Friday, December 13
Shadow

Duk Labarai

Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi, zata shiga yajin aiki

Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi, zata shiga yajin aiki

Siyasa
Kungiyar kwadago ta NLC ta ki amincewa da tayin Naira Dubu sittin(60,000) a matsayin mafi karancin Albashi. Wannan shine tayi na 4 da gwamnatin tarayya tawa NLC a cikin watanni 2 da aka shude ana tattaunawar. NLC dai ta sakko daga bukatar ta ta cewa sai an biya Naira 615,000 a matsayin mafi karancin albashi inda ta nemi yanzu a biya N118,000 zuwa N497,000. Wakilin NLC, Benson Upah ya bayyana cewa, Gwamnatin ba da gaske take ba da take cewa zata biyasu Naira Dubu sittin(60,000). Yace Gwamnatin ce ta jawo wannan matsala inda ta kawo tsare-tsare wanda suka saka al'umma cikin wahala
Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi  kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Duk Labarai
Mahajjatan Najeriya a kasar Saudiyya sun koka da kalar abincin da ake basu duk da biyan Naira Miliyan 8 a matsayin kudin aikin hajjin bana. Daya daga cikin mahajjatan me suna Babagana Digima ne ya wallafa hoton kalar abincin da ake basu a shafinsa na facebook. Abincin dai koko ne da kosai guda 3. Babagana Digima ya kara da cewa, mahajjata yanzu sun koma bara dan neman abinda zasu ci saboda kudinsu dala $300 daya rage daga cikin dala $500 da suke da ita har yanzu ba'a basu ba. Hukumar Alhazai ta kasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) da take martani akan lamarin, tace ta sa a yi bincike kan lamarin.
Kasar Japan zata gina Lifter wadda zata rika kai mutane sauran duniyoyi dake wajen Duniyar mu dan su ga yanda al’amura ke gudana

Kasar Japan zata gina Lifter wadda zata rika kai mutane sauran duniyoyi dake wajen Duniyar mu dan su ga yanda al’amura ke gudana

Duk Labarai
Wani kamfani na kasar Japan me suna Obayashi Corporation wanda shine ya gina gini mafi tsawo a kasar na shirin gina Lifter wadda zata rika kai mutane wajen Duniyar mu dan su ga yanda lamura ke gudana. Kamfanin yace zai fara wannan gini ne a shekara me zuwa watau 2025 wanda ake tsammanin kammalashi a shekarar 2050. Wannan lamari dai ya zowa mutane da mamaki amma wanda yace zai hadiye kota sai a sakar masa a gani.
‘Yansanda na bi gida-gida dan kama ‘yan daba dake shirin kai hari majalisar jihar Kano

‘Yansanda na bi gida-gida dan kama ‘yan daba dake shirin kai hari majalisar jihar Kano

Duk Labarai, Kano
Rahotanni daga jihar Kano na cewa, ‘yansanda na bi gida-gida suna kama matasa da ake zargin na shirin kai hari majalisar jihar Kano. Hakan na da nasaba da Sauke Aminu Ado Bayero da majalisar ta yi daga kan kujerar Sarautar Kano. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana hakan. Ya bayyana hakane da yammacin ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai. Ya bayyana wadanda ke shirin kai harin da cewa, makiyan jihar Kanone.
BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

Duk Labarai, Kano, Rashida Mai Sa'a
Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma tsohuwar mai baiwa Ganduje shawara, Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a ta bayyana cewa har yau Aminu Ado Bayero shi ne halastaccen sarkin Kano kuma ya dawo kujerarsa domin babu inda dangin miji suka taɓa sakin mata saboda ba su ne suka aura masa ita ba. Jaridar Dokin Karfe TV ta jiyo tsohuwar hadimar ta Ganduje wato Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a na cewa yanzu haka Aminu yana Nasarawa kuma za su ɗau wanka su fita Ido yana gani su raka shi fadarsa batare da zare Ido ba. “Sarki Aminu mutum ne mai tsoron Allah har zuci ba a baki ba. Kuma ba a taɓa sarki mai haƙurinsa ba, ba ya tsoma baki da katsalandan cikin siyasa”. Mai Sa’a ta kuma ƙara da cewa Sarki Aminu bai zo Kano don ya tada tarzoma ba, domin ya san muhim...
Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Duk Labarai, Kaduna, Kano
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin  Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna. Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter. Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar  Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna. Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.
Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Biyo bayan dambarwar data sarkake masarautar Kano, Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya fitar da sanarwa. Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun gidauniyarsa, ya bayyana cewa yana baiwa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Shawarar kada yayi abinda zai kawo hargitsi a jiharsa ta Kano. Malamin ya bayyana cewa, bai ji dadin abinda gwamnatin jihar Kano ta yi ba na sauke Aminu Ado Bayero ta nada Muhammad Sanusi II ba. Ya jawo hankalin gwamnatin jihar ta Kano cewa, ta yiwa doka biyayya dan zaman lafiya me dorewa a jihar ta kano. Shugaban gidauniyar ta Dahiru Bauchi, Ibrahim Dahiruin ya bayyana cewa, babu wanda yafi karfin doka. Yayi kira ga majalisar majalisar tarayya da ta yi doka da zata hana ‘yan siyasa amfani da damarsu wajan wulakanta sarakai ta hanyar saukesu. ...