Wednesday, January 8
Shadow

Duk Labarai

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Kaduna, Katsina
Sojojin Najeriya sun sun ce sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.. Cikin wata sanarwa kwamishin harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da Katsina Ya ƙara da cewa Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da sojojin suka samu daga jihar Katsina. Sanarwar ta ce sojojin sun yi ba-ta-kashi da 'yan bindigar a kusa da dajin Idasu, inda suka kashe ‘yan bindiga aƙalla 36 ciki har da Kacahalla Buharin Yadi. Ƙasurgumin ɗan bindigar ya yi...
‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

‘Yan Bindiga: Bani Da Ikon Tafiyar da Harkokin Tsaro A Zamfara – Gwamna Lawal

Jihar Zamfara, Tsaro
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ya kasa sarrafa gine-ginen tsaro a jihar. Lawal ya ce ba shi da iko a kan shugabannin hukumomin tsaro a jihar, yana mai jaddada cewa suna karbar umarni daga manyansu. Da yake jawabi yayin wani taron birnin tarayya na bikin ranar dimokuradiyyar Najeriya karo na 25 a Abuja ranar Laraba, gwamnan ya yi tir da ayyukan ‘yan bindiga a jihar. A cewar Lawal: “Da sunan, ni ne babban jami’in tsaro na jihata amma idan ana maganar umarni da iko, ba ni da iko a kan duk wani jami’in tsaro na soja, ko ‘yan sanda ko na Civil Defence. “Suna karbar umarninsu daga manyansu ba daga gwamnoni ba. Ba mu da wannan iko, ina fata muna da, da ya kasance wani labari na daban. " Ya ce matsalar tsaro ba ta gyaru a jihar ba sakamakon katsalandan da ya b...
An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

An Daure Wani Mutum A Gidan Yari Sakamakon Samun Sa Da Laifin Karbar Batirin Jirgin Kasa Na Sata

Duk Labarai
A ranar Alhamis ne wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a jihar Kaduna, ta yanke wa wani matashi mai suna Chibuzo Emmanuel, dan shekara 40 da haihuwa, hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari, bisa samunsa da laifin karbar baturan jirgin kasa da silinda na sata. Hukumar NSCDC, ta gurfanar da Emmanuel tare da Adamu Danbaba mai shekaru 52 da laifin sata da kuma karbar dukiyar sata. Jami'i mai shigar da kara na NSCDC, Mista Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa hukumar kula da layin dogo ta Najeriya da ke yankin Arewa ta tsakiya, Kafanchan, ta shigar da kara a ofishin hukumar a ranar 13 ga watan Mayu. Audu ya bayyana cewa Danbaba ma’aikacin layin dogo ne ya saci batir din jirgin kasa guda biyu da silinda mai nauyin kilogiram 12 a ofishin sa ya sayar wa Emmanuel akan kudi N24,000...

Cin yaji ga mai ciki

Duk Labarai, Gwajin Ciki
Cin abinci me yaji ga mai ciki bashi da matsala sam ko kadan. Kuma ba zai cutar da dan cikinki ba. Saboda yanayin bakin me ciki, zaki so cin abu me yaji dan kwadayi, masana sun ce zaki iya ci ba tare da matsala ba. Mutane da yawa na da tunanin cewa, abinci me yaji yana da hadari ga mai ciki amma hakan ba gaskiya bane. Saidai a sani ko menene aka yishi ya wuce iyaka zai iya bayar da matsala. Hakanan kowace mace da irin jikinta, wata Yaji zai iya zamar mata matsala, wata kuma bata da matsala dashi. Dan haka kinfi kowa sanin kanki. Yaji zai iya sa zafin kirji ko kuma rashin narkewar abinci wanda duka basu da mummunar illa ga me ciki. Jin kwadayin cin abinci me yaji ba matsala bane ga mace me ciki, ga wasu amfanin da abincin me yaji zai yiwa mace me ciki kamar haka: Cin...
Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Hoto: An kamashi da ka-wu-nan mutane 8 dan yin tsafi

