Matarnan data zargi Ministan ayyuka David Umahi da neman suyi soyayya duk da yasa tana da aure ta fito ta yi karin haske
Tracy Ohiri, matarnan data zargi Ministan ayyuka, David Umahi da neman ta su yi soyayya duk da yasan cewa ita matar aure ce ta fito ta karyata kanta.
Tace a yi hakuri abinda ta fada ba haka yake ba ko kuma an mata mummunar fassara ne.
Tace bayan ganawa da danginta da lauyanta, ta yanke shawarar mantawa da wannan magana ta ci gaba da rayuwarta.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data wallafa.
A baya dai ta bayyana cewa, abinda ya kawo wannan rikici tsakaninsu, aiki ne tawa Ministan amma yaki biyanta hakkinta.
https://www.youtube.com/watch?v=GHsjquvtlGU?si=FOC0GU1mAVyntD0e
Saidai wasu na zargin cewa barzana aka mata ko kuma kudi aka bata ta janye wannan kalamai nata








