filin marayun take so. Tace daga baya Almanar yace matar ta sayar masa da filin. An kira malam inda yace ba zai ke Brekete Family ba saidai lauyansa ya je. https://www.tiktok.com/@badyblog/video/7664588114043669780?_r=1&_t=ZS-98DchsUYSig https://www.tiktok.com/@badyblog/video/7664402483535514900?_r=1&_t=ZS-9...
Kalli Bidiyon: ‘Yan Argentina na shan suka saboda yanda suka juya baya yayin da ake baiwa Spain World Cup

Kalli Bidiyon: ‘Yan Argentina na shan suka saboda yanda suka juya baya yayin da ake baiwa Spain World Cup

Duk Labarai
'Yan kwallon Argentina sun gamu da suka a yayin da suka juya baya a daidai lokacin da ake baiwa kasar Spain kofin World Cup. Da yawa dai sun bayyana cewa hakan bai dace ba kuma ba abune na nuna karamci ba ga gasar ta World Cup. https://twitter.com/i/status/2079052184092877123 Ko da bayan da aka tashi wasan na World Cup dai sai da 'yan kasar Argentina suka tayar da rigima sukai ta fada da 'yan kasar Spain.
Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda Kocin Argentina, Lionel Scaloni ya fashe da kuka a gaban manema labarai bayan rashin nasara a wasan karshe na World Cup

Allah Sarki Kalli Bidiyon yanda Kocin Argentina, Lionel Scaloni ya fashe da kuka a gaban manema labarai bayan rashin nasara a wasan karshe na World Cup

Duk Labarai
Kocin Argentina, Lionel Scaloni yayin da yake ganawa da manema labarai bayan kammala wasan karshe na gasar World Cup, ya fashe da kuka. A karshe dai bai samu kammala Hirar ba, haka ya tashi ya tafi ya baiwa manema labaran hakuri. Spain tawa Argentina 1-0 a wasan na karshe na gasar World Cup wanda hakan ya baiwa Spain damar lashe kofin Duniya din. https://www.tiktok.com/@dailymailsport/video/7664581493007633686?_r=1&_t=ZS-98DACaXFORJ
A karin Farko, Budurwar Tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha da ya rasu suna tare ta bayyan ainahin abinda ya faru

A karin Farko, Budurwar Tsohon shugaban kasa, Marigayi Janar Sani Abacha da ya rasu suna tare ta bayyan ainahin abinda ya faru

Duk Labarai
A cikin wani littafi da tsohon jami'in hukumar DSS me suna Dennis Amachree ya rubuta, ya bayyana cewa, shine ya binciki Budurwar tsohon shugaban kasa, Marigayi, Janar Sani Abacha wadda suna tare ne tsohon shugaban ya rasu. Amachree yace Janar Sani Abacha ya rasu ne a cikin fadar shugaban kasa yayin da suke tare da Budurwarsa a dakin saukar baki na cikin fadar. Yace da budurwar Abacha ta lura da ya rasu sai ta tsere ta hau jirgi ta tafi Legas. Yace amma sun bibiyeta suka kamota. Yace da suka kamota ta bayyana musu cewa, ba ita ta Qashe Abacha ba, suna tsaka da soyayya akan gado ya rasu. Yace bayan ya kammala Bincike ta ne sai aka mayar da ita zuwa Abuja. Yace wannan shine ainahin abinda ya faru sabanin abinda aka ruwaito a kafafen watsa labarau.