Alamomin shigar ciki a satin farko
Wadannan bayanai na kasa sune alamomin dake nuna cewa kin dauki ciki a satin Farko.
Saidai ki sani mafi yawan mata basa ganin ko wace irin alama a satin farko bayan sun dauki ciki.
Saidai wasu matan kuma suna ganin alamomin daukar ciki a satin farko kamar su kasala, ciwon nono, da ciwon gabobi a kwanki 5 zuwa 6 bayan an yi jima'i.
Yawanci likitoci suna yin gwajin ciki ne sati daya bayan daukewar jinin al'ada.
Maganar gaskiya shine ganin alamun shigar ciki a satin farko bai cika faruwa ba ga mafi yawan mata amma kowace mace da irin jikinta.
Ga dai alamun da mace zata iya gani a satin farko wanda ke nuna alamar ta dauki ciki:
Rashin Ganin jinin Al'ada.
Zubar da jini, ba irin na al'ada ba, zai iya zuwa kadan kuma zai iya daukar kwanaki.
Za'a iya jin ciwon ciki, ciwon b...