Thursday, October 3
Shadow

Babu ƙanshin gaskiya cewa sojojinmu na yin murabus – Rundunar sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rahotannin kafafen yaɗa labarai na baya-bayan nan da ke nuna cewa jami’anta sun yi murabus daga aikinsu ne saboda cin hanci da rashawa, da rashin ɗa’a, da kuma rashin walwala.

A makon nan ne dai wasu kafofin watsa labaran Najeriya suka yi ta naƙalto wani rahoto da ke nuna yadda sojoji fiye da guda 1000 suka yi murabus bisa zarge-zargen rashin jin daɗin aiki da rashawa da cin hanci “da ya yi wa aikin katutu”.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta bayyana waɗannan iƙirari a matsayin karya da kuma yunƙurin ɓata mata suna da gangan.

Karanta Wannan  Hotuna:An kira wasu matasan Arewa aka raba musu kudade, Naira 1,500 dan su fasa yin Zanga-zanga

A cewar rundunar, rahotannin an yi su ne domin haifar da saɓani da kuma ɓata tarbiyar jami’anta.

Sanarwar ta kara da cewa: “Batun cewa sojoji na yin murabus daga muƙamansu saboda rashin jin dadin rayuwa, da cin hanci da rashawa ba gaskiya ba ne.”

Rundunar ta fayyace cewa jami’anta suna da ‘yancin yin murabus daga muƙamansu bisa raɗin kansu, bisa ga ka’idojin da aka tsara a cikin ƙa’idojin Hidima na Hafsa da Sojoji.

Rundunar Sojin ta kuma bayyana ci gaba da jajircewarta na jin dadin ma’aikatanta a ƙarkashin jagorancin babban hafsan sojin ƙasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Daga ƙarshe rundunar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su tantance bayanai kafin a buga su don hana yaɗa labaran da ba su da tushe da makama.

Karanta Wannan  Mun baiwa Shugaba Tinubu shawarar ya ƙara kudin haraji na VAT daga kashi 7.5% zuwa kashi 10% -inji Oyedele, shugaban Kwamitin Haraji na Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *