Gyaran nono da man kadanya
Wasu bayanai sun nuna cewa man kadanya yana sanya nonon mace ya kara cikowa kuma ya mike sosai ko ya tashi tsayen, haka kuma a wani kaulin yana maida tsohuwa yarinya.
Watau yana hana fatar nonon tsufa da wuri.
Akwai hanyoyi biyu da wasu bayanai na gargajiya sukace ana amfani dasu wajan gyaran nono da man kadanya.
Na farko shine, ana hadashi da man wanke baki watau Makilin a shafa akan nono zuwa wani lokaci a wanke.
A bayani na biyu kuma, an samo cewa ana samun man kadanya ko man kade shi kadai a rika shafashi akan nono a hankali kamar ana mai tausa.
Saidai duka wadannan bayanai basu da inganci a wajan likitoci, hanyoyi ne na gargajiya na gyaran nono a gida.
Abinda ya tabbata shine, idan nononki na kaikayi, zaki iya shafa man kade, yana maganin kaikayin nono da kaikayin ka...