Monday, January 20
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Gyaran fuska da man kwakwa

Amfanin Kwakwa, Gyaran Fuska, Kwalliya
Man kwakwa na da amfani da yawa a fuska, yana sa fuska ta yi laushi, yana maganin ciwo yayi saurin warkewa, yana kuma taimakawa wajan rage kumburi. A wannan rubutun, zamu kawo muku amfanin man kwakwa wajan gyaran fuska. Wani bincike ya tabbatar da man kwakwa na taimakawa sosai wajan maganin kurajen fuska da kuma yana a matsayin rigakafi dake hana kurajen fitowa mutum a fuska. Hakanan man kwakwa na taimakawa wajan kawar da alamun tsufa a fuska. Ana shafa man kwakwa a fuska ko jiki kamar yanda akw shafa sauran mai. Hakanan ana cinshi da abinci.

Gyaran fuska da man zaitun

Gyaran Fuska, Kwalliya
Man zaitun na da matukar amfani sosai,a wani bincike da masana suka yi wanda aka gwada akan bera, ya nuna cewa man zaitun din na kashe kaifin Kansa ko cutar daji. A wannan rubutu zamu yi bayanin amfanin man zaitun wajan gyaran fuska. Babban amfanin Man zaitun ga fuska shine yana kawar da alamun tsufa dake fuskar mutu. Wannan ya tabbata, masana sun yi amannar man zaitun yana kawar da alamun tsufa da suka hada da duhun fuska da tattarewarta sosai idan ana amfani dashi aka-akai. Man Zaitun yana matukar amfani sosai wajan kawar da matsalar fuska,musamman kurajen fuska. Hakanan yana maganin duhun da fuska ke yi idan an dade a rana. Ana iya amfani da man zaitun shi kadai ba tare da hadashi da wani abuba a fuska.

Gyaran fuska da madara

Gyaran Fuska, Kwalliya
Wani bincike ya tabbatar da ana amfani da madara a matsayin Cleanser a fuska dan kawar da kurajen fuska, duhun fuska, da matacciyar fatar fuska. Binciken ya bayyana cewa, madarar tana kuma hana bakaken abubuwa bayyana a fuska da kuma bude kofofin gashin fuska. Ana iya amfani da auduga ko kyalle me kyau a goga madarar a fuska. Ana amfani da madara wajan kara hasken fata, kuma akwai mayukan kara hasken fata da yawa da aka hadasu da madara. Saidai babu wani bincike na bangaren masana lafiya daya tabbatar da madara na kara hasken fata. Hakan na nufin za'a iya gwadawa a gani, idan yayi reaction sai a daina, idan kuma bai yi ba, za'a iya yin sati 4 ana gwadawa ana idan fata zata yi haske. Bayan dadewa a rana, ana iya amfani da Madara a shafa a fuska dan kawar da duhun fuska da ra...

Maganin kurajen fuska

Gyaran Fuska, Kwalliya
Akwai hanyoyi da yawa da ake magance matsalar kurajen fuska. A cikin wannan rubutu, zamu yi bayani kan yanda ake magance kurajen fuska ta hanyoyi daban-daban. Saidai kamin mu fara, a sani cewa, idan ana da kurajen fuska, kada a rika wasa dasu da hannu ko sosawa, ko da suna kaikai kuwa. Hakan zai kara dagula matsalar ne maimakon ya magance ta, kai cuta ma zata iya shiga, dan haka a kiyaye. Hanyoyin da za'a iya amfani dasu a matsayin maganin kurajen fuska sun hada da: Ana Amfani da kankara ko ruwan Sanyi: Idan aka dora kankara ko ruwan sanyi akan kurajen fuska, suna daina kaikayi da kumburi kusan nan take. Ana iya samun kankarar a nade a tsumma me tsafta a rika dorawa a jikin kurajen, ko kuma a samu ledar ruwa me sanyi a rika dorawa. Idan an dora a rika barinshi yana kai mintu...

