Dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya bayyanawa 'yan Najeriya cewa, mahaifinsa, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ba zai basu kunya ba.
Yayi kiran a ci gaba da baiwa Tinubun goyon baya.
https://twitter.com/i/status/2031311780576653614
Wannan wani tsoho ne dake kan Gadon Ajali wanda ya karbi Musulunci kamin ya rasu.
Bidiyon sa ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
https://www.tiktok.com/@alfaishmaelkamara/video/7614836939350478100?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7614836939350478100&source=h5_m×tamp=1773096588&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7606977366144993025&share_link_id=2981ec65-6faa-4768-a9e5-00e22b11e7ab&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b8727%2Cb2878&link_reflow_pop...
Tauraruwar Tiktok, Alpha Charles Borno ta bayyana cewa akwai wata kawarta da aka hadawa kawalci amma da ta je wajan sai taga ashe babanta ne.
https://www.tiktok.com/@alphacharlesborno/video/7614182206214393095?_r=1&_t=ZS-94YYge7eWv3
Wannan na zuwane yayin da fadan cacar baki ya barke tsakanin Sadiya Haruna da Babiana.
A Wannan Bidiyon na wasu tsaffin mutane da aka baiwa tallafin abincin Azumi na Gwamnatin tarayya sun nuna farin cikinsu.
An jisu suna cewa, shugaba Tinubu ya zarce a 2027.
https://www.tiktok.com/@arewablog_/video/7614864704837881109?_r=1&_t=ZS-94YXTNIpIkj
Saidai da yawa sun yi Allah wadai da hakan inda suke cewa abinda aka baiwa tsaffin ba zai dade ba zai kare.
Wani ya bayyana inda yace shine dan Marigayiya, Tauraruwar fina-finan Hausa, Saratu Gidado, Watau Daso.
Yace masu cewa bata taba haihuwa ba, ba gaskiya bane.
Yace shi danta ne.
https://www.tiktok.com/@a_a_apparels/video/7614945217153731861?_r=1&_t=ZS-94YW5aZPeYD
Kuma da yawa na cewa sun yi kama shi da ita.
Wannan Bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta inda aka ga wani miji ya kama matarsa a bandaki tana shan kemi yayin da ake azumi
An dai ji yana zaginta da yarbanci.
https://twitter.com/i/status/2031080293528912355
Jaruma Hassana Muhammad wacce aka fi sani da Safiya a shirin Zabi Biyu ta sanar yanzu cewa ta bar film saboda jin maganar mahaifiyarta, amma za ku gan ta a Zabi biyu zango na biyu da kuma uku tunda ta sanya hannu a yarjejeniyar shirin kuma an gama aikin zango na biyu an kusa gama na uku.
Sai kuma watakila wasu daidaikun shirye-shiryen da ta yi wanda bayan su ba za a sake ganin ta ba.
Wane fata zaku yi mata?
Daga Mutawakkil Gambo Doko
Wannan wani magidanci ne da ya bayyana cewa, baya son tallafin kayan abinci da za'a bashi muddin sai an daukeshi hoto.
An ga yanda ya dakatar da me daukar hoton inda yace baya son kayan abincin.
https://twitter.com/i/status/2030909083574763652
Da yawa sun jinjina masa inda suka ce ya kwatarwa kansa mutunci.
Wani Direban Tanki ya bayyana cewa, Aliko Dangote ba Alheri bane ga Najeriya inda ya nuna motocinsu na tanki a ajiye a kofar matatar man Dangote.
Yace Dangoten yaki basu lodin man inda yake shirin kara farashi.
https://www.tiktok.com/@ibrahimmikotaura/video/7614586857707392264?_r=1&_t=ZS-94XxlFFOzQn
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar yaki da rashawa da cin hanci, ICPC sun gano wasu gidaje a masar Egypt da suke kyautata zaton na Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne.
Gidajen suna a manyan unguwani ne na babban birnin kasar watau Cairo.
Rahotanni sun bayyana cewa darajar gidajen ta fara daga Naira Miliyan 700 ne zuwa sama da Naira Biliyan 5.
Kafar Daily Nigerian ta bayyana cewa wata majiya daga hukumar ICPC ce ta bayyana mata hakan inda ta kara da cewa, suna kokarin ganin sun samu cikakken bayani da zai tabbatar musu cewa gidajen na malam Nasiru Ahmad El-Rufai ne.
Saidai zuwa yanzu ICPC basu fitar da sanarwa kan hakan a hukumance ba.