Duk Labarai
Jami'an 'yansanda a jihar Ondo sun kama wani matashi me suna Yusuf Adinoyi bayan samunsa da kawunan mutane 8. Kwamishinan 'yansandan jihar, Abayomi Oladipo, ya tabbatar da kamen inda yace an kama wanda ake zarginne ranar Litinin bayan an kafa shingen bincike. Mutumin na kan hanyar zuwa Akure ne kamin aka tare motarsu wadda yayi kokarin tserewa amma aka bishi aka kamoshi. Ya amsa laifinsa inda yace a baya yana sana'ar sayar da manja ne amma rashin lafiyar mahaifiyarsa tasa ya shiga harkar sayar da kawuna. Yace wannan ne karo na 3 da yake son sayar da kawunan inda a farko ya sayar da guda 4, sannan ya sayar da guda 3 hakanan sai yanzu zai sayar da guda 8. Kwamishinan 'yansandan yace za'a gurfanar dashi a kotu bayan kammala bincike.
Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky ta koma kan ‘yan siyasa>>Inji Peter Obi

Siyasa
{"remix_data":[],"source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":false,"containsFTESticker":false} Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, ya kamata EFCC ta kyale Bobrisky da Obi Cubana ta je ta kama 'yan siyasa masu sata. Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV. Yace idan da a yanzu gwamnati zata ce zata ciyar da mata kadai a Najeriya, saboda yunwar da ake ciki, maza da yawa zasu saka kayan mata su je karbar abincin. Bobrisky dai yana can daure a gidan yari saboda lika kudi a wajan biki yayin da shi kuma Obi Cubana aka gurfanar dashi ...
Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

Atiku ya jajanta wa Tinubu dangane da “zamewar” da ya yi

labaran tinubu ayau, Siyasa
Mutumin da shugaba Tinubun ya kayar a zaɓen 2023, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP, ya ce yana jajanta wa Bola Tinubu dangane da "zamewar" da ya yi. "Ina matukar jajanta wa shugaba Bola Tinubu dangane da ɗan hatsarin da ya samu a lokaci da yake ƙoƙarin zagaya masu fareti ranar dimokaraɗiyya. Ina fatan lafiyar lau." A baya-bayan nan dai an ga yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ke ƙara ƙaimi wajen yin hamayya ta fuskar sukan abubuwan da yake ganin gwamnatin ba ta yi daidai ba.
Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Shettima ya buƙaci likitocin Najeriya su taimaka wajen inganta ƙasar

Siyasa
Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima ya yi kira ga likitocin ƙasar, su riƙa zama a ƙasar, don taimaka wa magance matsalar da ƙasar ke fuskanta ta ƙarancin likitoci. Shettima ya yi kiran ne a lokacin da ƙungiyar likitocin ƙasar - ƙarƙashin jagorancin sabon shugabanta, Farfesa Bala Audu - suka kai masa ziyara a ofishinsa ranar Talata. Mataimakin shugaban ƙasar ya nuna damuwa kan yadda likitocin ƙasar ke yawan ficewa daga ƙasar domin neman ayyuka a ƙasashen waje. A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar ficewar likitocin Najeriya daga ƙasar, zuwa ƙasashen wajen domin samun ingantaccen albashi da yanayin aikin mai kyau. Sai dai mataimakin shugaban ƙasar, ya jaddada cewa gwamnatinsu na iya bakin ƙoƙarinsu wajen inganta yanayin aikin likitoci a ƙasar, musamman waɗanda suka zaɓi ...
Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Hajji 2024: Fiye da maniyyata miliyan ɗaya da rabi ne za su sauke farali

Duk Labarai
Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan ɗaya da rabi ne suka isa ƙasar, daga sassan duniya daban-daban domin gudanar da akin hajjin bana. Jaridar Saudi Gazzet, ta ruwaito babban daraktan ofishin kula da bayar da biza na ƙasar, na cewa maniyyata miliyan 1,547,295 ne suka isa ƙasar ta sama da kan iyakokin ƙasa da kuma tasoshin jiragen ruwa. Ya ƙara da cewa maniyyata miliyan 1,483,312 ne suka shiga ƙasar ta jiragen sama, yayin dan mutum 59,273 suka shiga ƙasar ta kan iyakokin ƙasa, sai kuma maniyyata 4,710 da suka je ta jiragen ruwa. A ranar Juma'a 8 ga watan Dhul-Hijja ne za a fara gudanar da aikin Hajji na wannan shekarar.
YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

YANZU-YANZU: Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma’aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis

Siyasa
Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu Ya Bada Umarnin Biyan Naira Dubu Talatin A Matsayin Kyautar Goron Sallah Ga Dukkanin Ma'aikatan Jihar Da Na Kananan Hukumomi A Gobe Alhamis. A yayin da masu karbar fansho da alawus za su more kyautar naira dubu ashirin duk a matsayin goron sallah. Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto