AL’AJABI: Bunsuru Ya Raka Gàwaŕ Wata Ďàttìjuwa Zuwa Makabarta A Kano
AL'AJABI: Bunsuru Ya Raka Gàwaŕ Wata Ďàttìjuwa Zuwa Makabarta A Kano.
Dattijuwar sunan ta Fatima Sani amma ana kiranta da Baba Bebiya mai shekara 70 a duniya, wadda take zaune a unguwar Nata'ala Kurna Kwachiri dake Kano. Ta rasu jiya da daddare bayan rashin lafiya, da safiyar nan aka yi jana'izarta aka kai ta makwanci na karshe.
Saidai wani abin al'ajabi da ya auku shin a yayin jana'izar shine, Wannan ďàn àķùýa da shi aka tsaya sahun sallah aka kuma raka ta da shi zuwa makabarta yana bin mutane a baya kuma tare da shi aka dawo bayan binne ta a makabarta.
Tabbas na yi mamaki kwarai ganin yadda wannan dan akuya ya bi mu zuwa makabarta duk nisan dake tsakani amma ya juri tafiyar har aka dawo.
Allah Ya jikanta da rahama ya bawa iyalai da 'yan uwanta hakuri yasa bakin wahalarta ...