Saturday, January 11
Shadow

Duk Labarai

2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

2024Sojojin Najeriya sun musanta zarge-zargen da Amnesty International ta yi musu

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton da Amnesty International ta fitar na zargin jami’anta da tsare tare da cin zarafin mata da yara da dama da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram a yankin arewa maso gabas. Mai magana da yawun rundunar Edward Buba ta bakin mataimakinsa kan yaɗa labarai, Group Kaftin Ibrahim Ali Bukar, ya shaida wa BBC cewa "ba za su damu da irin waɗannan kalamai na son kai da aka yi da niyyar rage kwarin gwiwar sojojin fafutuka don tabbatar da tsaro ba" Ya kara da cewa sojojin za su yi haɗin gwiwa mai inganci da Amnesty International idan akwai bukatar yin hakan kuma za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na kawar da ta'addanci da tabbatar da tsaro. Wannan martanin ya zo ne kwana guda bayan da Amnesty International ta zargi gwamnati da gazawa wajen bai wa ...
Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Atiku ya yi Allah-wadai da harin da ya kashe mutum 50 a jihar Katsina

Katsina, Siyasa, Tsaro
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam'iyyar adawa ta PDP, a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi alla-wadai da harin da aka kai ƙauyen Ƴargoje da ke jihar Katsina, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama. Harin da ‘yan bindiga suka kai, ya kuma haɗa da garkuwa da mata da kananan yara marasa galihu, lamarin da ya kara ta’azzara wa al’ummar yankin. Da yake nuna alhininsa game da faruwar lamarin, Atiku ya yi ƙarin haske kan harin kwantan ɓauna da maharan suka yi wa jami’an tsaron da ke amsa kiran gaggawa a kauyukan Gidan Tofa da Dan Nakwabo wanda yayi sanadin mutuwar jami’an ‘yan sanda hudu da wasu ‘yan kungiyar sa ido na jihar Katsina guda biyu. “Wannan babban rashi ne, kuma tunanina yana tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu,” in ji shi Atiku ya soki matakan da gwamnati...
‘Jami’an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina’

‘Jami’an tsaro shida na cikin mutanen da aka kashe a harin Katsina’

Duk Labarai
Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Katsina ta ce akwai dakarunta huɗu da kuma dakarun tsaro biyu na gwamnatin jihar cikin mutanen da 'yanbindiga suka kashe a harin da suka kai ranar Lahadi. Kakakin 'yansadan a Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa an tsaurara tsaro a yankin ƙaramar hukumar Kankara, inda suke aiki da sauran hukumomin tsaro don kare sake aukuwar harin. "A ranar 8 ga watan Yuni da misalin ƙarfe 3:00 na rana maharan suka far wa garuruwan Gidan Tofa da Dan Nakwabo, inda suka harbe mutum 20 tare da raunata wasu biyu, sannan suka yi wa motarmu mai silke kwanton ɓauna kuma suka kashe jami'an 'yansanda huɗu da kuma biyu cikin dakarun tsaron gwamnatin Katsina (KSCWC)," in ji sanarwar. Tun da farko rahotonni sun ce aƙalla mutum 25 aka kashe a ...
Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa

Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa

Duk Labarai
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi wa fursunoni 110 afuwa a wata ziyara da ya kai a babban gidan gyara hali da ke cikin garin Kaduna. Gwamnan ya ɗauki matakin ne a ranar Talata, kwana ɗaya gabanin bukin ranar dimokuraɗiyyar ƙasar wanda zai gudana a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu. Uba Sani wanda ya kuma bai wa fursunonin da aka yi wa afuwar naira 30,000 a matsayin kuɗin mota.
Majalisar Najeriya na neman bahasi kan yawan lalacewar jirgin Abuja-Kaduna

Majalisar Najeriya na neman bahasi kan yawan lalacewar jirgin Abuja-Kaduna

Duk Labarai
Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci ministan sufurin kasar ya gurfana a gabanta domin amsa tamboyoyi kan matsalolin da ake ci gaba da fuskanta a kan hanyar jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna a 'yan kwanakin nan. Ko a makon da ya gabata jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya goce daga hanya, matakin da ya bar fasinjoji cikin zullumi. Kan haka ne Majalisar ta amince da matakin gudanar da bincike domin fahimtar matsalar da kuma shawo kanta. Ɗan majaisa Umar Ajilo mai wakiltar Makarfi da Kudan ya ce ya gabatar da ƙudirin ne na gaggawa domin duba lamarin. "Ni ɗan Kaduna ne kuma duk lokacin da na hau jirgin tare da mutane zan ji suna nuna fargaba," in ji.
Ba za mu bari a sake kashe lantarki da sunan zanga-zanga ba – ‘Yansandan Najeriya

Ba za mu bari a sake kashe lantarki da sunan zanga-zanga ba – ‘Yansandan Najeriya

