Tuesday, February 17
Shadow

Author: Bashir Ahmed

Ana fama da tsananin zafi a Saudiyya yayin da ake shirye-shiryen fara aikin hajji

Ana fama da tsananin zafi a Saudiyya yayin da ake shirye-shiryen fara aikin hajji

Hajjin Bana
Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ƙasar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji. Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a. Hukumomin ƙasar kan yi tanadin na'urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta. Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara
Hajji 2024: Saudiyya ta ƙaddamar da na’urar amsa fatawa ga maniyyata

Hajji 2024: Saudiyya ta ƙaddamar da na’urar amsa fatawa ga maniyyata

Hajjin Bana
Ƙasar Saudiyya ta ƙaddamar da na'urorin amsa fatawa ga masu ibada a masallatan harami. Na'urorin za su riƙa amsa tambayoyin da ke da nasaba da shari'a da dokokin addinin musulunci. Shafin X na Haramain ya ce an girke na'urori a harabobin masallatan harami domin bayar da fatawa ga maniyyata a lokacin aikin hajjin bana. Masu buƙatar fatawa za su kusanci na'urorin domin tambayar abin da ya shige musu duhu, inda su kuma na'urorin za su sada su da wani malami da zai amsa tambayar nan take. Na'urorin na karɓar fatawa da amsa ta cikin harsunan duniya 11, kamar yadda shafin Haramain ya bayyana
Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau. Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi ...
Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Duk Labarai
Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka isa ƙasar, daga sassan duniya daban-daban domin gudanar da akin hajjin bana. Jaridar Saudi Gazzet, ta ruwaito babban daraktan ofishin kula da bayar da biza na ƙasar, na cewa maniyyata miliyan 1,547,295 ne suka isa ƙasar ta sama da kan iyakokin ƙasa da kuma tasoshin jiragen ruwa. Ya ƙara da cewa maniyyata miliyan 1,483,312 ne suka shiga ƙasar ta jiragen sama, yayin dan mutum 59,273 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin ƙasa, sai kuma maniyyata 4,710 da suka je ta jiragen ruwa. A ranar Juma'a 8 ga watan Dhul-Hijja ne za a fara gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.
YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

Siyasa
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma'aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis. A yayin da masu karbar fansho da alawus za su more kyautar naira dubu ashirin duk a matsayin goron sallah. Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto
Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Faduwar da Tinubu yayi zata iya faruwa akan kowa, Cewar Sheikh Pantami, saidai da yawa sun sokeshi akan bai ce komai ba kan kashe-kashen da ake a Arewa amma gashi yana kare shugaban kasa

Siyasa
Babban malamin Addinin Islama, sheikh Isa Ali Pantami ya yi martani kan faduwar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yayi a wajan bikin ranar dimokradiyya. Sheikh Pantami ya bayyana cewa, faduwar shugaban kasar bata da alaka da shugabanci kuma zata iya faruwa akan kowa. Ya bayar da shawarar cewa a rika kawar da akai akan irin wadannan labarai zai fi kyau. "This can happen to any of us. It has nothing to do with governance. The earlier we ignore this kind of news, the better. May the Almighty make Nigeria a better place for us." https://twitter.com/ProfIsaPantami/status/1800855807711645873?t=2C5Wqjfz1fhBeyMVkRXelw&s=19 Malam yayi martanine bayan da jaridar Vanguard ta wallafa labarin faduwar shugaban kasar. Saidai malam ya sha martani daga bakin wasu dake cewa bai yi mag...

Alamun ciki a watan farko

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Watakila kinga canji a jikinki kin fara tambayar me ya faru? Ko kuma watakila batan wata ko daukewar jinin al'adane kadai kika fuskanta. Wasu matan na ganin alamun shigar ciki a watan Farko yayin da wasu basa gani. Ga alamun da ake gani na shigar ciki a watan Farko: Rashin zuwa jinin Al'ada ko batan wata: Musamman idan kina ganin jinin al'adarki akai-akai amma baki ganshi ba wannan karin, zai iya zama kina da ciki. Canjawar Dabi'a: Zai zamana kina saurin fushi ko kuma haka kawai ki rika jin bacin rai, hakanan zai iya zama kina dariya akan abinda bai kai ayi dariya akansa ba. Cikinki zai rika kuka ko kuma kiji kamar kinci abinci: Cin abinci irin su Aya, Tuwon masara, dawa, ko gero wanda ba'a barza ba, Kwakwa, wake zasu taimaka miki magance wannan matsalar. Zaki ji gabobink...

Yadda ake gane fitsarin mai ciki

Gwajin Ciki
Canjin kalar fitsarin mace me ciki abune wanda ba bako ba. Idan mace me ciki ta yi fitsari, idan aka duba za'a ga fitsarin ya kara duhu fiye da a baya. Wannan canjin kala na fitsari a mafi yawan lokuta ba matsala bane. Saidai a wasu lokutan da basu cika faruwa ba, yakan iya zama matsala. Yawanci kalar fitsari ruwa dorawa ne watau Yellow wanda bai ciza ba, amma na me ciki za'a ga yayi Yellow ko ruwan dorawa sosai. Hakanan zai iya zama kalar Mangwaro. Dalilan dake kawo Canjawar kalar Fitsarin mace mw ciki: Rashin isashshen ruwa a jiki: Cutar Infection a mafitsara. Cutar mafitsara da ake cewa, UTI. Canja kalar abincin da ake ci lokacin daukar ciki. Magungunan da ake sha lokacin da ake da ciki. Fitsari da jini, watau tsargiya. Cutar koda ko wani abu makamanc...