Saturday, April 25
Shadow

Duk Labarai

A A Rano ya bude gidan mai na farko wanda babu me zuba man fetur wanda zai rika aiki ba dare ba rana

A A Rano ya bude gidan mai na farko wanda babu me zuba man fetur wanda zai rika aiki ba dare ba rana

Duk Labarai
Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, me kamfanin A A Rano ya bude gidajen man fetur na farko da zasu rika aiki awanni 24, ba dare ba rana kuma babu me zuba mai. Mutum ne da kansa zai shiga da abin hawansa gidan man ya sa katinsa na ATM ya biya ya kuma zuba man ya kara gaba. A A Rano sun hada kai da kamfanin Petrosoft Limited ne dan samar da wannan tsari. Ya bayyana cewa, hakan zai saukakawa Kwastomominsu shan man sannan kuma zai saukaka musu aiki suma. A A Rano yace sabbin gidajen man zasu fara aiki a watan Janairu.
Da Duminsa: Majalisar Jihar Rivers ta fara shirin tsige gwamna Fubara

Da Duminsa: Majalisar Jihar Rivers ta fara shirin tsige gwamna Fubara

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Rivers sun bayyana cewa, Majalisar Jihar ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Simi Fubara. An ga kakakin majalisar a wani Bidiyo daya watsu sosai a kafafen sada zumunta yana cewa 'yan majalisar 26 sun sakawa takardar neman tsige Fubara hannu. https://twitter.com/i/status/2009198809163665530 Majalisar tace tana zargin Gwamna Fubara da karya dokar kundin tsarin Mulki. Kuma sun ce zasu aika masa da takarda kan hakan. Hakanan majalisar ta kuma ce ta fara shirin tsige mataimakin Gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Nma Odu. Majalisar ta kuma ce ta dakatar da shirin Gwamna Fubara na kai mata kasafin kudin shekarar 2026.