Maganin goge tabo a fuska

Gyaran Fuska, Kwalliya
Tabon fuska matsalace dake damun mata da yawa, kuma akwai hanyoyi da yawa da ake amfani dasu wajan goge shi. Ga wasu daga cikin hanyoyin da ake amfani dasu wajan goge tabon fuska kamar haka: Amfani da Aloe Vera: Ana amfani da mai ko ruwan Aloe Vera wajan goge tabon fuska kuma yana aiki sosai, ana iya sayen man Aloe Vera a shagon saida mai wanda ba'a hadashi da komai ba, a duba roba ko kwalin man a tabbatar ba'a hadashi da giya ba ko wasu abubuwa na daban ba, kamin a siya, mafi kyawun hanyar samun mai ko ruwa Aloe Vera shine a hadashi a gida. Ana samun ganyen Aloe Vera a kankare koren ganyen dake jikinshi a matso ruwan a rika shafawa a fuska dan maganin tabon fuska, mun yi cikakken bayani kan yanda ake amfani da Aloe Vera wajan gyaran fuska Hakanan ana amfani da Zuma wajan cire ...

Gyaran fuska da aloe vera

Gyaran Fuska, Kwalliya
Aloe Vera na gyara fatar fuska sosai inda yake kawar da dattin fuska da kara mata haske kuma idan aka duba za'a ganshi a cikin mayukan gyaran fuska da yawa. Ga jawabin amfanin da Aloe Vera ke yiwa fata da kuma yanda za'a sarrafashi a samu abinda ake so. Aloe Vera yana maganin duhun fata. Yana magamin canjawar fuska da zafin rana ke kawowa. Yana kawar da fatar data mutu a fuska wadda ke kawo duhun fuska. Yana maganin ciwo a fuska. Yana maganin kumburin fuska. Yana maganin cizon kwaro irinsu sauri kudin cizo da sauransu. Idan za'a sayi man shafawa dage dauke da Aloe vera a duba a tabbatar ba'a hadashi da giya ba ko sauran sinadarai masu kawowa fata illa. Babbar hanyar samun amfanin Aloe vera a fuska, shine mutum ya hada kayansa a gida. Yanda ake hada man Aloe Ve...
A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

A cikin watanni 11 da suka gabata, Shugaba Tinubu ya kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen saman da yake hawa

labaran tinubu ayau, Siyasa
Gwammatin tarayya a karkashin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta kashe Naira Biliyan 14.77 wajan kula da jiragen da shugaban kasar ke amfani dasu a cikin watanni 11 da suka gabata. Hakan na zuwane a yayin da majalisar tarayya ta amince a sayowa shugaban kasar sabbin jirage 2. Kudin da za'a kashe wajan siyo sabbin jiragen sun kai Naira Biliyan 918.7 ko kuma dala Miliyan 623.4, kamar yanda kwamitin majalisar ya bayyana. Rahotanni dai sun bayyana cewa, jiragen da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa,Kashim Shettima ke amfani dasu sun tsufa sosai suna bukatar a canjasu.
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja

Duk Labarai
Wasu ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Janar Din Sojoji a Abuja Rundunar ‘yan sanda a babban birnin tarayya, FCT, ta kaddamar da bincike kan wani mummunan kisan gilla da aka yi wa wani Birgediya Janar na sojojin Najeriya, Uwem Harold Udokwe mai ritaya. DIMOKURADIYYA ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe Janar Udokwe a babban birnin kasar ranar Asabar. Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kai wa marigayin hari tare da kashe shi a gidansa na Sunshine Homes Estate da misalin karfe 3 na safiyar ranar Asabar. Ta ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth C. Igweh, “ya ​​ba da umarnin gudanar da sahihin bincike kan al’amuran da ...
Magidanci ya koka da cewa, Matarsa na barzanar Kàśhěśhi saboda ya kasa gamsar da ita a gado

Magidanci ya koka da cewa, Matarsa na barzanar Kàśhěśhi saboda ya kasa gamsar da ita a gado

Auratayya
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":["local"],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Wani magidanci dan kimanin shekaru 49 ya koka cewa, matarsa na barazanar kasheshi saboda ya kasa gamsar da ita a gado. Lamarin ya farune a kasar Zambia inda mijin ya kai kara kotu. Matar ta kuma yi barazanar fara yin lalata da wasu a waje idaan mijin ya kasa gamsar da ita. Kafar Zambia Observer ta bayyana sunan mijin a da Dennis Sikanika inda tace matar kuma sunanta Faustina Chola. Saidai mijin yace tun kamin su yi aure, ya gayawa matar tasa cewa, shi ba...