Ƙungiyoyin TUC da NLC za su tsunduma yajin aiki ranar Litinin
Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na TUC da NLC a Najeriya sun yanke shawarar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani sakamakon rashin cimma yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.
Gamayyar ƙungiyoyin sun sanar da hakan ne da yammacin ranar Juma'a bayan wani taro da suka yi inda suka tattaunawa yiwuwar tsunduma yajin aikin.
A farkon makon nan ne dai manyan ƙungiyoyin ƙwadago guda biyu suka yi watsi da tayin naira 60 da gwamnatin tarayya ta yi masu a matsayin albashi mafi ƙanƙanta, biyo bayan zaman da suka yi da gwamnatin tarayya, inda a nan ne gwamnatin ta yi tayin.
Da farko dai sai da gwamnatin Najeriyar ta fara kara naira dubu uku a kan tayin naira dubu 47 da ta yi a baya.
Su ma ƙungiyoyin ƙwadagon sun rage dubu uku daga naira 497 da suke nema a matsayin albashi mafi ƙanƙanta....