BATUN ŹÀNĢA-ŹÀNĢA: Minista Na So Jama’a Su Ķara Haƙuri Ďomin Tinubu Yana Ķoƙarin Ŕage Matsi
BATUN ŹÀNĢA-ŹÀNĢA: Minista Na So Jama'a Su Ķara Haƙuri Ďomin Tinubu Yana Ķoƙarin Ŕage Matsi
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga 'yan Nijeriya, musamman matasa masu shirin zanga-zanga, da su yi haƙuri.
A halin yanzu wasu 'yan Nijeriya na ta yin shelar cewa za su yi zanga-zangar lumana a ƙarshen wannan watan domin bayyana ɓacin ran su kan matsin tattalin arziki da ake fuskanta a yau.
A wata hira da ya yi da BBC Hausa a ranar Asabar, ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wasu muhimman matakai domin magance matsalolin da 'yan Nijeriya ke fuskanta.
Ya ce: “Akwai mataki na farko da gwamnati ta ɗauka na a samu a raba kayan abinci ga al'ummar Nijeriya. An kai shinkafa jihohi duka ga baki ɗaya talatin da shida da kuma yankin Abuja.”
Ya ƙara...