Siyasa
Rundunar 'yansandan Najeriya ta yi gargaɗin cewa ba za ta bari a sake kashe babban layin lantarki na ƙasar ba da sunan zanga-zanga. Wata sanarwa da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a yau Talata ta ce rundunar za ta tura jami'nta domin gadin tashar babban layin mako guda bayan yajin aikin 'yan ƙwadago ya jefa ƙasar cikin duhu. Gargaɗin na zuwa ne yayin da rundunar ta ce ta samu labarin wasu na shirin gudanar da zanga-zanga a ƙasa baki ɗaya, tana mai gargaɗin cewa "ba za mu bari a kawo naƙasu ga gine-ginen more rayuwar sauran al'umma ba". "Ana tunatar da mutane cewa laifi ne taɓa babban layin wutar lantarki na ƙasa ta hanyar hanawa ko kuma kawo cikas ga samar da wutar," in ji sanarwar. "Yayin da rundunar 'yansanda ke da niyyar kare haƙƙin masu son yin zanga-zangar lu...
Wasu na shirin gudanar da zanga-zangar lalata Ranar Dimokuraɗiyya – DSS

Wasu na shirin gudanar da zanga-zangar lalata Ranar Dimokuraɗiyya – DSS

Tsaro
Rundunar 'yansadan Najeriya ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta ce ta samu labarin wasu na shirin fakewa da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar da zimmar aikata laifuka kuma ta nemi 'yan ƙasa su guji yin hakan. Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce an shirya zanga-zangar ne da gangan "domin ta dace da Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yuni". Ta alaƙanta zanga-zangar da gwagwarmayar neman ƙarin albashi mafi ƙaranci da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi, inda ta ce "gwamnatin tarayya ta fi son a warware matsalar cikin lumana har ma da maganar mafi ƙarancin albashi". "Sai dai kuma DSS na jaddada aniyarta ta kare ƙasar daga duk wani yunƙuri na wasu ƙungiyoyi na karya doka da oda. Sannan kuma za ta hada kai da sauran jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyi," in ji sanarwar. Ita ma runduna...

Abubuwan da mata suka fi so

Duk Labarai
Mata suna son abubuwa da yawa, ga kadan daga cikinsu kamar haka: Mata na son kyauta: Kyauta na kara dankon Soyayya, kyautar kudi, kayan sawa, Abinci ko wani abin amfani suna daukar hankalin Mata sosai. Mata na son namiji me kwalliya: Mata nason su ga namiji tsaf-tsaf yana kwalisa, Eh ka yi wanka kasa kaya masu kyau, hula me kyau, takalmi me kyau, zak ga mata na ta kallonka, kuma budurwarka zata so tsayawa tare da kai. Mata na son namiji me kudi: Kusan dukka mata na son namiji me kudi, dalili kuwa shine su dangin kudi ne, inda ake kyale-kyale da cin me dadi, me babbar mota, me yawan tafiye-tafiye, m rike babbar waya, me yawan kyauta. Kuma karka ga laifinsu, su dama abokan jin dadin rayuwa ne dan haka da kudi sun fi kyawun rikewa. Shiyasa ma karka ji haushi idan wanda yafi ka kud...

WATA SABUWA: Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, ya umarci hakimai a jihar Kano da su shigo cikin birnin na Kano domin fara shirin hawan sallah babba.

Duk Labarai
Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, ya umarci hakimai a jihar Kano da su shigo cikin birnin na Kano domin fara shirin hawan sallah babba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da galadiman Kano Alhaji Abba Sunusi ya sanyawa hannu. Sanarwar ta kuma buƙaci hakiman da su shigo cikin Kano da dagatansu, mahaya da kuma dawakansu. Menene ra'ayinku?

Alamomin shigar ciki a satin farko

Duk Labarai
Wadannan bayanai na kasa sune alamomin dake nuna cewa kin dauki ciki a satin Farko. Saidai ki sani mafi yawan mata basa ganin ko wace irin alama a satin farko bayan sun dauki ciki. Saidai wasu matan kuma suna ganin alamomin daukar ciki a satin farko kamar su kasala, ciwon nono, da ciwon gabobi a kwanki 5 zuwa 6 bayan an yi jima'i. Yawanci likitoci suna yin gwajin ciki ne sati daya bayan daukewar jinin al'ada. Maganar gaskiya shine ganin alamun shigar ciki a satin farko bai cika faruwa ba ga mafi yawan mata amma kowace mace da irin jikinta. Ga dai alamun da mace zata iya gani a satin farko wanda ke nuna alamar ta dauki ciki: Rashin Ganin jinin Al'ada. Zubar da jini, ba irin na al'ada ba, zai iya zuwa kadan kuma zai iya daukar kwanaki. Za'a iya jin ciwon ciki, ciwon b...